BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna fita harabar gidan, Amma yabada umarni akaisu gidan daddy suga gidan da Amal din zata koma da zama, haka akayi kuwa sunje gida kuma sun yaba, gida kamar ba’a qasar Nigerian kakeba

Daddy! Daddy!!
Wallahi katashi baqin nanfa zasu tafi, miqa yayi tare da addu’ar tashi daga bacci, dagashi sai jallabiya yafuto harabar gidan
Abba banda harararsa babu abinda yake

Yana qarasowa maisah cikin ranta tace tab wannan daga ganima may be shine angon, aikuwa har qasa ya tsugunna ya gaidasu

Yana basu hakuri Akan rashin zuwan sa jiya, sosai suka fahinceshi, sukace ai dama abokinka yace bakajin dadi

Baice komai ba, yasa hannu a aljihu ya ajiye musu damin kudi, yajuya yakoma

Maisah cikin ranta tace Allah Sarki Amal, kowanne irin zama za’a yi anan? Sam baya magana, ai dole ma ta dinga cewa gunki

  ***       ***      ***

Kuka na nake ni kadai adaki, Danaga babu inda kukan zai kaini, tashi nayi nashiga toilet nayi sabon wanka, Riga da sket nadauka acikin atamfofina mai launin purple na saka, dinkin yahau jikina kamar Danni akayi, ban daura dankwalin ba na futo falo na zauna nazuba uban tagumi, Babu waya bare inkira yan’uwana inji Yaya suke, Amma ai nariqe number kowa akaina, ko wayar ma’aikatan gidan nasamu zan kirasu umma da Yaya Shahid dina

Ina wannan Zaman bansan lokacin da bacci yafara daukana ba a kwance Akan kujera

Sosai ya hade cikin suit ruwan toka, yayi masifar yin kyau, yana fesa turare jb yace Toni zan wuce
Amma daka cire wannan kayan Kasa manya saboda kasancewarka ango yau

Kallansa yayi bece komai ba qarshe ma sai yace ka gaida gida
Tare suka futo, jb yafita shikuma yayi part din iyayensa
Yana zuwa yaga momy afalo, Bayan ya gaida tane, yamatsa jikinta, yadora kansa Akan fadarta yayi shiru
Sumar kansa dataji mayuka ta shafa, tace muje nabaka abinci ko

No momy banjin yunwa saide ko anjima

Kallansa tayi, tasan Sarai yanajin yunwa Amma saboda wannan auren yasa shi a damuwa har yaro bayasan cin abinci, Dan haka tayi shiru, tana shafa masa kansa
Abba ne yasauko daga daki,
Daddy na ganinsa tunma kafin ya gaidashi, yace kai tashi kaje kakiramin matarka zanyi magana daku

Mata?
Shi wallahi Yama manta da wannan yarinyar

Tashi yayi yatafi, iyayen suka bishi da kallo

Yana zuwa falon, yabi ko’Ina da kallo, har zai shiga daki yaga mutum Akan kujera, yasan de kowa yatafi Dan haka wannan itace

Tana kwance tana bacci, kyakkyawar Fuskarta ta bayyana, gashin idonta ya kalla Zara Zara dasu, sannan yabi Dan qaramin Bakinta mai launin pink color da kallo, goshinta ya kalla duk suma, alamar tana da gashi

Tsayawa yayi ya zuba mata ido yana kallo

Yana tsaye baisan lokacin daya tsugunna ba, yakafa mata ido, kawai yana kallan ta, meyasa komai nata yake da kyau haka?
Ba lefi gaskiyar jb ne, tanada Dan kyau, to Amma meyasa take sa wannan baqin abin aface dinta?

Wayarsa ce tayi qara, Dasauri ya miqe tsaye, yana picking Abba yace Bata nan ne?

Gamu nan zuwa Abba

Memakon ya tasheta a a saiya nufi fridge yadauko ruwa, yabude murfin ruwan, yafara tsiyaya mata ajikin ta
Azabure ta miqe tana salati
Sanadin haka ne yasa Dan kwalin kanta da bata daura ba yafadi

Zubawa gashin kanta ido yayi, yanzu wannan yar mitsitsiyar yarinyar har tasan tasaka attached Akan ta?
Lalle duniya tazo karshe

Kallansa tayi, da alama kallan cike yake da Jin haushi

Aranta tace azzalumi kawai

“ki tashi Abba yana kira “

Yana fadar haka ya wullar da robar ruwan
Yayi hanyar waje, har yaje bakin qofa yajuyo, ya kalleta, alokacin ta kama gashin kanta tana nadeshi akanta kamar ribbon

Tana gamawa tasaka hijab dinta, sai tayi kamar Tasa ribbon acuci maza

Abaya ta biyoshi ,yana gaba tana binsa abaya, sai harararsa take daga baya
Dahaka sukaje har folon
Momy da kallo ta bita, aranta tace kidahuma kawai, ji wani uban hijabi, Wai ita yar Malam

Yanda taga yayi, haka tayi itama, ta zauna aqasa, tana gaidasu ba yabo ba fallasa momy ta amsa

Abba kuwa tuni yafara fara’ah, yace Amal ki saki jikinki kinji, ki dauka kamar gida ne, muma kamar amatsayin iyayenki muke, da nan dacan duk daya ne kinji, kanta asunkuye tace to Abba Allah yaqara girma

Momyyyy nah, dahaka tafara tafado falon cikin murna tana rungume mahaifiyar ta

Anty mufy tace yar renin wayo, kizo kidau jakar ki, Babu bawanki anan, haba mufeeda, yanzu daga dawowar taku daga airport kike mata fada?
Yanzu fa ta duro qasar

To yanzu momy haka za’a bar yarinyar nan baza’a yi Mata fada ba, haba momy

Qarasowa falon tayi, daddy dasuke zaune qasa shida Amal, takaiwa rankwashi akansa

Dafe wajan yayi yace auuuch, kamar zaiyi kuka yace Haba anty mufy

Tace ohh bakai baka iya gaisuwa ba
Yana shafa wajan yace Mata morning

Tana daria ta zauna a kujera kusa da Abba

Amal ta dago kanta tace mata Ina kwana?
Cikin fara’ah tace lafiya kanwata ya kwanan baqunta
Alhmdlh kawai Amal tace

Abba ne ya kalli Shahida yace baki iya gaisuwa bane? Kallan daddy tayi tace Yaya daddy good morning, Ala Sanya alkhairi

Ko ‘a’ baice mataba

Sake kallan ta Abba yayi, tuni tagane manufarsa, kallan Amal tayi tana yatsina tace yakike?

Lafiya, Amal tabata amsa ataqaice

Cikin ranta tace dubeta Dan Allah, gashi de tanada kyau Amma ta boyeshi, tawani saka hijab, ita abinma abin qyanqyami
Kallanta tasake yi afakaice, ita kamar tana mata kama ma da wanda tasani

Abba ne yamiqowa, Amal kwalin waya qirar tecno yace gashi Amal, kidinga amfani da ita, ki bayar data hannunki

Cikin ranta tace Abba kenan nikam dama Ina Naga wata waya

Karba tayi tana godia

Ga wannan kuma, mukullin motar dana Sai miki ne, daddy zai koya miki da kansa

Kaikuma ga wannan

Mukullin ya kalla yagane Sarai na gidansa ne, Dan haka yaqi karba yazubawa Abba ido

Cikin fada Abba yace karbi mana
Amma Abba key din wancan gidan nefa

Abba yace sosai

Kansa ya sunkuyar yace Abba kayi hakuri bazan iya rayuwa agidan nanba, bazan iya shigaba, zai sani a damuwa

Zaka karba ko bazaka karba ba?

Ganin abban ya hade rai ne yasa yakarbi key din

Abba yace tashi kadau matarka ku tafi, za’a biyoku da kayaiyakin ku, basai kun dawo ba

Tashi yayi fuskar nan babu alamun wasa yafuto
Nima sallama nayi musu natashi, nafita

Abba yadubi mufy yace mufeeda kije keda shahida ku sa ma’aika ta sudau kayan kuje ku tayaasu gyaran gidan

To Abbanah inji mufy

Tashi yayi yakoma daki, mufeeda ma tayi part din daddy zata sa afara futo da kayaiyakin sa

Shahida ta kalli momy tace momy yaushe za’a fara dinner ne, na matsu in fadawa friends dina, suzo mu cashe

Babu abinda za’a yi shahida, abban ku yahana, bansan menene dalili ba, Koda yake garama ai Kar ayi komai din, Dan idan muka gayyaci mutane dayawa, aka tambayemu yar waye aka bawa daddy, bansan me zamu ceba

Gara Kar ayi taron dade muce yar Malam ce datake wani kango aka dauko

Ni momy meyasa ma Abba yake yiwa Yaya daddy hakane, Amma to momy shi yayan yana Santa ne?

Tabe baki momy juwairah tayi, tace oho masa, shi Ana gane alqiblarsa ne

Ai shikkenan, yauwa momy namanta ban baki labarin Shahid dinaba

Kallan mamaki tayi mata, shahida da soyaiya

Tace waye kuma shahid? Cikin shagwaba tace kaiii momy
Boyfriend dinanefa

Murmushi tasaki murmushi tace tofa, zamani Ina zaka damu?

   ***       ***       ***

Muna fita harabar gidan, Naga Sai huci yake kamar wani zaki, kallan motor sa yayi yakaiwa tayar motar duka da qafa, sannan yabude yashiga, yayi reverse
Nayi tunanin tafiya zaiyi yabarni, sainaga ya tsaya, Dasauri nabude Bayan motar nashiga tare da rufewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button