BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Amma saboda yarinta shi zata renawa hankali tace masa ciwon ta kusan 1 month har yanzu bai warkeba

Kode jitake Shima Yaron ne kamar ta?

Comments dinku yana qaramin qwarin gwiwa

Please share

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

14

Alama yayi Mata da kansa alamun ta matsa, zuba masa ido tayi ga ribbon ahannun ta, qara kawar da Kansa yayi alamun ta bashi waje, fuskar nan babu alamun wasa, tuni yayi Mata kwarjini, taja gefe guda tabashi waje
Da kallo tabishi harya haura sama,ko juyowa baiyi yasake Kallanta ba, haushi yasa tayi jifa da ribbon din Hannunta

Idanu ta zaro afili tace photunan matarsa
Ai aguje tayi dakinta, tare da kulle wa
Tafada kan gadon tana maida munfashi

Yana shiga dakinsa, yacire babbar rigarsa ya kwanta kan gadon yayi shiru yana kallan sama, daga baya yashiga toilet yayi wanka, jallabiya yasaka yasauko qasa
Dining ya kalla wayam Babu komai, wannan yarinyar Bata iya komai ba Sai shirme, antashi an aura masa wadda ko girki Bata iyaba
Juyawa yayi yashiga Dakin salma, tsayawa yayi yana kallan Dakin ganin komai yasauya

Acan Dakin Amal kuwa ta labe ajikin kofar Dakin, tana jiran sammaci, taji ya bude Dakin salma

Cikin bacin rai afili yace wannan yarinyar!!

Futowa yayi yazo Dakin ta, yatura yaji kofa gam arufe, qwanqwasawa yayi, tana jinsa tafara matsawa dabaya ahankali, sake qwanqwasawa yayi, tadaga murya tace Yaya daddy wasa nake saida safe

Kallan kofar Dakin yayi kamar ita yake kalla, tasan meta aikata ai dole ta rufe daki

Dakinsa yakoma, Idanunsa suka sauka Akan computer sa, kenan harnan tashigo, Lalle zai gamu da yarinyar nan

Computer yadauka yafara dube dube, wayarsa tadau qara dauka yayi tare da fadin jb ya akayi
Kai kuma shikkenan daga aure shiru ake jinka, wato kasamu sweet 18 ko
Girgiza kansa yayi ransa abace kamar jabeer din yana ganinsa, yace idan kasamu time kazo, katahomin da abinci a restaurant, yakashe wayar
Jb ya kalli wayar da mamaki
Shima anasa bangaren rufe computer yayi ya kwanta yafada duniyar tunani

Nikuwa kan gado nafada nasaki daria, afili nace hauka nake zan bude ka dakeni
Wayata na dauka nakira maisah, Bayan mun gaisa tacemin Ina oga, da fatan de komai lafiya?
Nace wacce lafiya maisah, nifa kinga Bama magana har yanzu, maisah zan iya cemiki tunda nazo gidan nan maganar arziqi Bata taba hadani dashiba,
Ajiyar zuciya maisah tayi, tace Anya Amal kina yiwa mijinki biyaiya kuwa?
Maisah wacce biyaiya sakinafa zaiyi

Subhanallah me kike fada haka Amal?
Shidinne da bakinsa yace zai sakeki?
To ai nafada masa idan yaci Zabe yasakeni na auri Yaya Shahid

Yasalam, Amal kanki daya kuwa? Mijinki kike cewa yasake ki Amal? Shin idan yasakeki kina tunanin baba zaiyi farin ciki da hakan ne?
Ke kanki idan yasakeki yamayar dake qaramar bazawara, ba Shahid kadai ba, a’idon kowama ke bazawara ce ba budurwa ba

Amal ki dawo hankalin ki, ki riqe aurenki dakyau, kede kifita haqqinsa, shi idan yasauke haqqinsa kansa, idan bai sauke ba yayiwa kansa

Nasan yanzu irin Dan Jan hankalin nan ma namata bakya yi Amal

Jikinane yayi sanyi dajin kalaman maisah, cikin sanyi jiki nace maisah wallahi inayi

Dazu ma haka nabashi ribbon nace masa hannu na yanamin ciwo ya daure min kaina, Amma shine ko arziqin magana bansamu ba, qarshe ma alama yayimin dakansa inmatsa tun kafin ya gabjeni

Maisah batasan lokacin datasa daria ba, tace Lalle Amal, to ai haushin dakika bashi ma kadai zaisa yakasa kulaki bare yayi miki magana, koni nan nasan ciwonki ya warke Amal, bare shi

Haka ake Jan hankalin?
Ki tashi tsaye ki gyara rayuwar aurenki Amal

Kidinga yimasa abinci, ya siyo abinci yakawo Amma saide kiyi kuci keda mai gadi
Shi ko oho
nace maisah idan nayi ma bazai ciba, tace kintaba yi ne yaqi ci?
Nayi shiru, tace yakamata de ki gyara, Dan gyaran Dakin nan, dayi masa magana ko bayaso, nide BURINAH shine inganki keda daddy Kuna shimfida soyaiya, kunyi bala’in dacewa da junanku Amal

Ina daria nace maisah soyaiya… Nide nagode Sai anjima

Ina kashe wayar, nafada duniyar tunani, maganganun maisah gaskiya ne, saide wannan mutumin kome nayi Bana tunanin zai Kalle ni, amatsayin mace, tunda tunanin matarsa bazai barshi ba, Amma Kuma aita mutu, yanzu nice matarsa, gaskya de dole insake taku

Yana kwance adakinsa, jb yashigo, ya ajiye masa take away yace na shigo inata sallama babu kowa agidan ne?

“tana nan”
Abinda yace kenan

Jb yace to meke faruwa yau din, baka samu abinda zaka ci agidan ba?
Ajiyar zuciya yasauke, yatashi daga kwanciyar dayayi, yace jb idan nakama yarinyar nan Sai jikinta yagaya mata

Subhanallah daddy meke faruwa ne?
Tashiga Dakin salma takwashe min pictures dinta gaba daya, tashigo dakina tadaukemin Wanda suke nan
Yaushe nafara wasa yarinyar nan jb?

Ajiyar zuciya jb yasaki, cikin ransa yace alhmdlh Zaman lafiya yakusa fara wanzuwa
Afili kuwa yace haba daddy kayi mana kasan fa yarinya ce
Nikuwa nasan yarinya ce jb
Dazu fa….
Saikuma yayi shiru, yaci gaba da fadin ni ban iya ko dafa shayi ba, kullum Bata bani abinci, narasa aure akamin kokuma Reno aka bani, kawai jb Bayan Zabe zan saki yarinyar nan

Dasauri jb yace Lalle daddy bakada hankali, karma kafara

Nagaji da Zaman Dakin Dan haka na futo falo domin infara gyarawa kamar yanda maisah tabani shawara, nagama shara Ina mopping naji takunsu, ina daga Kai mukai ido hudu dashi, ai aguje nayar da moper nayi daki jikake garam narufo kofar

Me jb zaiyi inba daria ba, wannan gida akwai drama

   ***      ***      ***

Washe gari Ina zaune afalo iliya mai gadi yazo yace Ana sallama Dani awaje, Dan qaramin hijabi na saka iyakarsa qirjina, ina futowa harabar gidan Naga wasu mutane su biyu, har rissinawa sukayi suka gaidani, nide nacika da mamaki, sukace ranki yadade anbamu umarni ne azo ayi Miki voters card
Araina nace ikon Allah
Nace to bissmillah, kujera iliya yadauko akayimin abuna, Babu Bata lokaci aka yi aka ciromin abina, dazasu tafi nace ku tsaya, nashiga ciki Dasauri nadauko musu ruwa da lemuka nace gashi kwasha ahanya banbaku ruwaba har zaku tafi, fuskar su dauke da fara’ah sukamin godia suka tafi
Suna fita daya yadubi dayan yace gaskya maigida yayi sa’ah, kaduba kaga yar qarama da ita Amma Babu girman Kai babu komai harda bamu abinsha, dayan yace eh gaskya wannan dole yaboyeta, kwanaki naji wasu samari suna cewa ba’a taba ganin matar daya sake aura ba

Kaikuwa me wannan dalleliyar matar Ina zai bari aganta? Dayan yace hakane Kam

Ina komawa ciki, na ajiye katin zaben Akan kujera nafada kitchen saida nasake gyara kitchen din sannan nafara girki, qamshi yacika ko ina, jallof din couscous nakeyi dayaji kayan lambu da nama, ina gamawa najera komai yanda yadace nadawo daki nayi wanka nakwanta
Wayata nadauka Ina game, in shiga nan induba nan har bacci ya daukeni
Cikin dare kamar Wanda aka tsikara natashi, naduba wayata Naga karfe uku daidai
Maganar anty mufy ce tafadomin, tsam natashi nayi toilet nadauro alwala nazo nafara gabatar da sallah, bansan ya akayi ba nide nasan na tsinci kaina dayiwa daddy addu’ah akan Allah yabashi nasara Akan zaben da zasuyi
Ban kwanta ba Sai da akayi sallar asuba, bacci na nake hani’an, har karfe goma da rabi, ina farkawa natashi Dasauri nashiga toilet domin wanka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button