DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Suna shiga sukai parking gaban dankareren asibitin dako wani asibitin cikin gari albarka, already nurses harsun gunguro gado dan sojoji sun riga sun sanar dasu, daura ta mazan sukayi akan gado nurses din na kallonta suka gungurata ciki, Sojan daya biyosu ciki yace “we will take it from here thank you” yanuna musu motarsu, komawa cikin motar sukayi sukabar orphanage din.
Wanan kenan!!!

Assignment din dazasuje yau shine hiking with benefit, sunan dasuka bashi kenan, chan wani mouthain zasu da tun jiya Waleed yatura maaiktan shi akaje dan dubawa dacire duk wani abu dazai cutar mai da yara sanan akai planting various gift awajaje daban daban dan za’ayi treasure hunt duk wanda yasamu wani abu yazama nashi halak malak saisa aka sama hiking din suna Hiking with benefits, yaran sai jin dadi suke, they’re super excited, gabaki dayansu yau sun saka sport wears da p-cap harda yan matan cikinsu, bayan kowani t-shirt anrubata sunan gidan marayun koda yaro zai bata za’a iya dawo dashi, ko tracing daga inda yake, kasancewan Ilham tacemai zata bishi yasa sune last to arrive venue din, bodyguard dinshi ya tukosu, tunda taga harda yan mata da sun isa aure a marayun yasa taji tama tsani aikin, sanye take da jeans da riga da sneakers amman saida yasa tadaura after dress akai, shikuma yana sanye da jeans da riga sai canvas da p cap akai, yay bala’in kyau idanunshi sanye cikin bakin glasses dan rana tafara fitowa takwas ne na safe dayan mintuna, Arham kawai suka samu akasa bai riga yafara hawa ba gabanshi da manya manyan jaka guda biyu wanda bottles water ke ciki da glucose incase wani yaro yagaji, kallo daya Ilham tamai tadauke kai tace “Barka da asuba” Barka yacemata yana kallonta saikuma yay murmushi ganin bata iya kallonshi tun bayan abinda yawakana tsakaninsu yace “blood your wife tayi kyau sosai cikin english wears dinan da sneakers menawani sa tasaka after dress akai?” jaka daya Waleed yadauka yagoya abaya sanan yace “she is married ba kyau ana ganin jikin matan aure, let’s go” yay maganan yanayin gaba yafara hawa kan dutsen, dan kallonta Arham yayi suka hada baki, lashe lips yayi irin kinyi kyau dinan u look yummy sanan yabi bayan Waleed, murmushi tayi ganin yanda ya mutu akan gayun shiko Waleed koya cemata tai kyau baiyyiba, ajere suke tafiya Waleed nagaba Arham atsakiya sai ita abaya, ahaka har sukakai saman mountain din kafanta kaman zai katse ta gaji, sauke jakan Waleed yayi yana murmushi ya kalli yanda yaran suka zuzzube akasa suna haki sai zufa suke nanko dazu sunfi kowa kosawa a tafi yace “are you tired children tun yanzu?” atare sukace eh, dariya yayi yashiga ciro rowan yana raba musu suna karba sauran ma’aikatan ma nabasu ruwawwakin dan kowa saida ya goyo jakan ruwan cikin maaikatan, wayanshi dayashiga kara yasa yamikama wani staff dinshi yamai alamu yacigaba da raba musu sanan ya matsa gefe yaciro wayan, ganin daga orphanage dinshi ake kiranshi Dr Kemi yasa da sauri yay picking yakai kunnenshi yace “talk to me Dr Kemi” anatse matan tace “Sir we have an emergency case, we need you here ASAP” bayan shi Dr Kemi is the second best Dr yakedashi a hospital dinshi, ganin ita da kanta tana fadomai akwai emergency ana bukatan shi yasa yace “what happen? Who is sick?” anatse tace “Sir a patient was brought into the hospital few minutes ago….” da sauri yace “is it a BID (brought in death) case”? Da sauri tace “no no sir, is not a BID case amman close to BID” “kaman ya close to BID? Dr Kemi skip the talk and cut to the chase” ajiyan zuciya tasauke tace “Dr Warbai 4 men suka kawo yarinyar nan cewan an tsinceta acikin ruwa, karkashin gadan murtala Muhammad Bridge in zaka lokoja, I believe them cause the evidence was obvious” anatse yace “did she sustain any injury?” “yes sir, yes, akwai bruises ajikinta ko’ina, sanan kanta yafashe” “what is kanta yafashe? Da kanta yafashe da BID za’a shigo da ita, tell me the exact lobe a head dinta daya fashe, is it the temporal lobe, frontal lobe, parietal lobe, ko occipital lobe, wanne ne yafashe?” anatse tace “occipital lobe dinta ne tasami injury, wajajen keya, wajen yatsage yafashe, the problem now is I believe water yay finding his way to her cerebellum, naduba eyes dinta sun karkace, I think her vision sight has been distorted” cikeda damuwa yace “that’s metamorphopsia, yawanci head injury nasaka hakan” ajiyan zuciya Dr kemi tasauke tace “she is unconscious, pulse dinta kadan ne sir” wani irin ajiyan zuciya yasauke yama kasa magana saikuma yace “I will be on my way just stabilise her condition” da sauri tace “ejo, mabinu Sir, listen sir” ahankali yace “yes! Kince”? anatse tace “Sir am the only Dr on duty am sorry bazan iya duba yarinyar nan ba trust ne indai yarinyar nan bayar ruwa bace to mami water ce, I just got married, I don’t want my husband to loose me” wani mugun tsaki yayi ya katse wayan yajuya ya kalli Arham daketa rabo itama Ilham na rabon, karasawa wajen yayi ya kirashi “blood” da sauri Arham yadago ganin yakira shi yasa ya ijiyema yaran snacks din yataho wajenshi yana kallon idanunshi yace “yanaga idanunka sun chanza? Menene?” ahankali Waleed yace “akwai emergency a orphanage a clinic, Dr Kemi isn’t helping matters, I need to be there now, but once nashawo kan case din zan dawo koda gobe ne, please don’t tell Ammi nakoma Abuja koda takirata, I don’t want her to know, zanbar Ilham ma anan, dankoda nace zanje da ita zata mayarmin aiki bayane ko?” da sauri Arham yace “yes kabarta anan aiduk muna tare she will be fine, but tell her first kafin katafi sabida karta damu kasan tana sonka dayawa, don’t worry I will take care of her, go and save life Allah sa muji alkhairi” side hug Waleed yabashi yace “thanks blood” sanan yakira Ilham dake wajen yara. “Khadija” da sauri Ilham tadago kanta saikuma ta tashi tazo inda yake tana kallon fuskarshi ganin kaman yanayinshi ya chanza tace “baby menene”? For the first time yakai hannunshi kan fuskarta kaman mai son lallashinta yace “I need to go to Abuja yanzun nan Ilham, ga Blood na he will take care of you, anything you need just let him know, zan dawo once nai stabilising case din, take care of yourself okay” gyadamai kai tayi kaman zatai kuka tace “Allah ya kiyaye” fuskanta yadan shafa yace “Ameen bye” gyadamai kai tayi, bye yama Arham yawuce, bodyguard dinshi yabishi mota ya shiga already akwai wallet dinshi ajikinshi daman, Airport yakaishi direct yabi available flight to Abuja baima sami business class ba haka yay managi da economy, yana kaiwa yadau drop direct to his orphanage, sojojinsu zasu taresu yasaukar da glass suna ganin shine aka bude gate da sauri ana gaidashi motan yawuce ya shiga, har gaban clinic dinshi yafito yabama direban kudaden dabaisan iya adadinsu ba.

Shiga cikin clinic din yayi da Dr kemi yafara haduwa a reception baibi takanta ba yawuce washhand basin dake reception dinshi ya wanke hanunshi da hand-wash sanan yatare senitizer yay amfani dashi yajuyo lab-coat dinshi Dr Kemi ta mikamai cikeda girmamawa tace “welcome Sir” gyadamata kai yayi yakarbi lab coat din yasaka daidai lokacin wata nurse takawo mai faranti da handglove kekai, dauka yayi yasaka sanan yace “where is the patient Dr Kemi” adan daburce Dr Kemi tace “ICU Dr” tafiya yafara yay hanyar ICU tana biyeda shi da nurse guda daya, Dr Kemi tace “Sir ko nurses dinmu sunce karmu tabata, kaganta wlh she is the definition of ba mutum bace” tsaki yayi baice musu komiba tsabagen takaici har sukakai gaban ICU din, ahankali yadaura hannunshi kan handle din kofan ya murda kafin ahankali yatura kofan.
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button