BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Da Olamide ta gaji da kallon masu rawa, ta tashi zata bar gurun, wayan ta yayi ringing, tana duba wanda ya kira, taga Hakeem. Ciki jin dadi da walwala, ta daga, sannan ta fita daga hall din, saboda kara yayi yawa.

Abdallah na juya kan sa, ya gan ta zata fita, ya tashi cikin natsuwa, ya biye mata baya, nan yaji tana waya. Ya aza ko saurayin ta ne take waya da, har heartbreak ya fara kama shi, sanda yaji tana cewa zata dake shi inta dawo, shi yasan bayanda zata ce zata daki saurayin ta. Hakalin sa bai gama kwaciya ba, sai lokacin da yaji tana kiran Fa’iza da autan Mummy, sannan hankalin sa ya kwanta. Yana ta ears dropping, har ta gama waya. Yana jiran yaga ta juya ta shiga hall, sai yaga ta nemi kujera, ta zauna. “Wato qalbi bata son damuwa da hayaniya kaman ni, hmm maybe in mata magana yanzu, because banda time kuma, gobe daurin aure, kuma ana gamawa, zamu kama hanyan Gombe, gwanda kawai na fada mata yanzu”.
Sanda yayi addu’a ya tofa ma kan sa, dan according to him, this is a life changing matter.

Da Olamide ta gama waya, ta ce bari ta zauna kafun masu rawa su gama rawan su, sai ta koma. Sai ta nemi wuri ta zauna, ta kunna data, tana WhatsApp. Tana cikin chatting din ta, taji ana mata sallama.

Daya gama addu’a, ya tofa, ya kara cewa “ya Allah, kaga niyya ta akan ta, I don’t mind getting married to her in the next two to three months, but Allah you know best, if she is going to be good for me, ya Allah kasa ta yarda dani, in kuma she will not be good for me, ya rab kasa karma ta saurare ni”.

Da bismillah, ya fara takawa har inda take, yaga duk hankalin ta na kan wayar hannun ta, sai yayi sallama. A hankali ta dago kai, ta amsa mai.

Olamide na ganin shi ne mai kallon ta a hall, ta fada a zuciyar ta, tace “ai kuwa sai ka fada mun dalilin daya sa ka kure ni da ido, sai kuma na maka lectures, saboda Islamically, only first look is halal, we are meant to lower our gaze, both male an female”.

Tana cikin tunani, taji yace “ina iya zama akan wannan kujeran”?
“Ka zauna ma, tunda dai baa kai na zaka zauna ba”. Ta fada tana wani bata rai”. Tana fadan haka, ta maida hankalin ta kan wayar ta.

“Dan Allah ki dan bani attention din ki, magana mai mahinmanci zan miki”. Abdallah ya fada.
“Toh ina sauraran ka”. Olamide ta fada, sanan ta kashe kawar.
“MashaAllah. Gaskiya ban san daga inda zan fara ba, amma let me start from anywhere. Please try and understand me, cause have never done this before”. Abdallah ya fada.
“Ba damuwa ina jin ka” Olamide ta fada.
“MashaAllah. Gaskiya kin burge ni, yanayin ki ya burge ni sosai. Yanda kike babbar kawan nan, da wata ce data caba fuskar ta da makeup, kuma tasa kaya anyhow, irin yanzu da ake rawa, ta zaman gaba awajan, kuma ta dunga rawan kai, amma ke kam ko ajikin ki. Wallahi tun da kika fito daga mota, nake ta observing din ki, and subhanallah, I found the feature in you, although yau na san ki, kuma yau din ma bai wuce 1hr ba, amma ji nake kaman na san ki da’a”.
Haka Abdallah ya ita zuba, ikon Allah, mutumin da baya wani sonyin magana dayawa da mutani, Olamide ko sai kallon shi take.

“Baki ce komai ba sister. Sorry, ban mayi tambayan sunan ki ba, am very sorry for that. So please zan iya sanin sunan beautiful creation din Allah”? Abdallah ya yana murmushi.
“Uhmnn Olamide”. Olamide ta amsa mai.
Cikin surprise, Abdallah yace “Olamide, ai wannan sunan yarbawa ne, ko akwai wannan sunan ne cikin Fulani, amma ban taba ji ba”.
“Toh ni nace maka ni Fulani ce?
Shi yasa ma bana son yan north na mun irin wannan maganan, dan yanzu zaku fara tribalism din Ku, mtchwwww” ta ja tsaki, ta maida hankalin ta kan wayar hannun ta.
“A’a sister, ni dai am not one of them, amma wallahi nayi zaton ke bafulatana ce”.
Cikin zafin rai, ta kashe wayar ta, tace “tunda kaji ba bafulatana bace, sai ka tashi ta koma inda ka fito, dan daman anan ka same ni”.
“A’a kar muyi haka da ke. Saboda ke ba fulani bace, doesn’t mean zan nuna maki banbanci, although akwai BANBANCIN KABILA tsakanin mu, saboda hakan yasa nakara son ki miss Olamide. So can I have digit please, kinga sai mu fara zumunci”.

“Hmm ban san shi a kai ba”. Bata gama magana ba, taji muryar Nafisa tace “ni nasani”. Nan taba shi digit din Olamide, ita kuma tana ta fushi, dan still bata so bashi numbern ta ba.
” So Mr Handsome, inba damuwa, zan dan rage maka jindadi, saboda Mide has to be inside likewise you”.
“Ba damuwa, nagode maki sosai kawar mu”.
“Awwwnn my pleasure mijin habibty. Amma sunana Nafisa”. Nafisa ta fada tana murmushi kar kunne.

Olamide na ganin yanda Nafisa keyi, tasan zata yi worst, sai ta bar wajan.
Nafisa ko ko a jikin ta, saboda daman ta riga tayi promising kan ta, duk wanda yace yana son habibtyn ta, kuma ya zauna mata, toh sai ta san yanda zata yi ta hada union din.
“Baka fada mun sunan ka ba”? Nafisa ta tambaya.
“Soo sorry for that, ko Olami ma ban fada mata ba, sunana Abdallah Umar Muhammad Yero”.
“MashaAllah, wayaga Abdallah weds Fa’iza. And yes wannan sunan, Olami din daka bata, yayi dadi sosai”. Nafisa ta fada.
“Daman sunan ta Fa’iza “? Abdallah ya tambaya.
“Ae, amma tafi amfani da sunan yoruban ta. Mu wuce ciki, kaga sai muyi hira a hanya, kafun mu shiga, kasan our presences is important”. Nafisa ta fada.
Suka tashi, suka kama hanyan hall din.
Sai kuma ta ce “kasan Olamide nada wani tsoro, ka daina ganin ta kaman she is tough, tana da tsoron kar familyn wanda ke neman ta su zo ba suyi accepting din ta ba, azo ana mata gori, shi yasa kwata kwata bata son ace mata zata auri dan north. Amma danAllah, inka san kaima zaka nuna mata BANBANCIN KABILA, kar ka ci gaba da neman ta. Olamide kaman yaya take gare ni, forget the fact din we are in the same level, ta girme ni with almost a year. Toh duk abun da aka mata kaman ni akayi wa. So am begging you in kasan kai da familyn ka zaku nuna ma habibty na banbanci, karka ci gaba da neman ta”.
Sanda ya numfasa, ya ce “my parent may not be the problem, amma ina da wani strict uncle, shi ne ma head of the family, da shi kawai za’a iya samun matsala, dan ya kafa mana dokan sai bafulatana kawai. Amma iyaye na are ready to accept anyone, in as far as am happy with my decision”. Ya fada yana murmushi.
“Hmm, wallahi bana kaunan inga habibty na cikin matsala, shi uncle din naka hope bazai muzguna ma ta ba, dan wallahi ina ji labari, ina iya zuwa inmai rashin mutunci enh”. Nafisa ta fada tana murguda baki.
“Ai ko da kin burge ni”. Abdallah ya fada, sai su biyu suka fashe da dariya, sannan ya kara cewa “danAllah kema bani digit din ki, kinga kaman ta keh zan samu kan qalbi ta”. Ya fada yana murmushi.
Nafisa ta kara fashewa da dariya, shi ma yayi joining din ta. Sai tace “su qalbi manja. Ai ko habibty na son sunan. Kaga bari in baka number na, kasan mun iso hall, kafun mutani su fara kallon mu”. Nafisa ta fada.
Nan ta ba shi numbern ta, sannan ya ce mata zai kira ta, da qalbin sa, sai suka yi sallama, suka shiga ciki, Nafisa taje side din mata, shima Abdallah yaje side din maza.

A cikin hall din kuma, ashe Asim ya gan su lokacin da suka zo kusa da kofar hall din, kuma lokacin suna dariya, sai yaji haushin kan sa, saboda a ganin sa, an riga shi samun ta, amma In Sha Allahu zai san yanda zai samu kan ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button