DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

❤❤❤
[11/1, 11:47 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

   ???????? _*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_???? ???? 





        ✍️ M SHAKUR 





              2️⃣6️⃣ & 2️⃣7️⃣

FREE PAGE
Komawa falo sukayi duk suka zauna Anty Hussai da Yakolo sukahau hira banda Anty Hassu datai shiru tana tunani ko kadan bata yarda da Ilham ba, but still batason tama Ilham tunanin datake yi, duka duka yaushe Ilham ta girma hartai wayon da da aurenta zata dingabin wasu mazan, ta tambayi kanta saikuma tai shiru, duka duka yaushe akai auren Ilham dake mugun son Waleed kaman zatai haukane zatabi wani namijin? Ajiyan zuciya ta sauke tana kokarin kawar da tunanin daga zuciyanta dan bamata fatan abinda take tunani shike faruwa.

Wuraren 4 na yamma ya shigo gidan marayun yay parking motarshi yana tattaro wasu uban takardu daya ijiyesu a kujeran gefen direba ya kwasa dayawa yarike sanan yabude motan yafito daidai Waleed yakaraso wajen dan daga masallaci yake, wani iri Arham yaji dayaga Waleed kaman zai maida takardun cikin motarshi saikuma yarike hannunshi, karasawa wurin shi Waleed yayi hannunshi zube cikin aljihu yace “kadawo blood” gyadamai kai Arham yayi yace “yes nadawo blood, Mama ta iya saka mutum aiki, iyaye sai ahankali” zaro hannu Waleed yayi daga aljihu yamika Arham din yana kallon uban papers din hannunshi yace “what are those blood mugani”

Da sauri Arham ya kalli papers din gabanshi nafaduwa Saikuma yakara linkesu yana lankwdhesu da kyau gudun karyaga mainene su yace “they’re not mine, nawani dan anguwan mu” saikuma yabude mota da sauri ya zubasu ciki sanan yamaida kofar motar yarufe yajuyo ya kalli Waleed dahar lokacin kallonshi yake, sanan yace “muje daman akwai maganan danake so namaka” juyawa Waleed yayi yace “am going to the clinic now to check my patient nafito mayi maganan” ganin kaman ran Waleed din yabaci yasa yace “muje to naraka ka clinic din” yabi bayan Waleed din, clinic din suka shiga da basuda much patient that are on admission saidai out patient wayanda kawai zasuzo suyi complain kazakaza na damunsu adubasu abasu magani sutafi, dakin da Widad take direct Waleed yayi Arham biyeda shi suka ya shiga, tana kwance akan gadon an lullubeta da bargo fuskarta ne kawai awaje da gashinta da akai parking tana bacci, idanunta har wani nama nama sukayi tsabagen bacci, karasawa gaban gadon yayi Arham biyeda shi, Arham yace “for the past 3month now kullum yarinyar nan nazo dakin nan bacci take saikace wacce take a coma” stethoscope yadauka yana makalawa a kunne yace “she’s not in a coma, babu ranan duniyan dabata tashi, yawanci sau daya take tashi, amata brush abata abinci suma duk tanaci tana gyangyadi tasha magungunan ta, I was the one that increase her dose, duk wanda yakeda damage a brain need absolute rest, yesterday nakara mata MRI da CT scan I was happy with the result, fluid din yaragu sosai wanda yarage baifi an atom size ba, yanzu shi nabashi 4days, dazaran kwanakin sun cika zan sake running test din inhar babu saina godema Allah, tagama da magungunan zan mata transfer zatabar hospital takoma hostel, dudda haka I will be monitoring her ina bata magungunan that help with the memory lost” yay maganan yana zare, stethoscope din daya daura kan kirjinta duk Arham na kallonshi, dan tabe baki yayi yace “tamayi kokari kusan watan ta 9 akan gadon asibiti, sai yanzu ma nake dana sani daban karanci medicine ba nima nadawo likita kaman kai nawani kama ina karanta engineering, kumako kasan inda na karanta medicine dafa nafika kwarewa” yay maganan ahankali hankalin shi nakan wayanshi dayake dannawa yana kokarin turawa Ilham message kartace baikara nemanta ba, dan juyowa Waleed yayi ya kallai jin maganan yamai wani iri aka, ganin wayama Arham din ke dannawa yasa yagyara mata bargon yace “let’s go” yay gaba shikuma Arham yamaida wayan aljihunshi da sauri yabishi suka fita, office din Waleed suka shiga, Arham yaja kujera ya zauna Waleed ma yazauna yana gyara zaman takardun kan table dinshi sanan yace “yes ina jinka kace akwai maganan da kakeso kamin blood”

Ahankali Arham yasake jawo kujeranshi gaban table din sosai yasauke ijiyan zuciya ahankali sanan yace “I need a favour blood, kaima kasan you’ve been my ride, my backbone my everything, u are my only friend I come to you in every situation” yadanyi shiru sanan yace “I need money blood, I need money sosai” ahankali Waleed yace “for what?” ahankali yace “kaga na farko, Maman su yarinyar nan da Mama tace na aura, kanwar Mama gidansu ya rushe, ruwa yamusu gyara, sanan inaso nasaya ma mijinta shanu da gona su dinga sana’a, sanan inaso nakaisu Umara harda Mama and many other thing, please kabani 10m blood” yakarshe maganan ahankali shiru Waleed yayi yana kallonshi, arayuwanshi baida mutum daya keso kaman Arham, saisa kome zaimai baya taba sa ido koyaga mezaiyi da kudin kowani abu baruwan shi, in yabashi kudi yabashi ne so badamuwarshi bane abinda zaiyi da itaba, baitaba cire kudinshi yasai kaya ma shi kadaiba bazaima iyabane inhar shi zai cire kudi yasai sitira to nashi dana Arham zaisaya, duk wani abu dazaisa ajikinshi inhar Arham baidashi to iyayen shi ne ko uncle dinshi suka siyamai, yana bama Arham kudi sosai excluding kudin albashin shi, lokacin bikinshi yabashi dollars da Ammi tabashi baimasan yawansu ba, ko last 2weeks saida yamai kyautan 3M cikin kudaden sa gwamnati takawo ma gidan marayu tallafi dan he don’t really needs government money kafin su kawo yay amfani da kudinshi yayi abinda ya kamata, abincin Mama da supplement dinta yana kanshi kowani wata saiya saya yakaimata yabata kudin kashewa amatsayinta na maman abokinshi, yabada kudin man motan ta dakudin man generator na gida, banda inverter dayasa aka saka agida saisa 247 duk lokacin dazaka gidan Mama nada wuta, Arham baya komi danta ko’ina ya tare mai wata dawainiyar shi to’ina yake kai kudin shi? Abin yadade yana damunshi bawai dan sa ido kowani abuba just amatsayin shi na abokinshi na gaskiya zaiso yasan inda yake kai kudaden shi karyazo yana wulakanta kudinshi koyana saka kudinshi awani abu na haram ne, yariga yasaimai dankareren gida a anguwan da gidanshi yake da Ilham keciki, incase inya tashi aure yasa matanshi ciki ballema yace gini yake da kudin ina Arham yake kai kudi, kowani bad abu yake da kudi? No hakkinshi ne amatsayin shi na abokinshi na gaskiya ya tambayeshi yaji. “X-man kayi shiru kobaza kabani bane?” Arham yatambaye shi, dan nisawa Waleed yayi yace “no bahaka bane, actually I’ve been wanting to ask you this question also, I think today is the right day, Arham” Waleed yakirashi anatse, zubamai idanu Arham yayi irin ina jinka dinan batare daya amsaba, ahankali Waleed yace “Arham banso kamin karya, tell me please mekake yi da kudi”? Dawani irin sauri har yana neman taran numfashin shi yace “kaman ya menake yi da kudi” dan jim Waleed yayi yana kallonshi saikuma yace “okay lemme do it like this kafahimce ni, blood duk wata dawainiya dazata sa ka kashe kudinka na dauke makashi yet kullum bakada kudi, me kakeyi da kudi”? Wani irin zabura Arham yayi yamike tsaye daga kan kujeran dayake kai yana kallon Waleed din yace “mekake nufi da duk wata dawainiyar dazata sa na kashe kudi ka daukemin ita yet kullum banida kudi, Waleed gori kakemin sabida kana siyama mahaifiyata yar buhun shinkafa duk wata kana kaimata”? Waleed was still seated akan kujeran shi ya girgiza kai yace “uhm’uhn that’s not wat I meant Arham, calm down and sit let’s talk please, banga abin zafin nanb……” wani irin buga table dinshi Arham yayi da hannu yay kara yace “don’t fucking tell me to calm down, on what account zaka dinga tambayana menake da kudi sabida ka daukemin dawainiyar kaina kana saima mamana yar buhun shinkafa da wake, Waleed ni kakema gori sabida kaga Allah bai horemana kaman kuba eh? Ni kake ma gori Waleed, am talking to you kamin shiru are you stupid”? Arham yadakama Waleed tsawa dayasa Waleed yaji ranshi yabaci dan ba’amai tsawa koda yana yaro baima sababa, tashi kawai yayi dan baiso yabiye mai suyi fada yay wajen hanger dayake makala suit dinshi yaja yadauka zai saka, wani irin shan gabanshi Arham yayi da jajayen idanunshi ya kalli Waleed yanuna kanshi da hannu yace “ni kakema gori Waleed, sanan inamaka magana kamin banza ni kake ma gori”? Kasa saka jacket dinma Waleed yayi sabida ihun Arham dayake mai a kunne kaman zai fasamai dodon kunne yamaida jacket din yarike a hannu sanan ya kalli Arham yace “since you are too dumb to understand a simple question dana tambayeka then take it anyhow you wish to take it” yana gama maganan yadau wayanshi daga kan table zai juya yay kofan fita Arham yasha gabanshi yace “ni kakema gori”? cikeda mugun bacin rai da kulewa da maganar Waleed yace “nayi, kai duk abinda kaga dama” kaman amafarki Arham bai wata wata ba ya daurama Waleed wata lafiyayyen mari ata gefen ido dan marin har yadan taba idanunshi na side din dama jikake kau! Idan Waleed yace he was expecting a slap from Arham he is lying, jin saukan mari yayi kawai daga sama baisan lokacin daya saki wayanshi da jacket din dake hannunshi akasa ba suka fadi, wani irin fincikanshi Arham yayi ya bugada bango bayanshi yabada bam, Arham ya shakemai wuya, cikin kunfan baki da mugun tsana yace “sabida rashi da talauci yasa am working under you, yaro dakai u are just 28 inada 35yrs na girmeka da shekaru shidda zaka tsaya kana gayamin magana yanda kaso, daman hausawa sunce yaro da kudi babba yake dawowa, this can not work with me, yau saina koyama hankali, I will teach you a lesson, fight me back now, fight me back” har alokacin Waleed was shocked yama kasa yarda Arham dinshi ke fada dashi haka, ya shakeshi yana neman kashe shi idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi sun fito, fuakanshi tai jajir abunku da farin mutum, ahankali ya iya yataba hannun Arham dake wuyanshi muryanshi bata fita sosai yace “u…..are….hurt…..ing me blood…..am….am…..my….my…..breath” yay maganan about to die amman Arham baida alamun sakinshi saima kara shakeshi dayayi yace “I said fight me, fight me mana, I want you to fight me dan Allah inka isa, kai fada dani kaga yanda zan baka kashi, na farfashe maka wanan bakin dakake min gori dashi kan kasayama Mahaifiyata wanan shegen tsukukun gidan kaman gidan kiwon kyankyasai, da shegiyar akurkan motar nan, inda don Allah kakeyi da tikeken gida zaka saya mata irin naku mansion, mota mai numfashi bata manoma ba, yau saina nuna maka kudin ka bazai iya taimakonka a hannunna ba, I will deal with you yau Waleed, wlh saikai fada dani zan kyaleka na rantse maka” daidai lokacin akai knocking kofar office dinshi, sake shakeshi yayi to the extend this time idanunshi sun soma juyawa gashi yakimai komi dan he can’t raise his hand on his friend or hurt him in anyway ba, da kyar hannunshi ya iya komawa baya dashi yatataba flower verse din dake kan table dinshi ya kabar dashi kasa yay kara akasa sabida wanda ke waje ke knocking kofarshi yaji ya shigo, jin karan flower verse yasa Mama Iyami tace “subhallahi karan menene wanan” ta murza handle din kofan kawai ta shigo ciki, ganin yanda Arham ya shake Waleed yasa da sauri tai kansu yace “Mr Arham innalillahi wa innailaihi raji’un, wats happening here? Meke faruwa haka? Kaida abokin ka, let him go, sakkashi kaga” ta shiga kokarin fincike hannun Arham daga wuyan Waleed, cikin fushi Arham yace “wlh bazan sakeshi ba saiyay fada dani, sainaga uban karfin dayike dashi dayake juyani yanda yakeso sabida yaga yanada kudi dan ubanshi” ganin yanda Arham ya harzuka Waleed na neman mutuwa a hannunshi yasa tafita daga office din da gudu ta kurma uban ihu. “jama’a kuzo kutaima keni, Dr Waleed Warbai and Mr Arham are fighting, please helppppp” ihunta gabaki daya yadauki gidan marayun, da gudu wasu staff din Waleed da yaran gidan marayun damasu shara, gardeners da waye da waye aka shigo office dinshi da gudu, Nura dawasu maza hudune suka fizge Arham, suka jashi baya Waleed kuma yay baya zai zube wasu ma’aikatan suka tareshi, da gudu Iyami tafashe da kuka tace “innalillahi is sir alive jama’a?” wani ma’aikaci ne mai suna Auwal yace “he’s alive but sai ankaishi asibiti” da sauri suka fita dashi daga office din, Mama Iyami tajuya ta kalli Arham dake huci yana tsaye ya fizge kanshi daga rikon da akamai tace “Mr Arham meya hadaka fada da abokin ka eh, dan uwanka fa, blood naji kuna kiran junanku, Mr Arham meya hadaku dashi” cikin wani irin fushi Arham yace “kije ki tambaye shi mana, dayake shi ogan kine bazaki iyaba shine yabaki aiki, yana baki na abinci bazaki iya tambayanshi ba, amman dayake ni kin rainani dole kitasani agaba kina tambaya, matsiyatan mutane, masuyin boyi boyi dan abasu kudi, fatararru kawai” yay maganan fuuu yafita daga office din ma’aikatan kowa yabishi da kallo ana mamakin tome yahada su tsawon shekaru nawa ba’a tabajin kansu ba saiyau, motarshi ya shige yaja motar yawuce yabar orphanage din.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button