ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

: *DANDANO DAGA *

MAIRO A GIDAN YAYA HABIBU!!!
© Sumayyah Takori
Litinin babbar rana, ko bature yana tsoronki. Habibu ya yi shirin ofis cikin suit din ma’aikatan bankin Barclays , da jibgegiyar rigar sanyi, hand-socks da leg-socks, yana so zai fita aiki. ga yara sunyi shirin makaranta tsaf, misalin karfe bakwai daidai na safe. amma babu hanya, domin kuwa tashi sukayi suka tarar kankara ta rufe kofar gidan ruf, da tagogi bakidaya.

Dina ma ta fito cikin nata shirin cikin kayanta na lauyoyin banki, tana ta korafi akan ‘snow’. Dole Habibu ya fiddo waya ya kira ma’aikatan sare kankara, nan da nan suka zo cikin minti goma, suka bambare kankarar sannan suka samu hanya suka fita.

Mairo ta fito daga dakinta ta yiwa sanyi mugun shiri, baka ganin komai nata sai shacin kayatacciyar fuskarta kai ka ce balarabiyar Morocco ce. Tasa yaran a gaba suka fito tana dauke da little Mairo, suka zo bakin hanya suka tsaya tana rike da hannayensu, tsayuwar minti biyar sukayi motar makarantar su ta iso ta sanya su ciki suka tafi, suna daga mata hannu itama tana daga musu. Kasancewar ita bata da karatu a yau sai ta kama hanya cikin nutsuwa ta koma gida.

( Wannan shine tsarin rayuwar gidan Yaya Habibu a kullum. Duk wayewar gari kowa abinda yake yi kenan).

Mairo na karantar Zamantakewar Dan adam (Sociology ) a jami’ar Michigan (Michigan State University) tun bayan dawowar ta gidan Yayanta Habibu. A yammacin ranar tana zaune a study-room da farin gilashin karatu a idanunta tana nazarin littafin ‘Haralarambus and Holborn ( Sociology , Themes and Perspectives ) domin wani assignment (aikin gida) mai matukar wuya da aka basu akan hedonism zasuyi submitting a washegari.
Aunty Dina ta murda kofar ta shigo fuskarta dauke da murmushi, sassanyan kamshin ta na turaren (yves saint laurent) shi ya fara bakuntar hancin Mairo kamar koyaushe, Dina mace ce mai darajja kamshi a jikinta ta dade da sanin wannan. Ta ja kujerar dake fuskantar Mairon ta zauna sannan tace “Mairo dan rakiya nake nema, London zan je gobe ko zan samu ki raka ni?”Mairo ta shiga girgiza kai da sauri “inada aiki mai yawa a makaranta goben, kuma zanyi submitting assignment dina, me zaki je kiyi?”
Ta ce “kallon ‘film-fare award’ na wannan shekarar, gara in gani vivid fiyeda a talabijin nafi gane komai. Tun wancan satin ake ta sanarwa za’ayi”.

Mairo bata san kallon Indian na Aunty Dina ya kai matsayin haka ba, da zata ni ki gari kasa-ya-kasa tun daga birnin Michigan har babban birnin Birtaniya don kawai ta ga GALA! Da sauri tace “sai kin dawo. Ni kam, bazan samu zuwa ba”.

Habibu da taya bera bari ya yankowa Dina tiket ta tashi a washegari, gidan ya saura sai su kadai. Tun safe Mairo na makaranta tana fama da ayyukan gaban ta itada kawarta Ir’eesh Tawheedah ‘yar asalin kasar Somalia. Bata dawo gida ba sai yamma lis, ta tarar tuni Yaya Habibu ya riga ta dawowa. Zaune suke a falon shi shida yaran suna aikin makaranta yana nuna musu. Mairo tayi sallama ta shigo suka yi tsalle suka daneta suna yi mata “oyoyo”.

Yaya Habibu ya daga ido ya kalle ta yana mamaki cikin ransa wai wannan Mairo ce, MAIRON GURIN-GAWA, MAIRON-HURE! Abu daya ya tuno a wannsn lokacin yayi murmushi (goruba daga kan bishiya a kauyen GURIN-GAWA) ya ce “Mairo ‘yan makaranta…. Mairon Dina. … Mairon Yaya Habibu…!” Ta yi dariya har fararen jerarrun hakoranta suka fito. Kirarin da yake mata kenan idan ya so nishadi. Ta wuce dakinta rungume da jakarta don ta kimtsa.

Bayan tayi sallar magriba tayi wanka ta canza kayan jikinta ta fito falon ta zauna tare dasu. Zuwa can Yaya Habibu ya fito daga dakinsa cikin shiri, sai kamshi yake. Ga dukkan alamu cikin sauri yake. Ya dube tayace “maza a shirya dinner, amma African-Dish . Inada babban bako anjima kadan. Babban abokina Amiru zai sauka yanzunnan daga Washington D.C zan je filin jirgi na dauko shi”. Yadda yake maganar cikin rawar jiki kadai zaka fahimci wannan bakon mai muhimmanci ne da matsayi na musamman a gareshi. Ba tun yau ba Mairo na jin sunan Amiru a bakin Yaya Habibu da Dina. Zata iya cewa rana bata fitowa ta fadi wani cikinsu bai ambaci Amiru ba.

Ta amsa da ladabi “toh, sai kun iso”.

Yana fita ta mike ta nufi kicin, Lynder na goge-goge ta bata hanya ta wuce, ta bude deep-freezer tana tunanin me zata dafa musu? Daga bisani zuciyarta ta tsaya akan tuwon shinkafa miyar danyar kubewa tunda dai suna da Okora (danyar kubewar gwangwani).

Nan da nan ta dora sanwa, tayi amfani da dried fish da mushroom curry cikin miyar, duk kicin din sai ya dau kamshi. Sunada zobo, don haka ta tafasa shi ta tace, ta markada abarba ta hade da zobon da fulebo din abarba ta juye a jug ta sanya a firji don ya yi dan sanyi ba tareda ta sanya sukari ba.
Ba tun yau ba ta san Yaya Habibu da son Danwanke, kai shi duk wani abinci ma na Africa to ya bi bayan dan wake. Don haka nan da nan ta jika kanwa ta kwaba ta jejjefa cikin tafashashshen ruwan zafi, cikin dan lokaci ta kammala komai.


Ta kashe wayar ba tareda ta baiwa Nabilah amsa ba. Jikinta a sanyaye matuka, maganganun Nabilah kullum irin na Anty Dina ne, ko maiyasa? Alhalin basu san juna ba, basu taba ganin juna ba ko a hoto, balle tace sun hada baki ne suna sharing idea don su kalubalanceta! Dai-dai lokacin taji shigowar Yaya Habibu da bakonsa. Da alama ba su biyu bane don tana jin muryoyin maza daban daban. Ta sake kudundunewa a cikin bargonta sama-sama take jiyo tashin muryarsu anata turanci kamar tashin duniya. Kira ya shigo wayarta, daga kwance ta mika hannu ta amsa a kasalance.
Dina ce.

Tace “yaya kuke Mairo? Hope ba matsala, ina nan tahowa gobe insha Allah, mai zan sayo miki?”
Mairo ta ce “munyi kewarki ne kawai Anty, duk gidan ba dadi da baki. Bana bukatar komai sai dawowar ki lafiya”. “Nima haka Mairo, ji na nake kamar nayi shekara ban ganku ba. Me ya samu wayar Habib ne? Na kasa kama shi”.
Tace “yana falo, yayi baki ne”.
“Su waye?”
Mairo ta ce “Na dai ji yace Amiru ne”
Dina tace “wow! Amiru yau a gidanmu? Maza kaiwa Habib wayar inason magana da shi”.
Ta mike rike da wayar ta fita, shaf ta manta ko kanta bata rufe ba tsabar yadda Dina ta matsu tayi magana da mijin nata, a haka ta isa falon. Ta karasa kusa da Habibu ta mika masa wayar. Juyowar nan da zatayi sai idonta cikin na Amiru, wanda ke zaune gefen Habib cikin Italian Suit bakake wul, ya sassautama wuyanshi ruwan tokar tie dake jikinshi. Suka samu kansu cikin matsananciyar faduwar gaba a lokaci guda. Ga ita Mairo, kwarjini ne da kyawun Amirun ya haifar mata da faduwar gaban. Amma ga AMIRUN, bazan iya cewa ba!

Habibu yace “Amiru meet my beloved sister MAIRO , da nake baka labari…”.
Yana mai kokarin saita lumsassun idanunsa akan Habibun, don kawar dasu daga nacewar da sukayi akan Mairon yace “itace Mairon??? Mairo zo mu gaisa….”. Amiru dai Hausa yayi, amma wani accent ne da Mairo bata taba jin mai gardinsa cikin kunnuwanta ba. Kamar yadda bata taba ganin mutum mai kyau da kwarjininsa ba, ilhamomin dake tare da shi bata taba haduwa da mai irin su ba! Wannan shine AMIRUN Yaya HABIBUN???

( The beginning of everything kenan)


Mairo data koma daki kwanciya tayi rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon mutum mai kima kamar Amiru, kace baka sonsa ai ya zama wulakanci da cin fuska. To amma ita a ganinta daidai tayi, don bata iya karya ko yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san bata kyauta ba. Saidai a ganinta gara hakan, da dai tayi irin auren da zuciyarta ta raya mata akansa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button