DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Staff, ma’aikata, yaran gidan marayun aka fiffito aka taru awaje, daman ance bad news yafi yanda wuri nanda nan aka cika ko’ina, aka cika gaban clinic da saida Dr Kemi da Dr Ayo suka kira security gate biyu sukazo, akasa kowa yakoma various places dinsu, Baba Mani ne kawai da Mama Iyami aka bari suka shiga asibitin har zuwa dakin da aka kwantar dashi likitoci akanshi ba’a bari sun shiga ciki ba, fuskarshi tai mugun jan da saita baka tsoro, gefen idanunshi na dama ya kumbura dan hardan tsagewa yayi jini yadan fito, kasa daurewa Mama Iyami tayi ta fashe da kuka a rayuwa tanason Waleed, bata taba haihuwa ba, mijinta yarasu, an koreta gidan haya yazo batada inda take kwana, abakin titi takoma tana bara tana tara kudin datake samu danta kama haya, wata rana tana cikin baranta taga anyi parking, Waleed yafito kai tsaye yace mata mesa kike bara Mama, tace banda kowa, mijina yarasu, banda y’aya Allah baitaba bani haihuwa ba, ankoreni agidan haya, bara nake natara kudi nasami matsugunni, budan bakinshi bazaki kara baraba, sanan yajuya yay wajen motarshi yace zomuje, gabanta nafaduwa amman hakanan taji zuciyarta nacemata tabishi, motar ta shiga, yana zaune agefenta ga basket da alamun abinci ne aka dafamai agida, dauka yayi duka basket din yabata yace kici, budewa tayi ta shigaci kaman bata tabacin abinci, yakaita gidan marayun shi, yakaita asibitin shi yasa tai wanka, aka kawo mata kayan asibiti tasaka yadubata tsaf bata dawani ciwo sai maleria yay treating nata, sanan dakanshi yakaita girls hostel yabata daki na musamman dake dauke da komi sanan yace “aikinta kawai ta dinga kulamai da activities din yaran nan, she’s in charge anan section din, zai dinga biyanta duk wata, sanan yasa akayo mata dinkunan kaya masu kyau aka kawo mata, tundaga ranan kulada ita yake to the extend har Ammi tasani tanada number ta, Ammi data ambata aranta yasa taciro wayarta ta shiga neman number Ammi tana kuka sosai, kaman wayan zata katse sanan Ammi ta dauki wayan, cikin kuka Mama Iyami tace “Allah yataimaki Hajiya amin afuwa hala ban kira alokacin daya kamata ba, amman dolece tasa nakira” takara wani irin rushewa da kuka dayasa gaban Ammi ya shiga dukan uku uku tama kasa magana tsabagen faduwan gaba dan tanada hawan jini, Mama Iyami cikin kuka tace “Hajiya kome kikeyi kibarshi kizo ba’asan ko karshen ne yazo ba, wayyo Allah na Hajiya” takara kecewa da kuka dayasa Ammi bakinta yafara motsi tana kokarin furta magana takasa dakyar tana wani irin nishi tace “k…..kar…..shen wane…. Iya…..mi”? Cikin wani irin mahaukacin kuka kaman wacce akama mutuwa Mama Iyami tace “karshen Dr Waleed Hajiya, Mr Arham yama Dr Waleed shegen duka, yanzu haka Dr Waleed baisan inda kanshi yakeba, likitocin mu gabaki daya na kanshi baisan inda kanshi yakeba ana kokarin ceto rayuwanshi, saisa nace kizo idan ma cikanwan ce yacika agaban ki, ai Mr Arham bai kyauta ba da kyar muka kwaci Dr Waleed a hannunshi Hajiya, dan Allah kizo yanzu koda karshen ce yayi ta a hannunki, wayyo Allah na Dr Waleed” tarushe dawani rikitaccen kuka tana katse wayan, majina shabe shabe.

Wani irin baya Ammi tayi zata zube akasa daidai lokacin mai aikinta tafito daga kitchen dauke da katuwan kulan abinci, wani irin sakin kulan tayi akasa tai kan Ammi da gudu kafin Ammi ta zube ta tareta tareda ihu tace “Hajiyaaa!” duk masifar Ammi tana bala’in sonta dan tayi aiki a gidaje da dama bata tabayin aiki agidan dataji dadi irin na Ammi ba, ganin Ammi ta sume yasa ta kuma ihu. “Mai gadi, direba, duk wanda yake awaje ya shigo ku taimake ni, Hajiya ta suma” da gudu ma’aikatan gidan suka shigo, su mai gadi naganin Hajiya assume sukai kitchen suka fitoda ruwa agora yayyafa mata ruwa sukayi tawani irin sauke ajiyan zuciya tare da bude idanunta, ahankali take kallonsu one by one, kafin ahankali tace “ku kaini wurin Waleed gida a orphanage, dan Allah ku kaini wurin Waleed dina a orphanage”.
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

        ✍️ M SHAKUR 





                    2️⃣9️⃣

FREE PAGE
Hayaniya da zata iya cewa tunda take a asibitin bata tabajin irinshi ba, hayaniyan ya mugun cika mata kunne yasa tabude idanunta ahankali tana kallon dakin, idanunta sunmata shegen nauyi sabida bacci bai isheta ba, sosai kirjinta taji yana wani irin faduwa, ward din datake gabaki daya ta kalla babu kowa cikin ward din sai ita kadai dake kwance akan gadon an lullubeta da bargo sanan anmata parking gashinta gabaki daya anyi mata parking na ponytail, ihu dawani irin masifa dataji yana sauka akan kunnenta yasa ta yaye bargon jikinta ta tashi zaune dagakan gadon tana kalle kallen dakin, ihu da hayaniya da masifan da akeyi jitake kaman a brain dinta akeyi, sakkowa tayi dagakan gadon tazira pink slippers dinta dake wajen sanan tadau Teddy dinta ta kankameshi akirjinta ta shiga tafiya ahankali kaman ana kiranta, hannu tasa tabude kofar dakin datake tafito tana tafiya dogon jelar gashinta na lilo tana kankame da Teddy ta kaganta kaman kasace ta kagudu, tai bala’in kyau doguwan yarinya da ita, batada wani kiba tana sanye da gown din asibiti daya wuce guiwanta da kadan, batada wani cikan kirji sosai, kirjinta moderate yan daidai irin na yaran larabawan nan, kanta an mata parking an daure da ribbon gashin na lilo, tundaga nesa take hango su Ammi, Mama da Mom na hayaniya dayasa ta tsorata tasake kankame Teddy gam gam idanunta na kawo kwalla dan tsoro taji sun bata hakan yasa ta shiga waige waige tana neman Waleed, fitowa tayi daga corridor ta shiga tafiyanta kaman bana mutum ba a reception din su Mom ko kadan basu lurada itaba, tunawa da ranan Waleed yayi kofa da ita yafita da ita yasa tai wajen kofan da sauri tana cikin tafiya kaman ance ta kalli glass din kofar emergency ta hango Waleed kwance kan gado fuskarshi a kumbure yasa tai dakin da sauri, hannu tasa tabude kofan ta shiga duksu Ammi basu lurada itaba, maida kofar tayi tarufe, ganin ciwo ajikinshi yasa tawani irin saki Teddy ta akasa tai kanshi da sauri, hannayenta tadaura kan cikinshi tabude bakinta tana kokarin ma magana takasa sai kawai tasaki kuka sosai tahau jijjigashi, amman bai motsa ba, kai hannunta tayi ta daura kan gefen idanunshi daya kumbura suntum ta taba tana kuka sosai tanaso tai magana tama kasa, bama tasan sunanshi ba amman sotake yabude ya kalleta, girgiza shi tayi tace “ahhhh, Umm mm” kafadarshi mai lafiya ta bubbuga tana kuka da kyar bakinta ya iya furta. “you, youuuuuuu, yo…..u” tasaki kuka sosai kaman zata mutu saikuma tadaura kanta kan kirjinshi tahau kuka tana jijjigashi tace “youuuu” sosai take kuka, takai kusan 5min ahaka tana kuka tana jijjigashi sanan tadago kanta ahankali ta kalli fuskarshi saikuma tajuya ta kalli TV dakin dake aiki da babu kara ko kadan dan anyi muting television din, tashar AIT ke aiki suna wani series na Korean film.

Daidai wata yarinya tashigo dakin wani namiji mara lafiya tana kuka tana zuwa kawai ta duka ta daura bakinta kan nashi sai saurayin ya farka, tana ganin haka da sauri tana kuka ta kallai, kafin ahankali tana kuka sosai takai fuskarta saitin nashi tana kallon fuskarshi yana mata wani irin kwarjini ta kafe pink lips dinshi da ido kafin ahankali ta saukar da bakinta kan nashi, tasaka all his lips inside her tiny mouth tai shiru tana kallon idanunshi ita adole tana jira yabude ido shima kaman na film hawaye na zuba daga idanunshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button