DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

DUNIYA BIYU MABANBANTA HAUSA NOVEL

Flat din Waleed tayi bude kofa tayi ta shiga da sauri Waleed dake zaune yana kokarin kunna system dinshi yadago kanshi ganin Ammi ne yasa yamike tsaye ahankali, maida kofar Ammi tayi tarufe cikeda bala’in masifa tace “okay Waleed am now the villain in the story ko, dani kake fushi eh? Mena maka?” cikin kulewa irin exactly child and mother’s fight dinan Waleed yace “ni nace kinmin wani abune? Akwai abinda kikace nayi dabanyi ba? U arrange marriage for me I didn’t say a thing, kince I shouldn’t go to office and am right here at home Ammi what else?” yay maganan idanunshi sunyi jajir kana ganinshi kasan yacika fam, yanda taga yanayinshi yasa hankalinta yawani irin mugun tashi, daura hannayenta akirji Ammi tayi cikin mugun mamaki tace “Waleed, Son!” juyawa yayi da sauri muryanshi narawa yace “ni bakimin komiba Ammi, I need a nap” yana maganan yay hanyar dazai sadashi da bedroom dinshi da sauri Ammi tabishi kafin yasa hannu yabude kofan ta fizgoshi tace “Waleed am talking to you” janyoshi tayi with so much love tai cupping face dinshi tana kallon fuskarshi duk yanda takaiga son su hada ido yaki bata daman hakan, cikin wata irin raunanniyan murya hankalinta inyay dubu yatashi ganin da gaske yaronta fushi yake da ita tace “Waleed dani kake fushi ni mahaifiyarka eh?” cikin muryanshi datahau rawa sosai kaman wanda ke shirin fashewa da kuka yace “Ammi nifa bance miki komiba I did exactly as you said please lea…….leav…” yakasa magana sai hawaye masu dumi, ji Ammi tayi kaman ta kurma ihu da sauri ta rungume shi tace “am sorry, am so sorry Waleed u are crying because me, ni mahaifiyar ka ke saka kuka, no no no, banda burin dayawuce insaka farin ciki aduniyan nan, I never knew my actions hurt this deep, Waleed, my Waleed kallen” tai maganan tana dago fuskarshi daga jikinta, fuskarshi harja tayi sabida hawaye, tsabagen rudewa dan kwalin English atampa dake jikinta hakan yasa gashinta dakenan da furfura anmata kitso shiku ya bayyana tadaura akan fuskarshi ta shiga sharemai hawayen tace “is okay, stop crying, stop crying Son, ya isa” bude bedroom dinshi tayi ta shiga tana rike da shi kan sitter gaban gadon ta zauna ta zaunar dashi tareda rike hannunshi kaman zatai kuka tace “Waleed I never meant to hurt you, kome nayi I did it for you dudda nasan my approach might seems wrong but that is me u know, Waleed kalli kaina” takamo jelar gashin kanta ta nunamai tace “Waleed furfura, am not getting younger anymore, tsufa nike kullum the same way yanda mahaifinka yarasu ya barmu haka nima zan rasu watarana” tadanyi shiru dan batason tai breaking down sanan tadanyi murmushi tai cupping face din Waleed din tace “Son you know about my hypersensitive situation, kaike monitoring minishi kana bani magani, masu irin condition dina can die any moment, na zauna nai tunani na kalleka nakuma karance ka Waleed matama basa gabanka sai aikin gidan marayu, and inaso kai aure inaso naga y’ayan ka my grandchildren kafin nima nabar duniyan nan, batun yau ko jiya nake nema maka mataba, nafara nemama matan aure tun kana 25yrs amman banga wacce tamin ba sai akan khadija, Khadija tayi sauka, tagama karatun ta lawyer ce mai zaman kanta, gata yar gidan mutunci, kuma ranan data fara ganinka na fahimci tana sonka so bakadan ba, inhar ban zabamaka irin matar nan ba wa zan baka maka? But I am sorry, na dauka na isa dakai but I guess I am w……” hannunshi yasa yarufe mata baki tareda girgiza mata kai yace “Ammi kin isa dani, I just didn’t wanna get married now ne, Ammi am too young, just 28 fa, and ita yarinyar she is 26 da 2yrs fa na girmeta” dan murmushi Ammi tayi ganin ya sauko ta rungumoshi ta hanyar daura kanshi kan shoulder dinta tace “age is just a number Waleed, nasan tsoro kake kan baka wani girmeta sosai ba bazata girmamaka ba, and you being 28 itakuma 26 baya nufin hakan I know yarinyar dana aura maka tanada dattako she will respect you kaman her king son, are we good now kahakura kadena fushin?” gyadamata kai yayi ahankali yace “yes” dago kanshi tayi ta manna mai kiss agoshi tace “thank you, Allah yamaka albarka, yanda ka rufamin asiri baka kunyatani ba kaima Allah bazai taba kunya taka ba duniya walahira, Allah yakareka daga makiyanka, akwai kaya na mussamman dana maka ordersu daga Morocco ????????”

“Sherwani masu kyau zakayi kaman wani dan India, dama yarona badai kyau ba ballema yasaka sherwani nan, dan murmushi kawai yayi, ahankali ta shafa kanshi tace “nagode kaji, ka rike amana kaji, ka kulada matarka, Uncle dinka ya shiga villa wai yanada meeting da president saisa baka ganshiba kafin anjima by 8 yatafi Airport dan jirgin su 10 zai tashi” gyadamata kai yayi kafin yatashi ahankali kan jikinta da sauri tace “ina zaka?” ahankali yace “waya zan dauko nakira blood” shiru tayi tareda binshi da kallo kaman yautafara ganinshi, wayan yadauko yadawo yay fillo da kafafunta ya kunna wayarshi yay dialing number Arham wayan yaji akashe hakan yasa ya ijiye wayan Ammi dake binshi da kallo tace “ya akayi? Baka sameshi bane?” dan tabe baki yayi yace “wayanshi akashe” gyadakai Ammi tayi tace “maybe yagaji ne ya kashe wayan dan ya kwanta yay bacci, yasha hidiman bikinka, tunda bikin ka yazo bawan Allah nan bai huta ba” murmushi yayi daya wani irin karama fuskarshi kyau ashagwabe yace “Ammi kinsan menene?” da sauri Ammi ta chusa hannunta agashin kanshi tahau shafawa tace “menene Waleed dina?” dagokai yayi ya kalleta yace “wlh am missing the orphanage so much, yau kawai dabanje be jinake kaman nai shekara I can’t stop thinking about those helpless children I know kowa na kewana barinma the little ones” murmushi Ammi tayi sosai ta cigaba da sosamai kai tace “that is why am a proud mother of this hard-working young man, My doctor, I know you are missing dinsu saisa nima I got a surprise 4 you” da sauri yatashi ya zauna ya kalleta yace “suprise Ammi namene?” dan dariya tayi takamoshi ya kwanta tace “to sarkin azarbabi koma ka kwanta” gyara kanshi yayi akan cinyanta yana murmushi itakuma ta maida hannunta cikin gashinshi ta cigaba da massaging tace “kwanaki kafadi mini on the 8th ne zakuje excursion da yaran gidan marayunka a Yankari ko” gyadamata kai yayi tace “so I checked my date sai nagama ma next week ne 8th, so I called the Yankari game resort namuku booking gabaki dayanshi from on the 8th to 16th, kadauki matarka duka kutafi and have fun, if seeing those children da zama dasu makes u happy then am ready to give it to you all, kuje kaida matarka da Arham da yaran all Allah ya tsaremin ku but zakadau bodyguard dinku, kuna dawowa kuma u can resume office” tunda take maganan yake kallonta ta mugun mugun faranta mai rai zai iya cewa acikin plenty gift din databashi da bakin nan nashi this is just the best gift, hannunta yama peck yace “thank you Ammi na, I love you so so sooo much” murmushi tayi ta dagashi tace “ni barni naje nai breakfast kaiba abinda ka iya dafawa balle na zauna adakinka kaje kitchen kamin girki” dariya yayi yace “Ammi Allah ki zauna namiki sakkwara da miyan kubewa” hancinshi taja tana dariya tace “yakuri son ban shirya cin mara dadi yau ba” da sauri yace “Allah Ammi” fashewa tayi da Dariya tajuya tafita kaman ba itaba inkaga dariyan Ammi da danta take.
[11/1, 11:46 PM] Re@l???? K@usy ????: ???? TWO DIFFERENT WORLD ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Leave a Reply

Back to top button