BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nazy yace a a shahida sannu da zuwa, bari akawo miki lemo, tace no nazy aida ka barshi ma, yace a a ai baqonka annabinka inji bahaushe, yafadi haka yana kallan Shahid, saiyaga shi idonsa arufe yake ma, aransa yace Lalle wannan gayen da gaske yake

Okasha ma yace aida kin fada mana zuwan naki da mun Dan gyagygyara gidan namu, Amma haka kin samemu…. Be qarasa ba yana murmushi tace Ayya babu komai okesh

Hmm Wai okesh, ni batasan wannan qyale qyalen na yanmata baya gabana ba, inji Shahid aransa

Nazy yana kawo Mata lemo yayi daki, Shima okasha haka
Tashi tayi ahankali tadawo kusa dashi ta zauna

Tasan ba bacci yakeba, kawai yayi hakane saboda bayasan ganinta, Dan haka tace kayi hakuri Ina takurama, dama nazo inyima sallama ne zanje nigeria yayanah yana aure

Bai Bude idonsa ba yace Allah ya kiyaye

Kallansa tayi tasaki murmushi, ita komai yayi wallahi birgeta yake, Dan haka dubu sajen fuskarsa, kamar tasashi a gaba taita kallo

Jakarta ta ajiye, ta miqe tafara gyara falon, tas takwashe abinda yake ciki, su gwangwanin lemukan dasukasha, tagyara kujerun, ta Kade su sosai, zuwa tayi dede inda yake, tarasa me zata ce masa. Dan haka tabude jakarta da sauri ta dauko wayarta, tafara tashinsa dede hannun sa tadan daka da wayar, Bude idonsa yayi bece mata komai ba, tace ko zaka Dan matsa zan gyara wajan ne

Waye yasaki?
Jikinta ne yayi sanyi
Tace kayi hakuri
Tashi yayi bece mata komai ba, yakoma kan kujera saida ta gama tsaf, sannan tadau jakarta tace to Sai Allah yadawo Dani lafiya

Kawai daga mata hannu yayi, tana kallansa harda Wai waye sannan tafi ce daga gidan

Tana fita su nazy suka dawo, hada ido sukai da okasha, okasha yace ah ashe har soyaiya tayi Nisa kenan, Kuna aiki tare, kaga muma munci albarkaci kunyi mana gyaran falo yau

Kallansu yayi yace ni? Dani zatai aiki?
Tab

Daga haka basu sake cewa komai ba Dan sun lura akusa yake

***        ***       ***

Jama’ah duk sun jigata, muna isa directly gidan momy aka kaimu, part dinta aka nufa Dani, qannan baba ne na Niger suka bani umarni in shiga da addu’ah haka akayi kuwa
Gidan cike yake da baki maqil, muna zuwa aka saukemu awani daki, maisah tana tare Dani, abinci aka kawo mana kowa yaci, nikam bawani na kirki naci ba, mukai wanka, wani less suka sake bani na saka light green sosai nayi bala’in yin kyau
Babu Bata lokaci Abba yaturo inje, nida yan’uwan mahaifina da maqotanmu muka tafi, kaina a lullube, Bayan ansake gaisawa ne
Suka bada amanata, sosai Abba ya karbemu hannu bibbiyu, momy ma babu yabo babu fallasa

Nan suka fada masa da safe suke San wuce, yace babu damuwa Allah yakaimu
Dakin da aka bamu muka dawo, sosai Dakin ya birgeni, kuma Wai ahakan ma na saukarmu ne, banawaba

Abba ne yadubi hajiya yace kiramin daddy awaya mana

Tana kiransa babu Bata lokaci yazo, yana cikin yadi fari mai mutuqar tsada, yayi kyau sosai
. Yana zama Abba yace Ina jabir?
Yana daki yana jirana Abba
OK kiramin shi

Wayarsa yadauka yakira jabeer
Kansu Akasa dukansu Abba yace jabeer sannu da zuwa ya hanya? Saikuma Mota ta lalace muku ahanya ko? Gashi babu yanda za’ai saikuka dawo gida bakuje wajan daurin auren ba

Jabir yakasa dago kansa, yace Abba kayi hakuri munyi laifi

Babu komai ai rayuwa ce, abinda zan fada muku kenan

Iyayen yarinyar sunzo kwana iya zuwa ku gaisa, inkuma hakanma kafin ku qarasa kafafunku zasu fara ciwo, zaku iya zama basai kunje ba

Wai yanzu alhaji saboda Allah Akan wannan yarinyar da aka dauko daga wani kango zaka dinga musu wannan fadan, haba alhaji

Wato juwairah Naga alama kece kike daure wa Yaron nan gindi yake abinda yaga dama
Auren nan de anriga da andaura, matarsa ce, bamu sa iko akanta saide muyi musu fatan zuri’ah ta Gari

Saida taji zance zuri’ah, sannan tayi ajiyar zuciya tace to Allah yabada Zaman lafiya

Abba yace dade yafi muku, yatashi yayi ciki ko sake kallan su daddy beyi ba Wanda kansu yake sunkuye

Aisai kuje ku gaisa, itama ta tashi tatafi

Jb yace kaga abinda nake fada Maka ko? Kaga abinda kajawo mana ko?
Abba yana ganin mutunci na Kasa yana yimana fada da girman mu da hankalin mu

Katashi muje

Kansa yariqe da hannun sa, shi tunda yake da iyayensa basu taba yimasa irin wannan fadan ba, bayasan damuwa ko kadan

Amma yanzu Akan wannan yarinyar har ran Abba yabaci yatashi yatafi yana yi musu fada

Jb kaje ku gaisa, gobe kafin su tafi zanje mu gaisa insha Allah

Yana fadar haka Shima yayi part dinsa

Girgiza Kai Jb yayi, yatashi yanufi part din su Amal

Lokacin dayaje harta tashi zata cire kayan jikinta ta kwanta, aka fada musu ga abokin ango yazo, har qasa ya tsugunna yagaidasu, sunata tambayar sa Ina ango Ina ango, yace bayajin dadi ne, Amma yace kuyi hakuri gobe yana Nan tafe insha Allah

A a babu komai wallahi

Tashi yayi zai tafi, aransa yace shi bemaga amaryar ba

Aikuwa Kamar sun San me yake cikin ransa, yana fita suka tura Amal taje tayi masa godia, kuma tace tana yiwa angon Allah yasawaqe

Yana tafiya yaji taku abayansa, yana juyawa sukai ido biyu dashi

Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya tsara wannan halitta

Amal ce ta katse masa tunanin sa da fadin

Mungode abokin ango

Jb ya zuba mata ido, wannan zazzaqar murya haka

Yace a a babu komai
Kece amaryar Tamu ne?

Karkada idonta tayi, tace nice, shidin meya hanashi zuwa?

Jb cikin ransa yace tofa, da alama wannan bazata ragawa daddy ba, wannan wanne irin zama za’a yi?

Cikin sauri yace bayajin dadi amarya Amma gobe ai dole yazo

Tabe baki tayi tana juyawa tace to Allah yasawaqe, mungode saida safe

Bayanta ya kalla, cikin ransa yace gaskya Allah yayi halitta anan, aikuwa dole inje infesawa abokina

Yana fadar haka cikin ransa, yayi part din daddy

Mrs Usman ce ✍????????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

11

Ina dawowa daki nakwanta, maisah tace gobe iyanzu kuma muna gida, ke maisah yanzu har murna kike zaki tafi ki barni
Zan tafi may be ba Lalle bane Inga mijin ki

Ni Ina miki maganar tafiya Amma kinamin zan can wancan me kamar gunkin
Amal mijin ki nefa, be dace kidinga fada masa hakaba

Ajiyar zuciya nasauke nakwanta tare da juya mata baya, bacci nayi me dadi cike da mafarkin Yaya Shahid

  ***      ***       ***

Kai abokina gaskya kayi babban kamu
Kaga matarka kuwa? Gaskya ta hadu ba qarya

Jb Dan Allah kayimin shiru, kazo Sai zuba kake kamar aku, daga ganin yarinya, bafa ita bace, ita wannan yarinyar batada lafiya larura gareta

Sannan koba hakaba, yanzu jb har yaushe zan iya mantawa da salma har inso wata Bayan ta? impossible jb

Shiru jabir yayi, shide yasan wannan yarinyar daya gani itace amarya, to Amma besan wacce larura daddy din yake nufi ba, may be ta aljanu ce

Dan haka kawai sai yayi shiru

  ***      ***      ***

Washe gari da wuri baqi suka shirya, saboda nisan hanya, Babu Bata lokaci aka kawo musu abinci, da abinsha, kowa Sosai yayaba, dazasu tafi Abba yabada motoci a mayar dasu, Amal ta riqe maisah banda kuka babu abinda take

Maisah karki tafi Dan Allah, Amal dole zan tafi, insha Allah nayi miki alqawarin watarana zanzo mu wuni, saina koma Amma banyi miki alqawarin kwana ba, Toshiknn maisah ki kula min da iyayena, ga wannan wasiqar Dan Allah ki kaiwa Yaya sham
Kiyi masa bayanin komai kice masa ya yafemin, sosai suka rungume junansu suna kuka, manyan ne suka qara yi Mata fada, sannan suka fita, zama tayi agefen gado ta dinga aikin kuka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button