DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

???? TWO DIFFERENT WORLD????

       ✍️ M SHAKUR








         4️⃣3️⃣ & 4️⃣4️⃣

Shiru yayi yana kallon Mom kaman bazaiyi magana ba sanan yadan nisa yace “Mom I don’t know” ahankali Mom tace “kaman ya you don’t know who she is” shiru yasake yi kaman wanda ke tunani saikuma yace “Mom wlh da gaske I don’t know who she is but Mom I love beyond much and I wanna marry her” kyar Mom kebinshi da ido ko kyaftawa batayi ganin maganar nashi da girma take, ganin yanda Mom ta tsareshi da ido yasa yace “an kawota gidan marayu ne about 10months ago, all this while tana admission bed ne sai kwanan nan tasami lafiya, before bata iya wani tafiyan kirki idanunta sun sami matsala and many more but yanzu tasami lafiya, kawai memory lost dinne shima due to cases din danaketa shiga kwanan nanne yasa ban daurata kan treatment dinba da tuni nafara” shiru Mom tayi tana sauraronshi tace “Waleed kasan mekake cewa kuwa? Yarinyar dabakasan waye itaba, bakasan daga ina takeba, yarinyar da bamata hayyacinta ne zakace kanaso? Kasan mekake fadi kuwa”? Shiru yayi shima yana kallon Mom din kafin ahankali yace “Mom you know me morethan Ammi, u were the one data rainen, you know me idan inason abu, Mom I love this girl and all I could think of right is moment is spending the rest of my life with her all other things are secondary, we can all handle it” yay dan shiru saikuma yabata labarin komi har zuwa abinda yafaru jiya da Arham yadauke ta yace “gwara na aureta na kilkace ta, na kula da ita duk tana karkashina, cus Mom inkinyi tunanin abin what if memory ta bai dawo ba? Haka zata cigaba da rayuwa batada kowa? Or babu wanda zai aureta harsai randa memory ta yadawo tafadi mana waye family ta, Mom I seriously love this girl saisa nafara tunkaran ki da maganan first inaso na aureta banma so idan kunsa rana yadauki tsawon month please kinji Mom” shiru Mom tayi danta itane batada matsala wlh, tasan ba’a bari ya auri ra’ayinshi da farko ba yanzu kuma yakawo she will support after all shi namijin mace hudu ne but Ammi zata yarda? Bayan ta aurama dan nata yar kawanta abundai da kamar wuya, maganan Waleed ne yadawo da ita daga dogon tunanin dataje. “Mom” dagokai ta kalleshi, murya chan kasa yana kama hannunta cikeda lallashi danta yarda yace “Mom please inaso yanzu ta zauna anan tareda ke cause I know Arham zai cigaba da neman ta, please Mom let her stay here har zuwa nan da nai magana da Ammi hopefully yau zan mata maganan kinji Mom” yay maganan ahankali akuma ashagwabe, ahankali Mom tace “naji zan rike maka ita, but Waleed dududu aurenka ko shekara daya chur ba acika da yiba karewanta ma yaune ake sunan danka shine zaka tado da maganan aure you are just 28 Waleed harzakai mata biyu karfa kazama namiji mai aure aure” murmushi yayi yace “Mom ni ko mace daya kacal ce zan iya rayuwana da ita inhar ina sonta sanan tanamin abin……” kasa karasa maganan yayi ganin Widad da Asma’u na saukowa daga stairs, Widad na sanye da wata atampa riga da skirt ash color da dark brown daya mata wani mahaukacin kyau, kayan sunbi jikinta tsaf kaman an aunata kafin adinga sun mugun fito mata da shape, Asma’u tamata daurin kallabi mai kyau daya bayyanar da gashin goshinta da gashin farko farkon kanta dasuka kwanta suna shinning, wani irin faduwa gabanshi yayi yaune rana da farko tun bayan randa aka kawota ajike dayake ganinta da kaya samadana asibiti, tai kyau ansaka mata dan kunne kaman wacce zatace gasan kyau, ko kallon Waleed dinma batayi ba sabida labarin da Moxi kebata da turenci datake ganewa sosai this is the first time datake fira dawata haka other than Waleed, ganin gabaki dayan hankali shi yayi akansu yasa Mom takara tabbatar wa cewan Waleed nason yarinyar kam sosai, ahankali tace “tashi muje kayi breakfast saika tafi wajen Ammi ka” tashi yayi Mom ma ta tashi duk sukai dinning, zama yayi kusada Mom yana satan kallon Widad din dahar lokacin hankalinta kekan Asma’u, gake deban mata fruit a bowl zata hada mata fruit juice mai madara.

Bai wani iyacin abincin ba yature yatashi daga dinning, jiyayi duk ranshi yabaci ganin yanda gabaki daya hankalinta kekan Asma’u, tana wani kallon Asma’u kaman tasami TV, cikeda daga murya yace “am going Mom” da gangan yay maganan kota juyo, jin maganan shi yace he’s going yasa da sauri tajuyo ta kalleshi ganin yamike yasa da sauri itama tamike tana kallonshi, daure fuska yayi yace “u are staying with your new friend” girgixa mai kai tayi da sauri tana shirin kuka ta zagayo ta inda yake da sauri tazo wurin shi zata rikeshi yadan zare mata ido alamun karta tabashi hakan yasa taki yakalli Mom yace “Mom bye” gyadamai kai Mom tayi tace “sai andawo” sanan yajuya ya kalleta yace “stay here don’t go anywhere” yay maganan yay waje, duk abinta bata iya ketare abinda yace fashewa tayi da kuka takoma ta zauna akan dinning Mom dai murmushi tayi tacigaba dacin abincin ta Asma’u kuma tacigaba da lallashinta.

Gida yakai yay parking motarshi, fitowa yayi sanin inya shiga bangaren Ammi bazai fitoda wuriba yasa yawuce direct flat dinshi zama yayi akan bed dinshi yadauki wayanshi yana kallo gabanshi nafaduwa, yasan Ammi zata iya bashi matsala a zancen auren nan, shikuma baison haka but ya tabbatar da inhar yafadima Uncle bazai taba jin kunyaba, ko mata dari yakeso Uncle is ready ya auro mishi, ciro number uncle yayi daga contact dinshi sanan yay dialing number, yana ringing aka kashe, murmushi yayi ko kadan Uncle bai daukan wayanshi wai International call ne za’a cinyema Waleed kudi saidai ya katse ya kirashi, yana cikin tunanin wayan ya shiga ruri, murmushi yayi yadau wayan yakai kunnenshi, cikeda wani irin shegen shagwaba yace “Uncle”
Cikin wata irin murna dake nuna tsantsan kewa Uncle yace “My not so little son, how are you Boy”?
Ahankali Waleed yace “Uncle I need something”
Gyara zama Uncle yayi ya kalli mutumin baturen dake cikin office dinshi yace “excuse me please my son need me” tashi baturen yayi cikeda girmamawa yafita daga office din yarufomai kofa, hakan yasa Uncle yace “yes Son, talk to me”
Dan jim Waleed yayi yana tunanin ta yanda zaifara gabatar ma da Uncle maganan daga farko sanan yace “Uncle there’s this girl in my orphanage…….” yabashi labari tatas sanan yakarake da “I really love her Uncle, but am afraid nai approaching Ammi, zata iya cewa bazan auri yarinyar da bamusan daga ina takeba”
Cikin muryan Uncle data riga takoma na turawa yace “no, no, no Son, Ammi bazata iya cewa hakaba, love doesn’t have anything to do with who you are or who are your parents, love has to do with two different souls da heart dinsu are connected, koma daga family mayu take ko family aljanu inhar kana sonta go for her, kai d’ana ne, my blood runs through your vein, family ba babu wanda bazasu iya aure aduniyan nan ba kodaga ina yarinyar take, kanadai sonta ko”?
Murya chan kasa akuma kunyace yace “eh”
Murmushi Uncle yayi jin kunya a voice dinshi yace “alright, yaushe kakeson wedding din should take place”
Murya chan kasa kaman wani na kirki yace “banma so yakai up to 1month”
Murmushi Uncle yayi yace “shikenan Waleed dina, once nabar office zan kira mahaifiyarka, take care of yourself okay, if you need anything just call me, koma menene, I’ve sent you gift din jikana Arham, ehen that brings me there, ya friend dinka Arham”?
Faduwa gaban Waleed yayi ko kadan baiso yafadi ma Uncle abinda yafaru tsakanin su hakan yasa yace “he is fine Uncle”
Gyadakai Uncle yayi yace “how do you want the wedding big wedding kakeso ko simple one”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button