BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Afili yace baba ai so nake nayi muku bazata, umma tace ai Kam munga bazata, bari inje in dorama dana abinci,mekakesan ci Shahid din umma? baba ne yace dakata samiya, bar abincin nan
Yanzu zan fita naje nasiyo kaji ayi masa farfesu
Tashi kaje kayi wanka kahuta Shahid
Yana murmushi yace to baba, yatashi yayi ciki
Bayan yayi wanka yana kwance a dakinsa umma tace yataso farfesu yahadu, yace to umma ganinan, yafuto kenan zai wuce Dakin Amal kawai saiya tura yashiga, Dakin ya kalla yana Nan yanda yake, duk tarkacanta suna nan aciki, Murmushi yasaki yace Amal din baba da Yaya Shahid Ina Nan tafe inzo inganki
Yana fadar haka ya wuce falo, yaci abinci, suna zaune dukansu baba yace shahid meyasa tun farko baka fadamin gaskiyar abinda kakeji game da yar’uwarka ba?
Sosa kansa yayi yace baba ai Amal yarinya ce, nabari ne in gama karatu tukunna
Jinjina Kai baba yayi yace hakane, Amma ni banji dadin wannan shirun nakaba, Naso ka auri Amal, BURINAH inganku Koda yaushe cikin farin ciki kaida yar’uwarka
Shahid yace baba ai babu komai haka Allah yatsara ikonsa, ubangiji Allah yasa hakane yafi alkhairi
Baba da umma suka hada baki wajan fadin amin
Baba yace ai mijin nata ma kwanaki yaci Zabe, shine gwamnan Garin nasu, Shahid yace da gaske baba?
Yace wallahi kuwa, suna can bauchi suna Fama da jama’ah . shekaran jiyama mijin nata ya aiko mana da takardar fili babba acan Bayan Gari, yace zai turo afara ginawa mu koma sabon gida, baisan wannan din dama na aro neba
Cikin murna yace kai Amma ya kyauta, Allah yasaka musu da alkhairi
Allah yatayasu riqo baba, Nima idan nahuta insha Allah zansa time inje in ganta
Umma tace eh gaskya yakamata Kam
Yanzu ma bari nakira ta awaya inyi mata albishir
*** *** ***
Ina zaune afalo ni kadai duk kewa ta dameni, yau kwanana biyu rabon danasa daddy a’idona, kafin yadawo nayi bacci, shikuma idan yadawo baya nemana
Abinci idan nayi wataran yaci wataran kuma yanda na ajiye haka zanje na dauke
Yanzu ma nagama jera komai a dining table, jira nake yadawo inde beci ba to wallahi nadena wahalar da kaina Akan yi masa abinci
Wayata ce ta dauki qara, cikin shagwaba nace umma Dan Allah kizo naganki, kokuma ni nataho
Ke rufemin baki shashasha kawai, ga yayanki
Daskarewa nayi a zaune wanne yayan nawa? Mamaki nane yakatse da naji muryar Yaya Shahid adodon kunne na
Ihun murna nasa nace Yaya Shahid Dan Allah Kaine?
Wayyo Yaya yaushe kadawo? Shine Koka fadamin ko?
Shigowarsa kenan daga waje, yayi kyau sosai cikin suit me launin blue, sosai ta karbi fatar jikinsa, ya tsaya yana kallan yanda take hauka awaya
Amal kuwa waya take zuciyar ta daya, yanzu yayanah me Dame kakawomin? Daga bangaren Shahid yace zanzo da kaina inkawo miki tsarabarki, cikin zumudin murna tace
Allah yaya Shahid? Amma naji dadi sosai wallahi, I miss you muahh, tasakar masa kiss ta wayar
Gabansa ne yafadi, yayinda qirjinsa yake masa wani mugun zafi, azuciye yaje zai karbe wayar saikuma yafasa, ya haura sama
Amal tana ganin giftawar sa tace tooo yau kuma dawuri aka dawo kenan
Taci gaba da wayar ta, baba ne yakarbi wayar yace Amal din baba, tace na’am baba
Yace bawa mijin ki waya zanyi masa godia, tace godia kuma baba?
Baba yace nace kikai masa ko, ahankali ta tashi tace to baba
Saman tahau, ta tura Dakin ahankali kamar marar gaskya, yana qoqarin cire suit dinsa tashigo
Juyawa yayi, yazuba mata ido, cikin in Ina tace am, dama waya ce baba yace nabaka
Tafadi haka tare da miqa masa wayar
Sallama yayi ahankali, cikin ladabi yagaida baba, Amal ta zuba masa ido tana kallan yanda yake motsa bakinsa yana magana kamar bayaso
Godia sosai baba yayi masa, daddy aransa yace yasan aikin Abba ne wannan Dan shide beyi musu komai ba
Yana kashe wayar yajuyo yamiqa mata, takawa tayi taje gabansa zata karba ya fuzgota har saida ta tsorata tayi yar qara
Dab da fuskar ta ya matso da tashi fuskar, cikin bacin rai da daga murya yace Ina kikaimin photon matata?
Tsorata tayi da yanayin sa nan da nan jikinta yahau rawa, tace ai.. Ai de zan dauko Maka abinka ko?
Cikin ransa yace dade yafi, Dan bazaki kwashe min photunan matata ke kije kina waya da wani qato ba
Sakinta yayi tayi hanyar fita aguje, taji yace zoki dauke wannan wayar daga kusa Dani tun kafin nafasa ta
Cikin tsoro tace toka ajiye mana saina dauka
Bazaki zo ki dauka ba?
Yafadi hakan cikin fishi
Itama cikin rashin kunya tace nace Maka ma ajiye ha’a
Batai tsammani ba taga yayi Mata jifa da wayar, yashige toilet cikin qunan rai
Amal ta dubi yanda wayar tayi daidai asaman tayils din Dakin, Dasauri ta tsugunna ta kashe, ta harari kofar toilet din, aranta tace mugu kawai azzalumi
Tayi waje
*** *** ***
Tana shigowa falon, security suka fara shigo mata da kayanta
Dasauri ta rungume mahaifiyar ta, momy tace oyoyo my daughter
Shahida tace momy driver yana daukoni Naga yakawo ni nan gidan ashe hardamu aka dawo
Momy tace eh anan muke shahida ta, momy Ina Yaya daddy?
Yana gidansa, ba Koda yaushe yake zama anan ba
Meyasameki Naga wannan zuwan kin rame haka? Momy babu komai fa kawai missing dinku ne, Abba ne yashigo shahida tace abbanah
Da murnar sa yace a a kaga auta andawo gida ko,? Yaya karatun to da fatan de angama lafiya? Lafiya Abba, to Allah yabada sa’ah tace amin
Momy ta kalla tace momy zanje inyi wanka nahuta, tashi momy tayi da kanta takaita har sabon dakinta sannan ta futo
Shahida na kwanciya zazzafan zazzabi yarufeta, har dare momy taji shahida shiru taje ta tarar da ita ba lafiya, dama tasan yarinyar nan batajin dadi Amma tace Wai missing dinsu ne yasa
Babu Bata lokaci momy Tasa Abba yakira musu doctor, yana gama duba ta Abba yace doctor meyake damun tane?
Doctor yace wato alhaji gaskya yarinyar nan tana akwai abinda yake damunta, Tasa damuwa aranta har hakan ya haifar mata da hawan jini
Momy tace hawan jini doctor? Innalillahi
Abba yace subhanallah wato doctor dama yarinyar tana yawan jinya kawai Ina ganin za’a fitar da ita ko zuwa India ne Sai muga doctor acan
Doctor yace karka damu alhaji insha Allah muma nan zamuyi bakin qoqarin mu muga ta samu lafiya
Abba yace Toshiknn doctor Allah yasa
Momy ce tadau waya takira domin fadawa daddy halin da ake ciki
*** *** ***
Abinci nakeci afalo, Naga yafuto Dasauri yana waya, dagaji kasan ba lafiya ba, yace yanzu Yaya Jikin shahidan? Ok to to momy ganinan zuwa
Hannu na natsame daga cikin abincin Dasauri natashi tsaye jikina Sai rawa yake kamar Wanda akace qanwar uwatace babu lafiya nace
Yaya daddy Nima zan bika Inga Jikin nata
Har cikin ransa yaji dadi, duk da wulaqancin da yamin dazu hakan bai hanani duba yar’uwar saba
Shirun Danaga yayi ne yabani damar surar hijabi na, nabishi abaya, bamu zarce ko Inaba Sai daya gidan
Muna shiga nayi saurin shiga Dakin dayake na shahida, har bangaje daddy nake, kamar yar’uwata nafara tambayar ta shahida yajikin naki?
Ganin su Abba da daddy yasa ahankali tace da sauqi, Abba ne suka fita shida daddy da doctor, Nakai kallo na wajan momy nace momy yajikin nata?
Tace keee karna sakeji Kin kirani da wannan sunan ubanki ya radamin sunan ko wa?
Idanuna ne suka ciko da qwallah, Babu Bata lokaci hawaye suka sakko asaman fuskata, shahida ce ta motsa da qyar tace Dalla malama fice kibar mana daki, Dasauri nadago kaina na kalleta, kafin nayi magana momy tace bazaki tashi ki fice ba?