BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

SAKON TA’AZIYA ZUWA GA PHATEEMA LAWAL

Ina me miki ta’aziyan rasuwar kakan ki, Allah Ya ji kan ta, Ya mata rahama, Ya gafarata mata zunuban ta, Ya haskaka kabarin ta, Yasa aljannah ce makomar ta. Sorry for the lose sister, Allah ya baku hakurin rashin ta, Amin.

Dedicating this chap to those who post my book. Thank you soooo much, I can't thank you guys less, I really appreciate your efforts.

2️⃣5️⃣&2️⃣6️⃣

Da suka isa gidan Nabila, Abdallah yayi horn, aka bude mai, ya shiga.

Da za su fita acikin motan, Abdallah yace “kinga lokacin sallah ya kusa, da mun dan yi hira. I can’t wait for you to be mine, then I won’t need any permission to be with you. Dan Allah kaman yanda kika yi alkawari, in Kika koma school, dan Allah ki ma mummy magana, nima zan ma su Abba magana. Kin san annabi Muhammad (SAW) yace; shi bai ga abun daya fi dacewa da mutani biyu dake son juna ba, inba aure ba. So why should we take long on a mere relationship, mu fahimci juna, even if it’s for 2 to three months, if we are okay with each other, we should take it further, amma idan vice versa ne, kai Allah ma ya kiyaye, In Sha Allahu zamu fahimci juna. Amma still ya na da kyau iyayen mu su san muna cikin relationship. Am going to miss you so very much, sai na kara zuwa kano In Sha Allah.”
“Kar ka damu, zan fada mata. Addu’an shi ne iyayen mu su yarda, ni dai na san side dina ba problem, domin a familyn mu, zaka iya auren kowaye, in as far as yana da addini, kuma yana amfani da shi, sannan in suka yi bincike akan shi da familyn shi, kuma ya zauna masu, toh they are good to go. Gaskiya ne maganan ka, ko ni ma bana son long relationship. Nima zanyi missing din ifemi (my love), amma I will wait for the right time. Kazo fa, inba haka ba, inyi fushi.” Ta fada tana rufe fuskar ta wai ita mai kunya.
“Toh shikenan Olamin Abdallah, aka qalbin Abdallah, In Sha Allah, baza’a samu matsala ba ta side din su Abba ma. Karki damu, in iyayen mu suka yarda, maybe wannan hutun naku, akai goron tambaye. And In Sha Allah I will come.”
Wani irin kunya ya kama ta, a kunyace, tace “toh, Allah ya tabbatar mana da mafi alheri. Kaga ana kiran sallah, bye”.
“Okay bye, take a very good care of my heart please”.
“In Sha Allah.”
“Toh habibty, nagode da kika bamu time din ki, Allah ya sauke ku lafiya, ya bar ki da Asim.”
“Sai yanzu kuka san dani kenan. Amin, nida yaya Asim dina.”
“A’a habibty, ai muna sane da ke. Amin, Allah ya bar ku tare.”
“Amin. Toh bye”. Nafisa ta fada, sannan suka fito daga cikin motan, Olamide nata waving din shi, har ya fita.

Da sallama suka shiga, suka samu Nabila da kannan Farouq a parlor. Nafisa taje tama Nabila side hug, amma sai taga tayi shuru, bata yi reciprocating, su kuma kannan Farouq suka fara dariya, abun ya ba Nafisa haushi, sai tace “meye haka dan Allah?”
Alokacin Nabila ta dago kai ta kalle su one by one, ita da Olamide, sai tace “ai da kun kwana ne kawai.”
“Ban gane damu kwana ba?” Wannan time din, Olamide tayi magana.
Suko kannan Farouq, kokarin danne dariya suke, amma yaki dannuwa.
“Ae mana, da kun kwana. Ku da kuka san gobe zaku wuce, amma kuka dade haka, kuma fa kun san duk da cewa zan dawo in the next two weeks, am still going to miss you. Saboda ku ne fa naji bana missing din gida, amma nasan daga gobe kam shikenan, komai zai dawo square one, gobe zan san ae na bar gida, instead ku dawo da wuri ku kwantar mun da hankali, amma sai yanzu kuka dawo.” Ta fada tana hawaye.
Olamide da Nafisa suka kalli juna, kawai Nafisa ta fashe da dariya, ita kuma Olamide taje kusa da Nabila tayi hugging din ta, tace “haba my black queen, ki daina kuka please, bada gangan muka ki dawowa da wuri ba. Naso mu dawo tun 6pm, amma Adda Fadila ta ita jan mu da hira, kuma wallahi we thought about this, tambayi Fisa. I know you are going to miss us, and we too will, na san yau din nan, we are meant to be with you, make you forget your worries, but man propose, God dispose, wani sain ba yanda kayi plan abun ke zuwa ba, so ina me baki hakuri, nice sillan haka, so am sorry. Amma if you can stay with us har 10:pm yau, we will pet you, till you get tired ko habibty?”
“Ae mama Olamide. Amma kin san har na fara jin haushin maganan ki, I was even ready to answer you back, ashe shagwaba kika, iye, su bila an iya tada hankalin mutum.” Nafisa ta fada tana daga ma Nabila gira, Nabila bata san lokacin data fara murmushi ba, yanda tayi murmushin, ya basu dariya, sai suka fashe da dariya, daman kannan Farouq na danna nasu, kawai sai suka yi bursting at the same time.
Sanda suka yi ma ishi, kafun Olamide tace “bari muje muyi sallah ko uwar shagwaba.”
“Ai kuwa, dan in muka biye maki, baza muyi ba.” Nafisa ta fada.
“Toh ai nima ban yi ba, daman ina jira ne ku shigo. Amma yaya kam tun 6:25 ya fita, sai kuma my marasa tausayi cousins, masu mun dariya.” Nabila ta fada tana hararan su Nusaiba.
“Su kuma suna jiran driver ne inya kawo dinner, su tafi dashi. All the time din da nake complain, suke ta dariya.”
“Toh kin ga laifin su ne?
Ko nima nayi dariya bale su.” Nafisa ta fada.
“Ni kam a bar surutu, muje muyi sallah.” Olamide ta fada.
“Toh uztaziya”. Nafisa ta fada.
“Ba zan biye maki ba, saboda baki ki a ita surutu ba har gobe.” Olamide ta fada, ta bar wajan, sannan kowan man su ta mara mata baya, amma banda Nabila, dakin ta ta wuce.

Suna idar da sallah, yayi gab da drivern gidan su Farouq ya zo. Nusiba da Hafiza suka yi hugging din su Olamide kaman sun san su daa, harda su we are going to miss you. Suma su Olamide suka raka su har cikin compound, inda suka shiga mota, sai Hafiza tace suyi exchanging din numbers dukan su, suka yi exchanging din numbers.

Sun idar da sallan isha, har sun ci abinci, su uku suna zaune a guestroom, Olamide ta jawo ledojin da Adda Fadi ta bata, ta mika ma Nafisa nata.
“Ina kuka samo wannan ledojin kuma?” Nabila ta tambaya.
“Adda Fadila ta bamu.” Olamide ta amsa.
“Very good, nama manta ban tambaye ki how far ba, amma tunda naga haka, nasan it went smoothly.” Nafisa ta fada.
“Gaskiya kam it deed, am so happy for you habibty. Kinga yanda ake tarerayan mu ne?
Gaskiya ita da mijin ta akwai kirki. Ga yar su ma Afra, very funny wallahi, kuma akwai saurin sabo, kawai dai Irfan that’s second born din ta, ya ke makale da ita, baya barin a taba shi, but everything went smoothly.”
“Allah sarki gashi da har kin fara damuwa, kinga this alone is a good sign, gaskiya naji dadi data tarbe ku da kyau, saura iyeye yanzu. Kar ki damu suma din zasu iyi accepting In Sha Allah”.
“Allah yasa, dan ni yanzu wallahi duk wanda ya raba ni da shi, zai zama babban enemy na, wanda baya son ganin farin ciki na.” Olamide ta fada.
“Kar ma ki damu, In Sha Allahu yaya Abdallah na qalbin sa ne.” Nafisa ta fada ta na shafa mata baya.
“Naji dadin yanda kika kira mun shi, da ina da goro dana baki.” Olamide ta fada tana rufe baki, saboda kar tayi dariya. Ita kuma Nabila ta fashe da dariya, tace ” ai baza’a rasa ba acikin unguwan nan.”
“Zan maku rashin M fa, no be only goro, na garawgaraw.” Nafisa ta fada tana hararan su.

“Yauwa Fisa, dan Allah bani labarin yanda Ore ta yi behaving a gidan please.”
“Enh, wato kin maida ni amebo business center ko, aka AK47.”
“Haba na isa, ai ban isa ba, kawai dai kin iya bada labari ne sosai.”
“Gulmanma kawai.” Olamide ta fada tana hararan ta.
“Nayin, gulman ma iyawa ne.” Nabila ta fada itama tana hararan ta.
“Zaku ci gaba ne, ko in fara baki labari?” Nafisa ta tambaya.
“Ki fara ooohh dear na.” Nabila ta amsa.
“A’a bani bace dearn ki ba.” Nafisa ta fada, daga nan ta fada ma Nabila duk yanda aka yi, ko mistake bata yi.
“Wow gaskiya har naji ina mugun son ta, I can’t wait for ranan da zai kai ni gidan ta, kuce dai harta fola ma friendship din mu ma, gaskiya ina son ta duk da ban san ta ba.”
“Hanya kin kai ni son ta, wallahi ta shiga rai na sosai, ga shi suna mugun kama da yaya Abdallah, difference din kawai shi ne shi namiji ne, ita kuma mace.” Nafisa ta fada.
“MashaAllah, gaskiya ina son ganin ta, ko kuna da hoton ta.”
“Ae, mun duki hoto tare, harda yaran ta.” Olamide ta fada, ta dauki wayar ta, ta bude galary, ta je camera, ta mika ma Nabila wayar, wai tana scrolling, zata ga hotunan. Nabila ko sai faman mashaAllah take.
Da Nabila ta gama kallon hotuna, sai tace su bude ledojin mana aga abun da sweet in law tasa. Olamide ta fara bude nata, atamfa ciganvi ke ciki, design din da colour combination din yayi kyau, sai kuma wani flat shoe carton brown mai mugun kyau.
“Wow mashaAllah, wallahi matan nan na son ki, gashi kaman ta san abun da zai yi fitting din ki, ki kira ta ki mata godiya gaskiya.” Nabila ta fada.
Sai Olamide tace “kaman kina cikin zuciya na, amma bari habibty ta bude nata ma mu gani. Ai da mun duba tun dazu, da mun mata godiya alokaci data kira, gashi tana ta mana godiya akan common chocolate da sweets din da muka siya, gaskiya har naji kunya.”
“Gaskiya ko ni, kunga bari nima in duba, mu kira ta tun da wuri.” Nafisa ta fada, ita ma ta bude nata ledan, sai taga takalmi ne, itama flat, amma golden colour, yayi kyau sosai, kuma zaiyi fitting din kafafuwan ta ita ma sosai.
“Gaskiya tana da kirki sosai, ku kira ta yanzu nan please. Kyauta haka, ai mungode”. Nabila ta fada.
Sharp sharp Olamide ta dau wayar ta, ta kira Adda Fadila, nan suka ita mata godiya, har sunyi magana da Nabila ma, tace mata nata ma na nan, amma sai tazo. Suka kara yin godiyan wannan ma, Afra ma ta masu magana, kafun suka yi sallama, suka kashe wayar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button