BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ke garama hakan, gara yaci zabensa yasakeni naje na auri dan’uwana

Wayar da Abba yabani na kunna aikuwa naganta da cajin ta, da Sim card aciki Ina duba balance dinma Naga ten thousand aciki, ido na zaro, towama zan kira da wannan uban katin

Wayar umma nafara kira cikin zumudi

  ***       ***     ***

Yanzu kenan tafiya zakiyi shahida,?
Tafiya zanyi nusy, tunda baza’a yi wani bidiri awajan bikin ba
Gobe zan koma school insha Allah

Nusy tayi fari da idonta, tace to ai kya kaimu gidan yayan naki muga new antyn naki ko

Dena ba tamin rai nusy, kidena min zance yar qauyen nan please

Shikkenan kiyi hakuri qawata yanzu de muje

Motar shahida suka nufa, suka shiga su biyar, da nusy babbar qawar shahida a Nigeria, sai sauran mutum uku, suka nufi gidan daddy

 ***     ***     ***

Ina gama waya da umma nakira baba, haka yayita tambayata babu abinda akemin de ko?
Nace babu, yace idan akwai abinda mijin yakemin in kirashi infada masa, tare da turo masa da address din gidan, in bashi awa hudu zuwa biyar

Daria ce takamani nace baba babu komai, yace to Allah yayi miki albarka

Muna sallama dashi, nakira yayana, shikuwa alokacin yaga sabon layi, daga nigeria, jiyake shahida ce Dan haka yaqi picking

Saida nazy yace masa, Ana kiranka fa Shahid, cikin sanyin murya yace share ta nazy nasan wannan yar wahalar ce, Amma Shahid yakamata ka kirata kaji me zata fadama

Nikuwa awajena Danaga bai dagaba saina sake kira

Ina kira cikin fada yace, Wai miye ne?

Nace yayanah, kaida waye?
Yana daga kwance baisan lokacin daya tashiba, yace Amal? Dan Allah kece?

Daria nasa nace nice yayanah, I miss you so so so much

Amal miss you too, ina mijin ki kika kirani? To yayanah dole Sai yana Nan zan kiraka?

Yaya banasan auren nan

Tokiyi hakuri qanwata, muyiwa baba biyaiya insha Allah zamu ga ribar hakan

Yaya ba wannan maganar ba, bani labari

Yace wai waye yabaki waya ne? Kafin ta bashi amsa aka qwanqwasa Dakin
Dan haka tace yayanah Ina zuwa zan kiraka, tana kashe wayar itama tana turo Dakin tana shigowa

Ajiye wayar tayi, ta miqe tsaye, ta zuba mata ido, Riga da wando ne de ajikinta kamar kullum

Tana yatsina tace sannu ko

Amal data gama gane yarinyar batada mutunci Kai tsaye tace yauwa

Zaki futo ki gaisa da qwayena suna falo, tana gama fadar haka tafi ce,

Afili Amal tace yarinyar nan yar renin wayo ce

Dan kwalin ta ta yafa akanta tafice zuwa falon

Tana fita su nusy suka kwashe da dariya harda nunata da hannu

Kallan jikinta Amal tayi, tana neman makusa ajikinta

Sukuwa suka miqe suna cigaba da daria, shahida tace jiwata shiga Dan Allah yar qauyen qauyawa, kidahuma dake waike kinzo amatsayin matar yayanah ko

Nunata tayi da hannu tace Dan Allah kiduba kuga wadda takesan zama new first lady in bauchi state
Taqarasa maganar tare da dungure mata Kai, har Dan kwalinta yafadi

Hakan ne yayi Sanadin baiyanar dogon gashin kanta

Gaba dayansu suka hada wajan fadin attached?

Shahida tace au kina nufin da wannan abin zaki yaudari yayanah?

Nusy bani Reza

Aikuwa tana Bata ta nufi gashin Amal gadan gadan, ta riqe shi zata yanke, bige mata hannunta Amal din tayi
Amma ko gizau shahida batayiba

Ganin haka yasa Amal dukan hannun shahida, suma su nusy suna ganin haka suka rirriqe Amal
Shahida zata dora rezar akanta, Amal tafara ihun kuka, saboda sarkin yawa yafi sarkin qarfi

Ku qyaleni!
ku rabu Dani nace!
da karfinta take fadar haka

Shahida takama gashi ta riqe, Amal tana qoqarin qwatar kanta har suka yanketa a hannunta

kamar wasa yaji ihu aqasa

Kuma kamar fada ake

Tashi yayi, dagashi sai wando ajikinsa three quarter, baqi Sai Riga yar qarama data kama jikinsa, dantsan hannun sa sun futo sosai

Saboda yana hutawa ne

Dasauri yasakko qasa, cikin tsawa yace ke shahida!!!!

Dasauri suka saki Amal, tana kuka tana yarfe hannunta inda suka yanketa

Wani mugun kallo yamusu baice musu uffan ba, suka fice cikin sauri

Kallan sa yakai kanta, ahankali ya tsugunna dede inda take zaune tana kuka, yazubawa gashin kanta daya barbaje ido, dama wannan yarinyar gashin tane haka?
To Amma de duk yanda akai sudin ba Yan nigeria bane

Hannunta ta rufe da dankwalinta dede inda yake jinin

Cikin kuka tace masa Dan Allah na roqeka, idan Kaci zaben kasauwaqe min, inje in auri Yaya Shahid

Ni bazan iyaba

Kallanta yake shi har yanzu mamakin gashin kanta bai sake Shiba

Cikin ransa yace SHAHID

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

13

Yanzu wannan yarinyar har tasan soyaiya?
Dududu ma nawa take? Yar qarama da ita har tasan asaketa ta auri wani? Waye wannan Yaron? Waye shi?
Hake yake fada cikin ransa, yayinda azahiri ya kafeta da idanunsa
Tashi yayi yabar ta awajan, yahaura sama

Tana ganin tashin sa tabishi da harara, tashige dakinta da gudu tafada kan gado tasaki wani malalacin kuka
Itada ko malami ne yadaketa a makaranta yayanta da mahaifinta basa zama Sai sun rama mata itace wata yarinya da aqalla Bata wuce sa’arta ba ta yanka da Reza

Yana shiga dakinsa yafada kan gado tareda hargitsa sumar kansa, shifa bayasan damuwa, gashi tun ba’a je ko’Inaba yarinyar nan tafara haddasa masa husuma

Tana daki tana bawa kanta hakuri tare da goge hawayen idonta, taji anbude kofa
Qin dagowa tayi bare ta kalleshi
Tsayawa yayi akanta, yana Kallanta, tayi rub da ciki, gashin kanta yabazu Akan gadon kamar wata aljana
Matsawa yayi dede inda take, yakai hannu zai tabata saiya fasa
Yasake Kai hannu akaro Nabiyu, Shima yafasa
Sai akaro na ukun ne yafizgi hannun nata da karfi
Batasan lokacin datasa qara ba wayyo baba wayyo Yaya Shahid

Ko kulata baiyi ba, ya tsugunna yafara treatment din hannun nata
Kanta ta sunkuyar saboda azabar datake ji, hakan datayi ne yabawa gashin kanta damar rufewa daddy fuska

Dago kansa yayi yana Kallanta, gashin ya zubawa ido, kamar bazai taba ba, saikuma yasa hannun yakawar dashi, yaci gaba da wanke mata wajan

Hannun ya kalla fari tas dashi, farcen ta gwanin sha’awa
Ahankali itama ta Dago da kanta, tana kallan yanda yake aikin
Ta shagala a kallansa, Sarai yasan kallansa take shiyasa yaqara tamke fuskar sa

Yana gamawa yasaki hannun, yafice yabar Dakin

Ita kuwa da idanu ta bishi, mayar da gashin ta baya tayi, ta kalli Dan yatsanta inda yaduba, ta kwanta awajan bacci me nauyi yadauketa

  ***      ***    ***

Amma Lalle yarinyar nan, jibafa yar qarama da ita har tasan duniya, shahida tace shiyasa nace muku bansan zuwa gidan, Dan zuciya ta zafi take, zatasa inyi abinda banyi niyyaba
Nusy tace to kiyi hakuri Kawai ai akwai wani lokacin saimun nuna mata ita yar qaramin matsiyaci ce
Dahaka sukai sallama, tatafi gida

  ***       ***     ***

Sai magrib na farka daga baccin danake, ahankali natashi nacire kayana, har banasan dungurar wajan da aka yanka ni, towel na daura nashiga toilet
Nayi wanka, sai dangale hannun nake, da hannu daya nashafa mai na janyo doguwar rigar material acikin kayana mai launin blue, tayi kyau sosai, nasaka, da hannu na mai ciwon nadanne Bayan rigar, marar ciwon kuma Naja zif narufe bayana
Ko falon ban komaba, Naja wayata nakira maisah, nabata labarin abinda qanwar daddy tayimin
Rumaisa tace subhanallah, Amma wannan yarinyar batada mutunci, kiyi hakuri Amal, komai lokaci ne
Maisah wallahi baba zan fadawa yazo yadaukeni ni bazan iyaba maisah, wannan jaraba har Ina,
A a Amal, kinsan halin baba, abinda zaiyi kowa ba zaiji dadi ba, kiyi hakuri, kiyiwa mijin ki biyaiya, ayanxu aljannarki kike nema awajansa, ita qanwar sa ba aurenta kikeba, shi kike aure

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button