BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nace hakane, nan nabata labarin anty mufy, maisah tace kinji ba, tunda kikaji yar’uwarsa tace haka yake, to kiyi masa uzuri, idan abin maganar yakamaki ke kiyi masa kece aqasan sa
Nace to maisah nagode

Nabawa Yaya sham latter ki Amal, yayi ta kuka, kamar ba namiji ba, ni har yabani kunya ma, nace Allah Sarki Yaya sham, yasoni maisah, tace hakane, Allah yasa hakane yafi alkhairi nace amin

  ***      ***     ***

Momy cikina ciwo, subhanallah Wai shahida har yanzu baki dena wannan ciwon marar ba?
Kai ta daga mata alamar eh
To sannu bari Akira likita, Bayan takira doctor yazo yadubata yabata magani tasha, yace hajiya idan bataji Dan sauqi ba atafi da ita hospital
Godia momy juwairah tayi masa yajuya yatafi

Kamar wasa taji sauqi, harma tafara hada kayanta, saboda gobe takesan komawa, momy tace haba shahida kibari kiji sauqi mana, saiki koma ko zuwa next week ne

Lalle momy Ina zan iya zama banje Naga shahid ba,
Afili kuwa saitace momy karki damu, ai naji sauqi
Momy tace Toshiknn

Kalau suka kwanta, tanata murna gobe zataje taga Shahid

1:00am ciwon nata yadawo, marar ta ta riqe har batasan tayi motsi

Haka tahanasu bacci Babu yanda momy ta’iya dole Sai asbiti suka tafi

Kamar wasa yana kwance yana bacci momy ta kirashi tafada masa halin dasuke ciki

Dasauri yasa jallabiyarsa, yahau Mota yafita, yana zuwa asbitin alokacin harta Samu bacci Bayan alluran datasha

Momy yajikin nata?
Da sauqi daddy, Abba ku yafita dazu shiyasa nakiraka, bari in shiga toilet zanyi sallah
Yace to momy

Gadon ya qarasa yana Kallanta, aransa yace marar ji kawai

Yana kallan Dakin dasuke kamar wasa yaji tana cewa Shahid…
Shahid…

Idanunta arufe da alama nafarki take, Kallanta yasake yi

Aransa yace SHAHID again?

  ***     ***     ***

After 2 week’s
Haka Zaman su Amal yakasan ce, daddy baya nemanta, itama haka
Babu wanda yake shiga sabgar dan’uwansa

Shi kullum babu fara’ah fuska a daure
Bata kula shi, ko taji motsinsa banza take dashi, saide abinda takasa ganewa shine, kullum saiya shiga Dakin dayake kusa danata

Tarasa me yake yi adakin tunda shide dakinsa asama yake

A bangaren daddy kuwa shi shaf ma yamanta da ita
Siyasar datake qara matsowa itace aransa

  ***      ***      ***

Kwalliya akeci tagani tafada, jamcy tace qawata Sai Ina haka?
Fari tayi da idonta tace Sai wajan Shahid na shahida

Zanje mufita ko shan ice cream ne

Kallan agogo tayi tace Amma shahida yanzu karfe tara fa, kina ganin zaki iya Jan hankalin sa har kuje tare?
Karki damu jamcy, tana fadar haka tadau Jakarta tafi ce

Bata zarce ko Inaba Sai gidansu Shahid
Suna falo suna kallo dukansu, tayi sallama tare da shiga falon, Nazy da okasha suka tashi suka bar musu wajan

Cikin ransa yace wannan yarinyar badai naci ba

Akusa dashi ta zauna tace um Shahid nace Dan Allah ko zaka shirya muje musha ice cream?

Kallanta yayi da mamaki baisan lokacin dayace
“shahida yaushe nafara magana dake mai tsawo dahar zan debi kafa nafita tare dake? “

Maimakon tayi fishi saitayi murmushi tace Shahid yau wacce Rana kakira sunana?

Tafe kansa yayi da hannun sa, yace Dan Allah kifita daga gidan nan, bazaki gane yanda zuciyata take zafi ba idan naganki, banasanki shahida
Akwai wadda nakeso

Hawaye ne suka wanke mata fuska, cikin kuka ta tsugunna qasa tace Shahid Ina sanka

Cikin zafi yace nikuma Bana sanki

Kafafunsa takama ta riqe, yafizge kafarsa, tareda Kai hannu zai dauketa da mari

Okasha ne yafuto Dasauri, wanda yaji suna rikici cikin daga murya, hakanne yasashi futowa

Yace haba Shahid?
Dukan mace?
Yadubi shahida yace shahida tashi ki tafi, insha Allah komai zaiyi normal kinji?
Kai ta daga masa tana goge hawayen idonta

Tana fita okasha yace abokina meyayi zafi haka?
Yarinyar nan tana sanka, koyayane kadinga kulata zataji dadi, be kamata irin haka yadinga shiga tsakanin Kuba

Okasha nafada mata banasanta, Bana Santa okasha, Yaya take so namata?
Har wannan yarinyar ce zatasa hannu tace zata riqeni?
Nawa ma take, Amma har tasan tana taba Jikin maza
Ahakan zan sota in aure ta?

Okasha ya kalleshi yace Amma na tabbatar ayanda kake bamu labarin Amal, abinda yafi riqewa ma kayi mata, shin ita Amal din muharramarka ce?
Amal da shahida duk daya suke awajanka, zaka iya auren kowa acikinsu

Amma Okasha…
Dan Allah kayi shiru Shahid, kadena kokarin dukan mace ko Yaya take Dan Allah

Shahid yana huci yashige daki, okasha bai taba yima sa fadaba Sai Akan wannan jarababbiyar yarinyar, tayaya zai sota?

  ***      ***      ***

After ten day’s

Zabe yarage saura kwana biyu, kullum daddy baya gida, dagani Sai mai gadi, haka nayi ta zagaye gidan yau ni kadai, naci abinci nakaiwa iliya mai gadi, acan nayi zamana mukasha firar mu

Hannu na ya dade da warkewa
Da yamma nayi wanka nasa Riga da sket dinkin Jan less sosai nayi kyau acikin less din, yakarbi fatar jikina, hips dina sun futo sosai, haka rigar ma Ana iya hango albarkatun qirjina

Kawai nishadi nakeji yau, kuma nakira Yaya Shahid bansameshiba, na zauna afalo na kunna kallo, kamar wasa nace ke bari de yau inga menene adakin nan da daddy yake shiga
Dakin natura nashiga, da photunan ta nafara tozali, tsayawa nayi Ina kallan Dakin, ko Ina photunan salma, kan gadon na kallah Naga Rigar baccinta akai, kenan nan yake zuwa yayita kallan pictures dinta, ya rungume rigar baccinta

To tayaya ma zai kulani,? Nan take naji wani qullulun baqin ciki araina

Aigara ni rayaiye nakeso, shikuwa Akan matacciya yakasa dubani, bai damu da cina da shana ba, kamar an ajiye masa gunki

Hararar photon nayi, afili nace Allah yaji qanki de

Computer nagani agefen gadon nasan tasace, Dan haka nadauka Nakai falo, nacire dankwali na, naci damara dashi, nakwashe pictures din duka Nakai dakina, naduba ko Ina, banbar komai nataba
Tas nakwashe komai nakaishi dakina, inata fada, ni za’a renawa hankali, nan gaba Naga inda zaka dinga shiga

Computer nadauka nahau sama, Nakai masa ita dakinsa, wannan ne Karo nafarko dana shiga Dakin, komai na Dakin red ne, Dakin yayi mugun tsaruwa kamar ba Dakin namiji ba

Akan bedside drawer na ajiye computer

Kallan Dakin naci gaba dayi, anan Naga pic dinsa babba, yasaka suit, yana daria, sosai photon yayi mugun kyau

Agefen gadonsa Naga wani Dan qarami, shikuma na salma ne, afili nace, afili nace, bacci salma, Rana kana Dakin salma, tayaya za’a kalli Amal?

Photon nadauke nasauko qasa dashi, ina Tafe Ina sababi, nasan tunda nace masa idan yaci Zabe yasakeni nasan zai sakeni, tunda naji yayi shiru, Amma Kuma mutum ma ai rahma ce, duk da zai sakeni Bayan zaben ai ko gaisawa yaci ace munayi

Amma muna zaune zama kamar Zaman gaba, inata magana ta afili Shima pic din nasake kaishi dakina
Dirin motarsa naji, Dan haka nacire dankwali na daga da marar danaci, nariqeshi ahannu na

Ribbon din kaina nacire gashin kaina yabazu har Saman kafaduna

Yarfe hannu na nafarayi me ciwon inajin Bude kofar falon, Nakai kallo na gareshi

Shima din niyake kallah, shi wallahi Yama manta da yarinyar saboda harkar Zabe dayazo kusa, mekuma yasamu hannun nata?

Kallansa tayi yayi kyau sosai cikin manyan kaya farare

Ahankali tataka taje kusa dashi tana Yarfe hannun, ta miqa masa ribbon din Hannunta red color, kalar kayan jikinta
Tace Dan dauremin gashi na, hannu na ciwo yakemin

Idanunsa masu fizgar yanmata yazuba mata, Lalle ma wannan yarinyar

Yasan cewa da Allah yabashi haihuwa da wuri shida salma da tuni sun haifeta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button