BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Da kyar ya samu ya shawo kan ta, har suka dan taba hira kadan kafun tace ta gaji barci take ji, suka yi sallama, ya kashe wayar.

“Ya ilahi, Allah kaga niyya na, bana son yin karya, amma ya na iya, this is the only way I can keep the love of my life. Bana son situation din da zai raba ni da ita. Na san yanzu dai su Abba are in shock ne, amma they will come around, har su zo su yarda da soyayyan mu. Kuma In Sha Allah zan yi duk a bun daya kamata, har su zo su gane ina son qalbi na, kuma qalbi na nada hankali, ga illimin addini, ga dabi’a mai kyau, ga respect. Kuma ai ko wani yare nada salihi da dan iska, ba yarbawa kadai keda su ba. Nama rasa abun daya sa iyaye suke irin wannan tunanin, kuma na rasa abun dayasa aka sa ma yarbawa lakanin nan. Ya Allah please guide me through, I hope our love conquers.” Abdallah ya fada yana thinking aloud.

Haka ya ita tunani, har barci ya dauke shi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Olamide kuwa da suka yi sallama ya kashe wayar, ta kalli Nafisa dake kwance kusa da ita, tace “na kasa yarda da shi, ina jin shi ajiki na kaman karya yake mun, kaman akwai abun da yake boye mun, saboda da safen nan fa ya kira ni ya fada mun wai bayan zuhur zasu hadu, amma in kira sa bayan asr kuma yace mun basu hadu ba, wani wai yana barci ne, kuma muryar sa bai yi kamada wanda yayi barci ba sannan yanzu kuma yana wani ce mun wai suna planning din yanda zasu masu magana just imagine habibty, is this not suspicious?” Olamide ta fada.
Ita kuma Nafisa inba kallon Mide ba, ba abun da take.
“Habibty fa dake nake.” Olamide ta fada tana daga mata gira.
“Toh me zan ce?” Nafisa ta tambaye ta.
“Mele.” Olamide ta fada tana murguda mata baki.
“Toh, amma you should trust him, relationships don’t work without trust.” Nafisa ta fada.
“I know, but am just finding it hard, saboda yanda yake magana ma zaka san there is something he is hiding, but I will put my trust in Allah, dan na san he is the only one that will never disappoint me.” Olamide ta fada.
“Yes he is. Ki kwantar da hankalin ki kin jin bibtyn Fisa?”
“Naji bibtyn Fa’iza.”

Suka ci gaba da hira, Nafisa na ta bata advice, har suka gaji, Nafisa ta koma kan katifan ta, kowannan su tayi barci.

Thanks for reading and been patient, wallahi abubuwa suka mun yawa .

Comment
Like &
Share.

~Zeexee ce~ ????️????️????️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

Dedicating this chap to my sweet and lovely cousins aunty Jamila and Jamila. I love you guys sooo much????????????????❤❤❤❤❤.

3️⃣3️⃣&3️⃣4️⃣

Bismillah

Ranan Friday, tunda short day ne, Abdallah ya dawo da wuri, nan ya samu, har sisters din sa, da matar hamma Sudais da jikokin gidan duka sun zo, amma banda na adda zee, saboda basu countryn.

Ya na fita daga motar sa, kananan yaran suka zo suna mai oyoyo, one after the other ya rinka daukan su.
Manyan kuma, suka zo suna gaishe shi. Haka suka bi sa a baya, ya gaishe da kowa da kowa, kafun ya tafi dakin sa, saboda yayi wanka, sannan ya chanza kaya.

Daya gama komai, sai ya koma parlor, ya samu kowannan su a parlor, suna hira. Ya kira baban cikin su, Jamila (yarinyar mijin Adda Wasila), ya mika mata leda cike da su chocolate, sweets, chewing gum, da dai sauran su, ya ce ta raba masu. 

Ya kalli umma a shagwabe ya ce “umman auta, ina jin yunwa fa”.
Adda Fadila na jin haka, ta ce “ai ba sai ka fada ma umma ba, ko ni sai ka fada min, bari in kawo maka. Anan zaka ci ko a dinning?” Ta tambaye shi.
“Anan zan ci.” Ya fada a shagwabe.
Yana fadan haka, ta tashi, ta wuce kitchen, ta je kawo mai abinci.
“Kai auta! A lan an kwaso gajiya ne ko?” Abba ya fada yaba shafa bayan sa.
“Sosai abba na, na gaji.” Abdallah ya amsa.
“Sannu Uncle auta, ai kana kokari sosai.” Aunty Aisha matar hamma Sudais ta fada.
“Ni kam ku bar shagwaba shi, wai ku baku san ya isa ace yana da yara ko yaro ba ne da zaku dinga wani shagwaba shi kaman baby.” Adda Wasila ta fada.
“Ai shi ne, ji yanda kuke yi dashi.” Umma ta fada, sai ta kalli Abdallah, ta ce “kai kuma ka tsaya a wajan a dinga maida ka yaro.”
Tana gama fadan gakan, sai ga Adda Fadila niki niki da Abincin Abdallah a kan tray, sai ta tura stool, tasa a gaban shi, kafun ta ajiye abinci, ta ce “A ci lafiya auta.”
Suna hada ido da Umma, taga irin hallon da take mata, sai ta kau da kai.
Umma tace “ku kuka sani, in yaso ku maida shi dan shekara biyar.”
“A’a Hajiya ya ishe ki haka. Yaro ya kwaso gajiya, instead ki lallabe shi, kina kara mai gajiya akan gajiya. Ya samu masu mai kuma kina complain. Kar ki damu, inya yi aure, ya rage ni dake, zaki san value din auta. Ko auta.” Abba ya fada yana kallon shi.
“Sosai ma, idan na auri Ola….” Sai yayi shuru, ya ma manta, bai san lokacin da sunan ya fito daga bakin sa ba.
“Ka auri wa?” Adda Wasila ta tambaya.
“Babu, ina auri all my wives nake son fada.” Abdallah ya fada yana murmushin dole.
“All your wives kuma?
Ashe mata da yawa zaka aura a rana daya.” Umma ta fada.
“Kai Umma, ai uncle auta ba haka yake ba, kawai dai wasa yake. Kuma ai yana da ikon auran matan hudu.” Aunty Aisha ta fada.
“Toh ai shi ne, in yaso ya aure su a rana daya, but the fact still remains, zaki yi missing din auta.” Adda Fadila ta fada tana murmushi.

Haka suka ita hira, Umma da adda Wasila na zolayan Abdallah, kafun shima hamma Sudais yazo, teams din suka cika 3-4, wannan team din na zolayan Abdallah, wayannan kuma na bada amsa.

Daman idan 6:pm yayi, ko wannan su ke komawa gida. So by 5, Abdallah ya ma hamma Sudais da adda Fadi text, yace su hadu a balcony, shi zai yi kaman yayi fushi, ya fito, su kuma su biyo shi.

Haka ko aka yi, adda Wasila na dukan shi a baya da wasa, ya hada rai, ya tashi ya bar wajan, suma suka biyo shi a baya. Da suka fita, suka yi dariya kasa kasa, hamma Sudais yace “toh me kake son fada mana ne, ka fada yanzu, kafun su ga mun dade, a fara suspecting din wani abu.”
“First of all, ina son in maku godiya for like her, na gode maku sosai, Allah ya saka maku da jannah.”
“Amin.” Su biyu suka amsa.
“Secondly, akan yandan zan fada masu abba ne, nace ko zaku zo ne gobe ko jibi, ku taya ni mu fada masu please.”
“Any day is okay with me, but zanyi preferring din Saturday more.” Adda Fadi ta fada.
“Toh muzo Saturday. Allah yasa su yarda, Allah ya sa ka auri Olamiden ka, they will be pleased and happy to accept your relationship In Sha Allah.” Hamma Sudais ya fada.
“Amin suka amsa tare.”
Sai suka koma ciki, aka ci gaba da hiran, da su.

6:pm nayi, alokacin sun taya Umma girka dinner, kuma suma sun ci, kafun ko wannan su ya ja motar sa ya bar gidan, amma banda adda Fadi, saboda ita bata dashi, so sanda ta jira mijin ta, ya zo ya dauke su, ita da yaran ta, kafun suma suka bar gidan.

A rannan dai, Abdallah ya kwana ya na tunanin yanda gobe zai kasance in Allah ya kai mu da rai da lafiya, Allah yasa su yarda. Daya fada ma Mide ma lokacin da suke waya, ta nuna mai damuwa, yana ta kwantar ma da hankali, alhalin ko shi ma hankalin sa bai kwanta ba.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya kashe wayar, ta tashi da sauri, ta shiga toilet, ta yo alwala, ta fara nafls, saboda hankalin ta yaki kwatawa kwata kwata, sai taji kaman this phone call was there last goodbye, amma daya ita kwantar mata da hankali lokacin da suke waya, she felt a little bit alright, but still ba wai hankalin ta ya kwanta bane.

Ta ita yin nafil, tana kuka, ya ilahi, she true loves Abdallah, but what will she do idan iyayen sa suka ki relationship din su, ina zata sa kan ta. Haka dai ta ita sallah tana kuka, tun kuka baya fita, har ya fara fita.
Da Nafisa taji kaman tana kuka, sai ta bari sanda ta yi tayya, tayi sallama, kafun taje gaban ta, tace “what is it again habibty, wai me yasa almost every time idan kuka gama waya sai kin yi kuka, kuma idan akan iyayen sa ne, kar ki damu everything will be alright.
Wallahi if not because you are already in love with him, dana yi advising din ki kuyi breakup haba what is it self, kullum ke kenan cikin tashin hankali, baki da natsuwa, kullum sai kuka. Ni kam idan relationship din nan ba zai sa ki dinga samun kwanciyan hankali ba, toh ki bari gaskiya.”
Da jajjayen idon ta ta kalli Nafisa ta ce “abun da zaki ce kenan?” Ta tambayi Nafisa hawaye na zuba a idon ta.
“Ba haka bane, amma ni fa kwata kwata bana son inga hawayen ki.” Nafisa ta fada tana share mata hawaye.
Cikin jin haushi ta ce “ki kyale ni. Say the truth, tunda muke tare, na taba irin halin?
“A’a, ni fa habibty, bance ki daina son shi ba, I said da baki son shi yanda kike son shi ba, dana baki advice kuyi breakup.” Nafisa ta fada.
“Shi yasa nace ki kyale ni, if you can’t give me advice, just let me be. Ni kadai na san abun da nake ji, ni nasan irin son da nake masa, so if you can’t be with me in this time of worry, then ki kyale ni.” Olamide ta fada, sai ta tashi ta je ta kwanta akan katifan ta. Takaici duk ya bi ya dame ta. Nafisan data kamata ta kwantar mata da hankali, tana mata irin wannan maganganun.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button