DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Othman Benjalloun dattijo ne dakeda shekaru 62 aduniya, bala’in mai kudine agarin morroco, agabaki dayan garin ance bayan Mohammed VI wanda yake number 1 mai kudin garin, Othman shine the second richest person in the whole morroco, yana harkan banking insurance, yanada bankuna yanada kasuwanci da dama, matayenshi uku aduniya, Mahaifiyar Widad itace ta farko wanda a yanzu ta rasu, sai matarshi da biyu wacce Widad takira da Umm, sai ta ukun wacce yasaka sabida cutar da Widad datasoyi Allah ya tona mata asiri, yarshi daya aduniyan nan tal Widad, Allah baitaba bashi haihuwaba sai akanta, itama din harya cire rai dan yaga yay mata uku duk shiru yace halan daga shine sai kwatsam ga mahaifiyar Widad da ciki, yakusan karaman hausa a lokacin daya gane tanada ciki saisa da aka haifamai mace saiya radamata suna WIDAD ma’ana love, yana bala’in son yarinyar so mai zafi, gashi kana ganin yarinyar kaganshi kaman yay kaki, ko office zashi da yarshi da mahaifiyar ta yake zuwa sabida yadinga sata a ido kodayaushe, indan tafiyan fitanshi daga gari ce ta taso saidai yadauki mahaifiyar ta da ita dan bazai iya nisa da itaba saisa itama yarinyar ta taso tana bala’in son mahaifinta, tanada shekaru 18 mahaifiyar ta tarasu daga ciwon kwana daya tal, Widad takusan hauka take mahaifin nata yafita da ita da kyar aka samu taji sauki aka dawo da ita gida tadinga kuka daga karshe taroki mahaifinta tunda tagama sakandire yakaita wata kasar tai University intana gida tunawa da mahaifiyar ta take sosai, da kyar da kyar saima dayaga ta kwanta tana ciwo sanan ya yarda yakaita Egypt yamata komi yasaman mata admission in datake karanta mass communication.

Wani hadadden babban daki suka shiga itada Amah dake upstairs, dakin wakacece ne babba dayasha carpet tako ina mai bala’in kyau dan duk wanda yasan morroco yasansu da sana’ar kera carpet su sayar, gadaje biyune hadaddun gaske masu rumfa da aka zagaye da labulaye farare masu kyau acikin dakin babba da karamin gado, tun bayan mahaifiyarta ta rasu tadawo dakin kakanta da zama kakanta ne kadai takejin dadin zama da ita dan tana sonta kaman ne, jakanta tacire ta ijiye akasa sanan ta taka zuwa gaban wardrobe din dakin dan neman kayan dazata saka, Amah kuma ta ijiye sandarta agefe ta zauna ahankali kan gadonta tanabin bayan Widad din da kallo, shekara daya kacal dabata ganta ba amman saitaga ta chanza mata a ido sosai, dan murmushi tasaki tana tunanin Widad da aka haifa jiyane ta girma haka, batare da Widad tajuyo ta kalleta ba cikin harshen larabci tace “Amahh why are you smiling? Tunanin me kike?” tai maganan tareda juyowa hannunta rikeda wata jan kaftan dayasha ado kaman irin dogayen rigunan India, hararan ta Amah tayi tace “wuce kije kiyi wanka, favourite dinki nasa aka dafa tagine, rice da herbs saikuma flat bread” washe baki tayi ta yarda rigan hannunta kan gado da gudu tai bayi, kyalkyacewa da dariya Amah tayi tadauki sandarta tawuce tafita dan tabbatar da yan aikin sun jera komi a tsakiyan falon barinma wanda tasan yar jikallenta tafiso. Dan aikin datagani awurin yana ijiye plate dake dauke da dry fruits tacema “ina flat breads din danasa ku gasama Widad?” cikeda girmamawa yace “yanzun nan jibril zai karasa baking dinsu yafito dasu” zata sake magana taga Aby na saukowa daga sama shima da hannu tama dan aikin alamu daya wuce yabata wuri, da sauri yawuce bayan ya gaida Aby, saukowa daga benen Aby yayi yazo gabanta mahaifiyar tashi yace “Assalamu Alaykum Amah” “waallaikumus salam” ta amsashi tana zama, ahankali shima ya zauna gefenta yadau inibi daya yajefa abaki yanadan bin wakan da akeyi awaje cikin kwanciyan hankali, ganin yanda yake farin ciki yasa mahaifiyar shi takira sunan shi. “Othman” anatse yajuyo ya kalleta tareda ijiye inibin daya so jefawa cikin baki kan faranti, dan gyara zama Amah tayi da kyau kaman yanda shima ya natsu yana jiran yaji mezatace mai, cikin muryanta na tsofaffi tace “wace shawara ka yanke akan maganan damukai dakai jiya?” fuzar da iska yayi fuskarshi ya dan nuna damuwa yace “I don’t know Amah, all I know for sure is bazata koma wanan makarantan babu aure akanta ba, ai nai mata kokari dana iya nabar y’ata wacce ita kadai ce Allah yabani aduniyan nan taje chan wani kasa tana karatu ba, banda hakama Amah bakiga yanda alamomin girma suka bayyana ajikinta sosai ba?” gyadamai kai Amah tayi cikeda gamsuwa da bayaninshi tace “nagani” yace “burin kowani mahaifin ya killace yarshi intana wanan matakin ya aurar da ita, na kashe all meetings danake dashi throughout this week, hutun sati biyu kacal gareta, nariga na sanar da iyayen Ahmad zasuzo anjima da daddare we are having engagement ceremony tonight, nikah zai biyo baya nanda sati in 7days time dudda a al’adance yakamata bayan engagement ceremony da shekara ne ake biki but I can’t wait that long” ya karashe maganan ahankali saikuma yasaki dan murmushi mai kama data bakin ciki ya kalli Amah yace “Amah anya zan iya rayuwa kuwa in bana ganin y’ata?” yasakeyin murmushi hawaye na taruwaa idanunshi yace “Amah bantaba fadamiki wanan ba sabida nasan fada zakimin kice nabar yarinya tai concentrating a karatu kaza kaza kaza, kinkosan cewa ban taba kaiwa sati daya cur batare danaje Egypt ba dukko nisan shi?” ware ido Amah tayi cikeda mugun mamakin shi dan tasan dan danta business man ne yana yawan tafiye tafiye but bata taba sanin haka yake zuwa wajen Widad a makarantan ba frequently ba, one thing she knows for sure shine she always wondered ayanda Aby keson Widad kaman zaiyi hauka ya iya hakura hartai shekara a makaranta bai gantaba, maganan shi ne ya yanke mata dogon tunanin dataje yace “kinsan yanzu intai aure bazan iya dinga zuwa haka ina ganota bako” ya share hawayen dayadan zubomai da sauri yay murmushi yace “Amah banson ko kadan Widad ta wahala aduniyan nan, saisa nake aiki nake neman kudi sabida ita, dazaran na aurar da ita I believe lokacin tadawo cikakiyar mace, zanyi handing all over my properties, companies komi da komi nawa, all my assets to her ni zanyi retire na huta, shi will be managing everything, komi da komi dana mallaka nata ne Amah dan banda wani magaji aduniyan nan sai ita, I make sure nabata komi ranan da aka daura aurenta agaban mijinta da kowa, innai haka hankalina zai kwanta dan nasan tanada komi bazata taba wahala ba, yakika gani Amah?” kumatun shi Amah taja cikeda murmushi tace “brilliant thought, kasan I’m always proud of you Othman kai d’a ne nagari mai adalci, ina mai goyamaka baya dari bisa dari akan wanan hukuncin daka yanke, mu munriga munyi rayuwanmu aduniyan nan, munci duniyan mu da tsinke, mutuwa yauko gobe takan iya daukanmu, inhar bamu bama Widad da yanzu tafara girma komi damuka mallaka ba maimuka yi?” dan murmushi tayi tace “nima zinaruka na tunna lokacin aurena da mahaifinka, gabaki daya daman ita nakema ijiyansu ranan aurenta da izinin Allah zan bata, Allah yamaka albarka Othman Allah kuma yasanya ma auren albarka, na yarda da Ahmad sosai, nakuma san yanda yake sonta tun tana yar yarinya” dan dariya Aby yayi yace “kinsan mahaifinshi yacemin daya fadamai maganan engagement din danayi yakusan suma kinji fa yarinta” “ba yarinta bane tsabagen so ne da kauna ta gaskiya” suka kwashe da dariya irin ta manyan nan kafin tai hugging nashi su a dariya atare gwanin ban sha’awa.
[11/1, 11:44 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button