BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

  ***      ***       ***

Yana shiryawa cikin manyan kaya yadi mai kyau da tsada launin light blue, wayarsa tadau qara, yana picking Abba yafara fada yana cewa Ina kuka tsayane har yanzu banga an nuna agidan TV kaje kayi zaben ba?
Kaida yakamata ace tunda wuri kunje kun dawo, tomude munje, kadau matarka kukama hanya kutafi, inkuma yanzun ma nunamin zakai bakasan siyasar ka watsamin qasa a ido Toshiknn
Saura kuma Kasa wannan qananun kayan naka kaji
Yana gama fadansa yakashe wayar
Kallan wayar daddy yayi, Wai Abba ya yakeson yayi ne? Shi wallahi baisan hayaniya, kallan kansa yayi, yace danma nasa manyan kayan de

Fita yayi daga Dakin cikin sauri, har yaje zai fita saikuma yadawo, yatura kansa cikin Dakin Amal

Alokacin tana gaban mirror tana kwalliya, kanta ko Dan kwali babu, tsayawa yayi daga bakin kofar Dakin yana Kallanta, Gaba daya tagama diriricewa, jambaki ta dauka tasaka launin ja adan qaramin bakinta, cikakken gashin girarta ta taje, tadauki mascara tana taje Zara zaran gashin idonta

Yakafeta da ido yana Kallanta, Gaba daya jikinta yayi sanyi, takasa kuzari, shigowa Dakin yayi yana zagayawa, addu’ah take aranta Allah yasa karyaga pictures din salma

Yana zagayawa har yazo saitin inda take tsaye, kallansu tayi amadubi taga yazuba mata ido, Babu um bare um um

Dasauri ta dauki ribbon dinta zata daure gashin kanta, taga ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa qirar Gucci
Yaga tana neman Bata masa lokaci Dan haka yasa hannu zai karbi ribbon din, hannunsa ta kalla duk gashi ya kwanta ajikinsa, Dasauri tasaki ribbon din

Karba yayi yadawo Bayanta har tana jiyo hucin numfashinsa, ahankali yakana gashin kanta yafara daurewa

Ido tazuba masa ta mirror tana kallan yanda yake daure gashin, fuskar sa atamke kamar tayi masa dole

Yana gamawa yayi hanyar fita
“zomu tafi”

Kamar amafarki taji maganr sa, karfin Hali tayi wajan fadin Ina zamu je?

“nace kizo muje “

Daga kafadunta tayi tace to
Mayafin doguwar rigar jikinta tayi sauri ta dauka tayi rolling, tayi mugun kyau
Tana futowa falo taga baya nan, kayanta ta kalla tasaki daria, tace yaude munyi iri daya da daddy kamar hadin baki

Tana fita harabar gidan taga yashiga Mota, Dasauri tabude gaban motar tashiga
Tashin motar yayi suka fara tafiya, sunyi Nisa kadan suna shiga jama’ah
Ya kalleta, yakawar da kansa, tissue din gaban motar yadauka ya miqa mata
Kallan tissue din tayi, Babu alamun wasa afuskar sa
Dan haka takasa tambayar sa, Tasa hannu takarba, kamar bazaiyi maganaba Sai can yace

” goge abin bakinki “

Sake kallansa tayi, ahankali ta yagi tissue din ta goge jambakin datasa
Motarsu tana dosar wajan mutane suka cika wajan danqam, yanayin parking yafuto ‘yan jarida da gidan TV suka fara daukarsa, yafara tafiya kenan, wayarsa tadau qara yana dagawa Abba yace katafi kabar yarinya abaya, daddy banasan shirme fa

Kallan sa yakai kanta, yazuba mata ido, wato daga zuwan sa har andauka Ana nuna shi agidan TV su Abba suna kallansu dayake live ne

Hannunsa yakai kan nata, ya riqe ta suka fara ratsa jama’ar wajan suna shiga, tako’ina jinake qyas qyas qaran camera

Basu bi layiba aka tantance su, sukaje aka basu ballot paper suka dangwala, idanunta Akan takardar hannunsa, duk abinda taga yayi itama shi tayi, yana gamawa jama’ah suka fara yimasa tambayoyi yana amsawa

Dakyar yasamu yafuto still hannunsu yana sarqe dana juna

Saida suka zo gab da motar sannan ya fizge nasa hannun, kallansa tayi tasakar masa harara afakaice, suka shiga Mota suka tafi

   ***       ***     ***

After one week
Sakamakon Zabe ya bayyana inda daddy yayi nasarar lashe zaben jihar, saboda jama’ah masu taya murna gidan Abba muka koma
Kasancewar momy tana cikin farin ciki ko kulani ma batayiba, saide duk inda ka duba social media pictures dinane yake yawo New first lady,, new first lady

Su baba sunkira Abba sun tayashi murna sosai shida umma

Saida komai yalafa su Momy juwairah suka koma government house, yayinda daddy yace baya buqatar Zaman gidan, saide lokaci zuwa lokaci muna zuwa
Wani lokacin kuma zai barni agida ni kadai shikuma yaje can Sai wajan dare yadawo gida saboda ayyukan dasuke gabansa
Bayan an rantsar dasu ne yafara gabatar da aiki gadan gadan tareda temakon mahaifinsa, inda yake qara dorashi Akan hanyar data dace

Doka ta farko daya fara kafawa itace duk wani Wanda zai hau machine to doka ce yasaka hular kwano akansa, saboda matsalar qwaqwalwa da ake yawan samu idan hatsarin machine yafaru
Amma idan da ita abin zaizo da sauqi

Tunda yafara gabatar da mulkinsa baya zama yau shine can gobe can, yau meeting gobe zuwa ziyara asbiti saboda ganin marasa lafiya

Yau shine Bude wannan taro gobe shine barin qasar, Gaba daya ya hauka ta jihar da ayyuka

Nikaina saina dade ban ganshi ba, haka ce taci gaba da faruwa har zuwa tsawon wani lokaci mai tsawo, saide inkira su umma ko maisah musha firar duniya kokuma Yaya Shahid yayita sakani daria hakan ne yahanani Zaman kadaici

   ***      ***       ***

Yanzu shahida menene abin damuwa Dan zaki rabu da wannan gayen?

Bazaki ganeba jamcy wallahi Ina sansa Amma yakasa fahimta ta, to tunda yakasa basai ki rabu dashiba

Toshiknn jamcy insha Allah zan gwada hakan

tunda ga lokacin shahida tadena kula Shahid, ko hakan zaisa ta manta shi, saide hakan bai samu ba asalima qara kaunar sa take
Bayan wasu watanni suka kammala karatunsu lafiya, suna karbar results dinsu alhaji sidi yaturo musu kudin jirgi

Shahid ko neman shahida baiyi ba, haka suka hau shirin tahowa nigeria shida okasha da nazy

Ko yan gida bai fadawa zaizo ba yafison yayi musu surprised

Yau suka sauka a Nigerian saida suka huta dukansu a gidansu okasha sannan Shahid yayi hanyar jigawa, nazy kuma yayi hanyar bauchi

Shahida kuka Tasa lokacin dataji labarin su Shahid sun tafi, ta kuma tabbatar Bata gaban Shahid,kuma batasan inda zata sake ganinsaba,
hakan ne ya kwantar da ita jinya, inda sukaje asbiti aka tabbatar musu dacewa tana dauke da hawan jini

Babu yanda ta iya, itama tana karbar result dinta, ta tashi hankalin jamcy Akan su hada kayansu su dawo nigeria

Daga ranar suma suka fara shirin dawowa gida

(gaskya babu abinda zance da masoyan wannan littafin nawa sai godia, Facebook fan’s da wahtsp dakowa dakowa Ina godia harda masu Bina ta privet chat, duk Ina godia tare da miqa saqon gaisuwa ta agareku)

Karku manta da

Comments
Share

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

15

Befi 2 hours ba yayi ahanya, yasauka agarin maigatari, kallan yanayin Garin yayi, an Dan same canji ba kamar bayaba, har kofar gida mai motar daya kawo shi yakai shi, kafin yashiga saida yaqarewa gidan kallo, yana Nan yanda yake komai kalau, harma sabunta fanti da akayi

Baba hamani akwai riqon alqawari bai lalata wannan gidan ba, yasan hakanne ma yahana mai gidan tashin su
Mai motar yasallama yakwashi jakunkunansa, yayi cikin gidan, da umma yafara tozali
Tana harhada kayan abincin dazata dora

Yana ganinta yazubar da jakar yatafi da gudu ya rungume ta

Umma tace Shahid? Kaine? Kaine Shahid?
Shikuwa daria ma tahanashi magana, umma ta qwalawa baba kira
Malam! Malam!! Futo ga Shahid
Baba hamani yana futowa Shahid yahadasu duka ya rungume su, Gaba daya suka rasa inda zasu saka shi Dan murna
Umma barin dora abincin tayi, suka dawo falo, aka Bude babin fira, baba yace meyasa baka fadamana zaka zoba, aida na shirya da kaina naje nadauko Amal munje har filin jirgin mun dauko ka
Cikin ransa yace baba kenan, har yanzu de yana Nan yanda yake, inba hakaba yarinya agidan mijinta kaje ka dauko ta, saboda zan dawo

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button