BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
“ni direban ki? “
Kamar wasa ta tsinci maganar sa, Dan haka ta futo Takoma gaban motar suka dau hanyar gidansa
Aranta tana tambyar kanta to meyasa bayasan shiga gidan?
Nashiga uku kode aljanu ne agidan?
Kokuma wani Abu aka masa yace gidan zai sashi a damuwa?
Meyake nufi da hakan?
(nikuwa nace tambayeshi)
Suna Zuwa kofar gate din dayake gidan ba Nisa, iliya mai gadi yazo ya wangale musu gate
Harabar gidan ta kalla da swimming pool tafara tozali, gashi an qawata shi da flowers
Yana ajiye motar ya shige gidan ransa abace
Dasauri ta futo tabi bayansa, Saman beni taga yahau Dan haka ta nemi kujera a falon ta zauna
Daga kan dazatai idonta yayi tozali da tamgamemen photonsa shida salma, tana rungume ajikinsa suna murmushi
Gabanta ne yafadi bade aure ne da mutumin nan ba
Dama yana murmushi?
To Amma wacece wannan,? Kode Shima ta addabeshi ne shiyasa yaqi Zaman gidan Amma shine ita aka yayimota aka kawo ta
Photon ta zubawa ido tana kallo
Ahankali taji taku akanta, tana daga Kai, ta ganshi yasauko da key ahannunsa
Yabude wani Dakin aqasa yashiga tare da banko kofar
Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
12
Tagumi na rafka, saikace Wanda nayi masa wani Abu zai dokomin kofa , da abayansa nakema saide injita afuska ta
Hijabin jikina nakama nacire, nadaure kaina da dankwali
Naci gaba da Tagumi Ina tunanin wannan sabuwar rayuwa dazan fuskanta
Yarinyar dazu natuna, daga gani zatai rashin kunya, kuma wallahi bazan daukaba, kodan mema yahadani da ita, dazan kulata Ina asarar mutunci na dana iyayena
Ina wannan tunanin Naga anfara shigowa da akwatuna
Nawa aka fara shigowa dasu Ana ajiyewa a falon
Sannan na daddy
Anty mufy ce tashigo da murmushi afuskar ta, kusa Dani ta zauna, tana cire mayafin jikinta
Tace qanwata ki saki jikinki kinji, nan gidan mijin ki ne
Kinji? Tafadi haka tana murmushi
Ban iya cemata komai ba Sai gyada Kai
Am raliya Dan Allah Kai mana wadannan akwatunan wannan Dakin ta nuna wani daki kusa da wanda daddy yashiga
Nan da nan suka Kai akwatunan Amma na wajena
Kallo na tasake yi da murmushi tace Ina mijin ki yake?
Diriricewa nayi, Wai mijina
Ina in Ina nace mata yana Nan
Na nuna mata Dakin daya shiga
Kallo na tayi da murmushi ta tashi tashige Dakin
Gani nayi ta futo, yabiyota abaya
Hannayensa suna cikin aljihun wandon suit dinsa
Zama tayi kusa Dani ta dafa kafada ta, tace Amal
Kinga wannan? Ta nunamin daddy
Ku biyu zaku zauna agidan nan, bayasan ma’aika ta, saboda haka ki ware ki saki Jikin ki
Idan aiki yatashi kiyi masa magana yazo kuyi tare
Karki yarda yabarki da aiki ke kadai, ta dubeni tana murmushi tare da fadin kin gane?
Kallan Wanda ake maganar akansa nayi, Naga shi ko ajikinsa, yana tsaye yana zagaya wa acikin falon, juyowar dazaiyi idonmu yahadu
Dasauri na sunkuyar da kaina
Duk atakure nake jina, ni ban saba cire hijabi naba inba agaban Yaya Shahid ba
Kamar tasan abinda nake tunani tace muje dakin mu shirya kayan ko
Nace to
Muka shige Dakin dayake amatsayin nawa, tajuyo ta wurgawa daddy harara
Wai ita datace yazo yazauna a falon yabarni ni kadai shine yazo yatsaya mana aka kamar wani soja
Muna shiga Dakin ta jeramin akwatunan waje daya
Ta shirya min gaban mirror na
Ta Bude jakata ta shirya min wasu kayan, sauran tace idan nagama insaka su awani wajan daban
Gaskya Dakin ya birgeni sosai, komai pink color ne adakin,
Toilet din babba dashi
Muna gamawa takama hannu na muka futo falon, yana zaune adaya daga cikin kujerun falon
Kitchen muka shiga, da ita, haka ta ware tana fira tana Jana da surutu, nadan fara sakewa da ita, pride rice mukayi Sai farfesun kaza, dayaji kayan qamshi
Duk abinda Naga bansaniba a kitchen din, warewa nayi nake tambayarta, sosai na fahimci komai cikin qanqanin lokaci
A dining muka ajiye komai, tace Amal zuba mana abinci Ina zuwa
Wajan daddy ta nufa, tana zuwa takama kunnansa taja, da karfi yace wayyo anty mufy
Tace wuce muje Kaci abinci, tana riqe da kunnansa takawo shi har dining din, nikuwa Ina kallan su, sai suka bani sha’awa, nan take na tuna da Yaya Shahid dina
Cikin shagwaba yace anty mufy nifa na qoshi
Ban yardaba qanina,maza Bude bakinka
Haka ta dinga bashi abinci da kanta, Babu abinda suke tunamin irin lokacin da yayanah yake bani abinci agida, wani Abu na baqin ciki ya tokare min baqoshina
banda juya spoon din babu abinda nake
Juyowa tayi tace saura ke Amal
Dasauri nace anty na qoshi
No ban yarda ba, haka tabani abinci da dakanta, naci, gaskya matar nan tana da kirki sosai, nafadi hakan cikin Raina
Muna gamawa tace Toni zan wuce qanina, sai wani lokacin kariqe Amal sosai
Tace qanwata zomuje ki rakani zan tafi
Kamar zanyi kuka nace Dan Allah karki tafi
Juyowa yayi ya kalleni,fuskar nan atamke wato za’a barta da dodo ko aljani ko
Murmushi anty mufy tayi tace karki damu, duk lokacin da kikesan ganina ki fadawa daddy zai kawoki har Abujan kinji
Cikin sanyin jiki na girgiza kaina
Hannu na takama muka shige dakina, Shima daddy tashi yayi yahaura sama
Muna shiga Dakin muka zauna abakin gado, takama hannayena duka biyun tace
Amal, Dan Allah ki kula min da qanina, daddy yana buqatar kulawarki, karki damu da rashin maganar sa, haka yake, zaku zauna dashi maganar minti biyu bazata shiga tsakaninku ba
Sai Bayan zuwan salma cikin rayuwar sa ne muka Dan samu canjin halayensa
Bansan lokacin da bakina ya furta wacece salma?
Kai tsaye tacemin matarsa ce
Cikin Raina nace ai dama nafada
Anty mufy taci gaba da fadin matarsa ce Amal, Amma Allah yayi Mata rasuwa
Yana tsananin kaunar ta, itama haka, iyayenmu basuda wani Jin dadi da kwanciyar hankali, kasancewar mu yan kadan
Bamuda kowa
Kuma Allah Bai bamu haihuwar Akan lokaci ba, na dade da aure Amal, Amma har yanzu Yarona daya, salma ta samu ciki, wanda muka dauki son duniya muka dorawa cikin
A qarshe datazo haihuwa ta rasu itada abin dayake cikin ta
Daddy ya fuskanci qunci, kuma har yanzu shine yasa bai dawo normal ba kamar yanda yake da
Kinsan Abba Dan siyasa ne gaba da baya, sau biyu yanayin govnor Awannan jihar, daddy kuma ya riqe muqamin sanata sau daya
Hakan ne yasa ayanxu haka suka tsaida shi Dan takarar govnor na wannan jihar, wanda za’ai zaben nan da wata daya insha Allah
Salma ta rasu Awannan gabar, hakan ne yasa Abba yahadaku aure keda daddy, saboda cancantarki, saboda yasan zaki iya kula dashi,
Ki tayashi da addu’ah, Allah yasa adace a zaben dazamu fuskanta
Addu’ar mata Akan mijinta Bata hijabi awajan ubangiji, naroqeki kidinga sa daddy acikin addu’ah Bayan kinyi sallah
Kati ta dauko ta miqamin, dakyar na karba saboda yanda jikina yayi sanyi dajin kalaman ta
Tace Number na ce, idan da matsala, kokuma akwai abinda yake miki Wanda bakya so, saikiyimin magana ta waya
Nizan tafi, daqyar na iya cemata to anty nagode, saboda yanda jikina yayi sanyi, kenan auren rufin asiri akamin, saboda anaso yaci Zabe, Kar ya zauna baida mata
Muje na rakaki anty, a a Amal kiyi Zaman ki ki huta, driver na jirana awaje, ki kula da kanki da mijin ki, sai anjima
Tana fita, bansan lokacin danaji hawaye ba, ni anrabani da Yaya sham, anrabani da yayanah mai sona Yaya Shahid
Anzo an liqawa Wanda bai damu daniba, hakan yana nufin dazaran yaci zabensa banda wani amfani kenan