BUDURWAR MIJINA COMPLETE NOVEL

“Mahfuz mai yasa ka dawo dani gidanan bayan kasan bazaka iya rayuwa ba Hadeeza ba? yau Zan kwana biyu da dawowa amma mahfuz har ka koma wajenta idan har kasan kana santa haka Mai yasa ka dage min na dawo”?
“Ke fa dama idan Kika tashi haukarki bakya lissafi da tunani ni nace miki wajen Hadeeza naje”?
“Ko baka fadamin ba mahfuz ga kamshin turaren ta nan a jikinka ga Jan baki nan a kwalar rigarka dan Allah bakaji kunya ba Mahfuz na tsaneka ka sakeni kaje ka aurota idan Kuma dawo da ita gidanan zakayi sai ka dawo da ita mahfuz amma ni lubna na gama zama dakai ka rubuta min takarda ta mahfuz wlh na gama aurenka”
Nace cikin ihun kuka tare da Kara cakumo rigarsa Mara gaskiya ko a ruwa yake gumi yakeyi Ina cewa Yana kamshin turaren Hadeeza ya hau zare Ido,gumi na tsatsafo masa ya jawo kwalar rigarsa ya hau dubawa bai kalleni ba ya runtsa idonsa na cigaba da jijjiga shi Ina ya sakeni
“Ki yarda dani ba wajen Hadeeza naje ba abokina ne ya fesa irin turarenta yarsa da na dauka yasa na goge janbakin bakinta”
“Kutumar uban abokinka da yarsa baka ma iya karya ba mahfuz,yaushe maza suka fara fesa turaren mata mahfuz bana kaunarka bana San ganinka idan baka so na tara.maka jamaa ka bani takardar sakina gobe da safe na bar.maka gidanan kaje kayi duk abinda kaga dama da Hadeeza”
“Lubna dan sakeni dan Allah dan annabi karki manta dare yayi mu Shiga ciki muyi magana”
“Bazan sake ka ba sai ka bani takarda ta mahfuz wlh dak’yar nake numfashi sabida ganinka da nakeyi mahfuz ka bani takardata”
“Lubna na rantse da Allah bazan iya sakinki ba Ina kaunarki dan Allah ki tsaya mu fahimci juna wlh indai Hadeeza ce zan rabu da ita wlh sabida na faranta miki rai na canja layin wayata yanzu ma na saka layin ne dan na kwafi lambobi dan Allah kiyi hakuri ki cikani”
“Mahfuz idan kaga na cikaka wlh ka furta kalmar saki a gareni mahfuz yau kwana daya da wuni duk abinda kayimin duk baka ga girmansa ba daga dawowa ta ka Kara koma Mata,Ina san da kake min yake mahfuz ka daina yaudarar kanka,Hadeeza kake so ba lubna ba dan haka Zan hutashe ka ka bani takarda ta ka aurota ko kuyi zaman daduron duk abinda ka yanke yayi daidai nidai ka sakeni”
“Toh ki cikani mu Shiga ciki na rubuta miki”
Da sauri na sake shi yayi hanyar palo da sauri nabi bayansa Ina Jin kamar na shako shi dagaske ba abinda nake burin gani sama da takardar sakina
Muna Shiga palon ya shige d’akina na bishi har d’akin da shigarsa ya daki ya duka a kasa duk wani abu da mahfuz zaiyi yanzu bakinsa nake gani,ba abinda zai fadamin da zai Shiga kunnena duk rokon nan da ya ringayi na dawo ashe na munafirci ne daga dawowa ta ya tafi wajen budurwa bazan zauna mahfuz ya saka min hawan jini ba,ban damu da durkusawan da yayi ba na hau dube duben inda Zan samu takarda da biro,drawers din dake gefen mudubi na nufa da sauri,na hau watso da tarkacen ciki jikina sai rawa yake tamkar yanda na kamashi da Hadeeza zuciyata ta ringa Kuna haka nakeji a yanzu dan Koda bangansu a taren ba kamshin turaren da yake da dan janbakin gefen wuyansa ya tabbatar min da wajenta yaje babu ma ja
“Lubna dan girman Allah ki nutsu muyi magana Lubna ko kasheni zakiyi bazan iya sakinki ba Ina kaunarki lubna wlh sanki bai tab’a raguwa a zuciyata ba daidai da second guda”
A zabure na jawo drawer na jefa masa cikin ihu Ina “Karya kake Yi mahfuz da kana sona bazaka ci amanata ba,da kana sona bazaka kawomin budurwarka har gida ka ringa kwanciya da ita,da kana sona bazaka fifita budurwarka a kaina ba Ina matarka ka wuceni ka barni a gida kaje wajenta dan kawai na hana ka kaina bayan duk abinda kamin mahfuz,kwana biyu da dawowa ka Kara koma mata Ina San yake anan ka fadamin mahfuz ka maidani shashasha ka wulakantani kaci mutuncina ka nunawa budurwar ka banida wani matsayi a wajenka har gidanku ka kaita mahfuz sabida tsananin san da kake mata duk abinan daka min ka dage na dawo daga dawowa ta ka Kara komawa wajenta,Mai na maka dana cancanci haka daga wajenka mahfuz,dame na rageka da ka fifita budurwarka a kaina laifi ne dan na soka na aureka har yanzu ba muyi shekara biyu ba mahfuz”
Kukan da yaci karfina yasa na kasa cigaba da magana sosai nake Jin ciwon abinda mahfuz yamin
Zafin da kirjina yakemin yasa na dafe kirjina da hannu biyu bansan lokacin daya iso ba sai ji nayi ya kamkameni cikin rawar murya Yana “Baki rageni da komai ba Lubna wlh duk abinda ya faru sharrin shaidan ne bansan Mai ya hau kaina ba Hadeeza shuuma yarinya ce bansan ya akayi ta ja raayina har na kawota ba wlh ba wai bana kaunarki bane Ina sanki wlh Allah kiyi hakuri ki yafemin ki bani dama na gyara kuskure na nayi alkawari duk abinda kikeso shi zanyi a gabanki zan karya layin Nan da Hadeeza ta sani dashi”
Rashin kwari yasa bama zan iya kwace kaina daga rukon da yamin ba kamshin turaren Hadeeza da nake Shak’a a jikinsa yasa nake Kara Jin zuciyata na zafi
“Wane irin kalamai ne baka min kafin na dawo ba wane irin ban hakuri ne baka bani ba kafin na dawo daga dawowata mahfuz ka koma gareta mahfuz ka daina wahalar dani kana wahalar da kanka ka sakeni kaje ka zauna da Hadeeza dan Allah ka daina azabtar dani ka rabu dani na bar Mata kai duniya da lahira”
“Bani naje wajenta ba lubna ita tazo ta sameni a wajen da naje cin abinci”
“Shine ta danneka ta maka fyade ko mahfuz”?
“Dan Allah kiyi hakuri Lubna ki tausaya min ki kwantar da hankalinki”
“Kwanciyar hankalina shine ka bani takardata dan bazan iya zama da fasiki ba”
“Toh naji ki kwanta gobe da safe sai na rubuta miki”
“Bazan iya kwanciya ba sai ka bani mahfuz babban burina ka bani takarda ta”
“Wlh Lubna Zan rabu da Hadeeza duk abinda kikeso wlh Allah zanyi na Miki na farko na Miki na karshe idan kin Kara kamani da ko waya Ina Yi da ita nayi Miki alkwarin Zan sakeki”
Haukace masa nayi akan lailai sai ya sakeni,ya dage da magiya kaina danajin Yana baranazar rabewa biyu yasa na samu waje a gefen gado na zauna,
Yana k’ok’arin nufoni na daka Masa tsawa akan ya fice min daga d’aki.
Ya fita da sauri na koma na kwanta
Banida burin da ya wuce garin Allah ya waye na hada kayana,mahfuz ya Saba da Hadeeza ko min daidaita bazai fasa nemanta ba banga amfanin zamana dashi ba.
Sam bacci bai ga idona ba sai wajen karfe hudu bacci yayi awon gaba dani.
Mahfuz
So yayi tana bude k’ofar ko bai dauketa da Mari ba zai jijjigata har shi zata kulle a waje , sam dabaran Kiran mahaifiyar lubna bai fado masa na sai dayaga dagaske Lunbna ta shiryawa ya kwana a wajen hakane yasa ya Kira Aunty nurse duk da bashida tabbacin zata dauki wayar ga mamakinsa a kira na biyu ta dauki wayar bayan ya gaisheta ya fada mata kulleshi da lubna tayi a waje a san ya kara Kare kansa yace Mata abinci ya tafi nema kafin ya dawo ta kulle tunda lubna ta dawo take masa rashin mutunci jiya ma koroso tayi daga d’akin,daga yanda take sallati yasan ta fusata hakuri ta bashi akan bari ta Kira lubna Yana zaune ba dadewa yaji an bud’e k’ofar.
Ransa a b’ace ya shiga gidan so yayi ya zubawa lubna rashin mutunci Yana parking ya doshi wajen da take tsaya ga mamakinsa kafin ya Isa wajenta ta iso wajensa tare da cakumar rigarsa tana ya bata takardar sakinta haka kawai yaji gabansa ya Fadi har ga Allah inta furta sakin nan sai yaji hankalinsa ya tashi