DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

        ✍️ M SHAKUR 





                   4️⃣

FREE PAGE
Direban gidansu Arham yatura dazasuje su dauko Amarya da kawayen ta to the event centre cus 9 za’a fara dinner dasu Hasim da friends dinsu, saida ya tabbatar sun tafi sanan yakoma cikin gidan, Waleed yasamu azaune kan kujera yana aiki da laptop dinshi ko ajikinshi kaman ba shine angon bikin ba, maida kofan Arham yayi yarufe ya karaso cikin dakin tsayawa yayi chak akanshi yace “muje ka shirya mutafi ai ba’a office kakeba yanzu kana gida” dan dagokai yayi ya kalli Arham din wata yar gajeren tsaki yaja yace “Omg wai why did u initiate this dinner stuff at the first place ma eh? Goddd! Mutum cannot rest again yayi abinda yakamata, am so so sick of this wedding, gosh!” girgixa kai Arham yayi ganin yanda yake masifa bil hakki ya karbe laptop din tareda shutting nashi down yarufe yarike ahannu sanan ya mikamai hannu yace “muje mushirya” ahankali yatashi Arham yabishi da kallo yana sanye da faran t-shirt sai wani 3quater short daya tsayamai wajajen gwuiwa shima fari, kafafunshi sanye cikin farin bathroom slippers, gashin kafarnan kwance lub lub irin na mugun dan hutun nan. Ahankali kaman wanda kwai yafashe wa aciki yake tafiya Arham yabude kofar hadadden bedroom dinshi suka shiga ciki, wajen wardrobe dinshi yayi yafito dawasu kaya da bama abude ba yazube su kan gadon sanan yabude ya shiga shiryawa cikin wata white suit na ermenegildo zenga, suit din yamugun fitting nashi daga kasan waje akamai order suit din aka tahomai dashi, sanan yadauki cover shoe dinshi na dinner sabo fil Black, designers shima na Testoni, tsayawa chak Arham yayi yana kallonshi yamugun yin kyau sai kallon kayan yake, juyowa Waleed yayi ya mikamai bow tie din dake hannunshi yace “tayani sawa blood” karban bowtie din Arham yayi yashiga samai kaman ba zaice komiba saikuma yace “amman wanan takalmin da suit din bashi mukaje muka sayo tareba a dunes ko?” girgiza mai kai yayi yace “Uncle yazomin dashi daga Ukraine jiya daya iso” gyadamai kai Arham yayi baisake cewa komiba yana gama samai yawuce yaje wardrobe yaciro wayanda suka sayo tare, yazaro tashi suit din black, dan abokan ango black suit zasu saka shikuma ango white, ya shirya tsaf sanan yataho key motar Waleed ya dauka yace “let’s go” fitowa sukayi daga dakin, har zasu fita daga falon Ammi ta shigo dakin sun kusan cin karo, binsu tai da kallo yanda suka mata kyau sosai kafin ta sauke idanunta kan Waleed dayay mata wani irin kyau batasan lokacin data saki wani kayataccen murmushi ba, wucesu tayi tazauna kan sofa sanan takalli Waleed tace “zonan Son” tahowa yayi ahankali kaman wanda baison tafiya yazauna kusada ita inda take nunamai, hannunta takai tai cupping face dinshi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi kafin ta shafa fuskar tace “you look so much like your father today, kayi kyau sosai, Allah ya maka albarka kaji” dan lusme ido yayi yana danne abinda yakeji a zuciyan shi yace “Ameen” purse din data shigo dakin dashi ta ijiye agefenta tadauka tabude taciro rapas nayan dollars guda biyu tamikamai tace “gashi kama y’ata manni dasu” karban kudin yayi ahankali dan baiso yaki karba taji haushi, rungume shi tayi ahankali taredamai kiss akumatu tace “stop being sad, I love you son, kaci abinci kuwa?” juyawa da sauri Arham yayi yafita daga dakin ya shiga mota Waleed din yay zamanshi a mazaunin direba, he just wish inama shine Waleed, kome zaiyi iyayen shi basa tabamai fada komin girman abun, unlike him da kullum abu kadan Umma fada takemai, abu dan kankani sai fada, Waleed ko abinci ma abaki ake bashi, bodyguard ma saida sukai fada da Ammi sosai dan anso kusan 10 sudinga binshi da kyar ya karbi daya wanda yadawo direban shi, bama abari yasha wahalan neman mataba aka samomai yar gidan masu kudi, graduate lawyer fa dudda dai bai taba ganinta ba aka bashi, just look at suit din da uncle dinshi ya kawo mai daga Ukraine, suit din ermenegildo yana costing about 22 to 28000 dollars, suit din jikinshi kadai worth a fortune dan yakai almost 8.8million naira a kudin Nigeria, takalmin kafanshi na Testoni kusan 3m ne shima, gata da dadi is beyond tunanin kowa ko shima inda bai gani da idanunshi ba dabazai taba yarda ana bama yaro gata irin gatan da ake bama Waleed ba, why was he born from the poor home? Maisa Umma ta auri Abban shi wani Malam Muhammad Bala, malamin islamiyya? Yataso ko gidan kansu basuda shi sai gidan haya, gidan dakuna ashirin da biyu da bayi guda biyu daya na kashi daya na fitsari, daga baya kuma yazo yarasu ya barsu cikin talauci, Waleed ne ya shigo rayuwan shi ya chanza mai komi….. Bude motan da akayi yadawo dashi daga daga dogon tunanin dayaje Ammi ne tabude ma Waleed din kofar motan tana kallon Arham tace “son ina gajiya” cikeda kunya dan yafi sakewa da Mom sabida ita tanada raha sosai while Ammi batada raha tanada fada, bata cika wasa da yaraba, aduniya in tana tareda Waleed ne kawai zaka dinga ganin dariyanta da murmushi ta abanza, da farkoma ya dauka bata sonshi ne sai daga baya ya lura haka Allah yayi ta ita kawai bamai yawan wasa da sakema yara fuska bane, cikeda girmamawa ya sauke fuskanshi yace “ina yini Ammi, ya taro” tana kokarin saka Waleed dake mata wani shegen shagwaba a mota tace “Alhamdulillah Arham, ai tuntuni muna tareda mahaifiyarka ma wlh, mamanka akwai kirki, kaga Arham gashinan drive him safe please, saikun dawo, bye Son, have fun okay, if u need anything ka kirani zan aikoma dashi” ta shafa kan Waleed din dake tura mata baki tana murmushi, kunna motar Arham yayi yaja Ammi na daga musu hannu tana murmushi, saida sukadan yi nisa ahanya sanan ya kalli Arham din dayaga yay shiru kuma ba halin shi bane yamika mai rapas din dollars din da Ammi tabashi duka biyun yace “use this” da sauri Arham ya kallai saikuma ya maida kanshi kan tukin yace “a’a, abinda Ammi tabaka zan karba” murmushi yayi kafin ahankali yace “take it inada wanda zanyi amfani dashi already” “shikenan” Arham yafadi ahankali kafin yace “thanks blood” murmushi Waleed yamai baice komiba, ahaka har suka karasa event centre babu wanda yakara magana cikinsu, daman yawanci in suna tare Arham ne mai kawo hira shi Waleed iya kanshi um a’a kokuma yan maganganu kadan, parking yayi yace “ka zauna aciki, I need to confirm in Amarya ta iso dan tare zaku shiga Hall din” bai jira amsanshi ba yamaida kofan yarufe yay wurin entrance din daidai zai shiga Abdul suna saukowa daga elevator tareda Salima suna hira shiru sukayi ganin Arham, Salima tace “you must be Arham ko? Best friend na ango” dan murmushi Arham yayi yana binta da kallo tana sanye cikin asshobi kawayen Amarya pitch yace “yeah nice to meet you Mss Salima” murmushi Salima tayi tana kallonshi ganinshi shima kyakkyawa sosai saidai dudda kyanshi baikai kyawun Dr ba, kuma Dr yafishi kaurin jiki da cikama mutum ido, ganin kallonshi take yasa ya katse shirun yace “ina Amarya? Cus they’re going in together” “eh tana wani daki asama where is Dr?” juyawa yayi yace “lemme get him” har wajen motan yaje yabude motan ya kalli Waleed dake dandanna waya yace “let’s go ango” ballamai harara Waleed yasakeyi hakan yasa Arham yace “sorry mana ai kuma gaskiya nafadi kai angon ne” ahankali Waleed yafito yana gyara suit din jikinshi su karan kansu su Abdul da Salima kallonshi suke yawani irin yin mugun kyau cikin white suit din dasukai mugun fitting dinshi maida kofar Arham yayi yana kallonshi yace “muje” ahankali suke tafiya har zuwa gaban entrance din Salima takasa daina kallonshi, dan kallonta yayi sanan ya kalli Abdul batare dayace musu komiba, anatse Abdul yace “sannu da zuwa Ya Waleed” bai kallesu ba yacema Arham dake kusadashi “let’s go” wucewa sukayi dukansu suka shiga lift din yakaisu 4th floor, wani daki Salima tabude tana kallon Arham dan Waleed mugun cika mata ido yake tace “ku shigo tana nan” shiga ciki tayi suka hada ido da Ilham datasha uban gayu anmata makeup tasaka wani gown white daya mata fitinannen kyau ita kadai zaune kan wani Royal chair tai kyau sosai, cikin tafiyan nan nashi mai daukan ido daidai ya sawo kanshi cikin dakin Arham biyeda shi abaya, ahankali ta mike tsaye tana kallonshi hada ido sukayi hakan yasa ya tsaya chak shima, wani irin dadi ne ya lullubeta batasan lokacin data saki murmushi ba da sauri tazo wajenshi batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi, ihu dakin ya dauka Arham ya shigo dakin da kyau yana kallonsu yana murmushi, da sauri Salima taciro wayarta tafara musu hotuna, ahankali yadaga hannayenshi ya rungume ta back, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta shige jikinshi sosai tana shakan kamshin dayakeyi, kaman ta jawo gobe takeji ayi a daura musu aure tayi ta dawo matar this ajebota handsome rich kid, “wai anan zamu kwana ne” Abdul yafada yana dariya, ahankali tasake shi cikeda jin kunya hakan yasa shima ya saketa, juyawa tayi suka hada ido da Arham da tundazu yake kallon bayanta Allah Allah yake yaga fuskarta, dan murmushi tayi sanan tajuya ta kalli Waleed din, dan lumshe ido yayi yabude kaman mai rada yace “my best friend, my brother, my blood, Arham” wani irin murmushi tayi ta juya ta kalli Arham tace “the great Arham nasha jin labarin ka tun abakin Ammi, my husband best friend childhood friend, so nice to meet you” dan murmushi Arham yayi yakasa daina kallonta yace “yes your husband is my blood we’ve been together since childhood, and he means the world to me, so ki kula min da abokina dakyau” dan dagakai tayi ta kalli Waleed kafin ahankali takama hannunshi tarike gam tana kallon face dinshi tace “I was born to do that, I love you so much Doctor na” ganin akwai mutane awajen yasa ahankali yace “thanks” wani iri Arham yaji he just feel inama shine yake da wanan soyayyan, Waleed is the definition of yaran da ake haifa da silver spoon abakin su, Waleed is just surrounded with love ne ta ko’ina, just look at yanda wanan hadaddiyar classic graduate lawyer yarinyar nan kesonshi tama mutu akanshi but yana yanga, infact baima sonta, baima son auren ko kadan, yarinya ga shegen kyau, itama yar masu kudi but yake yanga, he just wish zai sami yarinya haka dazata dinga mutunmai dinan, Salima ne ta katse silent din tace “I think we should go anfara event fa tundazu” fitowa sukayi duka atare, bayan an sanar da isowansu a hall aka kunna music suka shiga cikin kasa ita sai hotuna ake musu, sosai akai event kala kala duk in Ilham zata dagokai saita hada ido da Arham dake kallonta saidai ta sakanmai murmushi ta maida hankalinta kan Waleed, anso sai asuba za’a tashi 1 nayi Waleed kaman zaiyi kuka yakira Arham awaya bai dauka ba, ganin duk yay wani iri yasa Ilham tace “me kakeso baby?” batare daya kalleta ba murya chan kasa yace “nagaji i think atashi” ayanda yay maganan saida yasa har wani lumshe idanu tayi, Waleed is handsome gawasu mayun pink lips dayake dashi dake shinning kaman ka lashe, she can’t wait to have a taste of them, kasa cemishi komi tayi sai binshi take da kallo, ganin kiss call dinshi yasa Arham yazo gayamai yayi atashi yagaji bacci yakeji, Arham baimai musu ba ya sanar da dj a kunne, yan abubuwa kadan akayi aka tashi, dudda yanda Waleed keso yaje gida Arham yace mai ba haka akeba shizai raka Amarya gida sanan saisu tafi, yanaji yana gani Arham yasa aka saka Amarya a bayan motansu yasa Waleed din kusada ita sanan yakoma gaba ya shiga ya tukasu, sun danyi nisa da tafiya Ilham ta matsa kusadashi ahankali tareda saka hannunta kan nashi ta kama gam, shiru yamata yana dan lumshe ido kafin daga baya bacci yay nasa ran kwasheshi ya daura kanshi kan kafadarta, wani irin dadine ya kasheta tai dan murmushi tace “haka abokinka keda saurin bacci?” ta glass din gaban motan ya kallesu yay dan murmushi yace “ai zakisha shagwaba, haka Allah ya yishi, mijinki shagwababbe ne” murmushi tayi ta shafa fuskarshi bata sake cewa komiba shima Arham haka har suka kai gaban gidansu, ahankali ta gyaramai kai tareda pecking nashi ta kalli Arham daya bude mata mota tace “good night our blood” murmushi yayi yace “good night our wife” gyadamai kai tayi tawuce yamaida kofan yarufe yana dan satan kallon bayanta, ta shiga gidan su, dakinta tawuce direct inda Salima da wata kawarta suke zaune harsun chanza kaya dansu tun dazu suka iso itakuma dayake ahankali Arham ke gudu saisa basu iso dawuri ba.
[11/1, 11:44 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button