BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Adaidai lokacin daddy yashigo, harara ya zabgawa shahida, ya tsugunna dede inda nake zaune Ina kuka, hannun sa ya dora Akan kafaduna yatasheni tsaye, tare da riqo hannu na muka fice daga Dakin

Inda momy tatasa shahida agaba Akan tafada mata damuwar ta, ba tayi kokarin karya ba Nan ta shaida mata Akan Shahid ne

  ***      ***      ***

Muna tafiya amota banda kuka babu abinda nake, wannan wanne irin cin mutunci ne? Ubana?

Yanajin kukanta Amma yakasa rarrashin ta, dazata gane data dena kukan nan saboda yanda yake taba masa zuciya

Yanayin parking na futo dagudu nayi cikin dakina Ina kuka

Futowa yayi Shima yakaiwa motar duka, meyasa momy take hakane? Whay?

Nikuwa tunda nashiga daki nakwanta nake kuka, qarshema kulle kofata nayi, ko abinci ban qara waiwaitarsa ba nayi kwanciya ta

 ***     ***     ***

Next day
Da sassafe yashirya cikin manyan kaya, sai zuba qamshi yake yadin fari ya karbi fatar jikinsa, cikin takun qasaita yafuto already motoci sun zama ready Bude masa akayi, yashiga suka fita
Saida sukai Nisa sannan yafada musu inda zasuje, Dasauri suka qarasa babban shagon kayan wasa, yana futowa cikin sauri yashiga tun kafin mutane su taru
Mutum biyu ne suka take masa baya har ciki, cikin ladabi me shagon ya rissina yace yallabai me ake buqata?
Saida yayi Dan jimm sannan cikin sakin fuska yace kayan wasa zaka hadamin
To wanne iri kenan yallabai?
Haka teddy’s da babyn roba, kagane kawai kayan wasa de na mata yarinya ce zatayi amfani dasu Bata wuce 18 year’s ba haka

Me shagon yasake kallansa da mamaki gashi babu damar tambaya, cikin ransa yace ikon Allah 18 years fa

Hada musu kayan yayi me mugun yawa Dan teddy’s kadai ma kusan guda hudu Akasa manya

Daya daga cikin masu take masa bayane yabada ATM aka cire kudin suka futo daga shagon

Ina zaune afalo Naga anfara shigowa da kayan wasa, da mamaki Nakai dubana kansu, cikin Raina yace to wannan kuma kosu junior ne suka zo?
Bangama mamaki naba, Naga yashigo, kallansa nake Shima niyake kallo, rabona dashi tun jiya
Kusa Dani yazo ya tsaya ya nunamin kayan wasan yace

“gashinan kidinga wasa nasan zasu debe miki kewa idan Bana nan “

Amal batasan lokacin datasa daria ba, Lalle ma daddy yarasa wazai siyowa wannan kayan saini? Shekara goma Sha tara? Daria taci gaba dayi sosai, tana daga teddy’s din

Ya shagala a kallan ta, ashe tana daria haka? Ikon Allah, yasan wannan dariyar duk saboda an siyo mata kayan wasa ne, Allah Sarki andade ba’a hadu ba
Taga kayan wasa, shida yasan tana San kayan wasan aida tuni yabada order akawo mata, kodan ta dena damunsa

Koda yake ai kwanaki ma Tataba fada masa tana wasa

Cikin daria tace nagode, tafara jidarsu tanayin dakinta dasu, gaskya wannan mutumin ya mugun Rena mata hankali

Saida tashiga daki sannan yajuya yakoma dakinsa

 ***     ***     ***

After one week
Shahid kakaiwa Amal kayan miyar nan nasan zata dinga amfani dasu, wannan kuma umma ta nuna masa wata jarka, da tsumi aciki na maganin mata
Tace kafada mata ta dinga Sha kullum kafin ta kwanta da daddare
Kallan jarkar yayi, yace umma menene aciki?
Tace banasan tambaya Shahid, tashi katafi Allah ya kiyaye hanya, Murmushi yayi yace to umma na bye bye

Yana sauka a bauchi, directly gidansu nazy yatafi, saida yahuta, sannan yakira Amal Yace tayi masa kwatancen gidan nata gashi yazo

Murna acikin Amal tace Yayanah kawai kace akawo ka government house munzo tun jiya muna nan, ok kawai yace yakashe wayar

Shida nazy suka tafi, Akan machine din nazy roba roba mai kyau, dayake nazy Dan Garin ne basu Sha wahala ba Kai tsaye suka nufi gidan
Bayin Allah basu San ansa dokar saka hular kwano ba, kasancewar suna Indonesia lokacin dayahau
Suna Zuwa gate din gidan, security suka musu kallan banza suka watsar

Shahid ne yasauko yayi masifar kyau cikin qananun kaya wandon blue jeans, da rigar ciki fara, sai yar sama ya dora kalar jeans din

Hannu yamiqawa daya daga cikin su yayi masa bayani yazo wajan qanwar sane, security din yadubeshi yace Dan samari ka matsa daga kusa Dani tun kafin bindigar hannu na tafara aiki
Shahid yace subhanallah me yayi zafi haka?
In banda renin wayo ansa doka agari kun karya, sannan kazo Wai abarka kashiga ciki

Nazy ne ya taso yace dalla malamai idan bazaku barmu mushiga ba miye na fadar magana?
Aikuwa nan hayaniya ta kaure tsakanin su
Su sukace saisun shiga security kuma suka hanasu

Yana daga dakinsa yaji hayaniya ta window yaleqa, yaga abinda yake faruwa nan yatashi yafuto da kansa, Amal ma takira Shahid yace Mata yana gate anhanashi shiga, Dan haka tafuto domin tayi musu magana

Shahida kuwa da aka tasheta a bacci cikin masifa tafuto falon

Alokacin har daddy yabada umarni abarsu su shigo gidan yaga su waye, kuma me suke nema?

Shahid kuwa yana shiga, aka nuna musu hanyar falon, iya tsaruwa gaskya gidan ya tsaru, Tako’ina sojoji ne atsaye

Yana shiga falon Amal tataso da gudu ta rungume shi tana cewa yeeee ga Yaya Shahid

Daskarewa daddy yayi atsaye, cikin ransa ya maimaita SHAHID

Janyeta yayi daga jikinsa yadago ta kenan Idanunsa yasauka Akan na shahida, yayinda nazy yacika da mamaki meya kawo shahida nan?

Dagudu Takoma daki tana kuka tana fasa kayan Dakin, komai ta Zara jifa take dashi, tana kuka

wayyo momy nashiga uku na lalace

Momy tafuto Dasauri tayi Dakin shahida tana tambayar ta menene?

Cikin kuka tace momy nashiga uku na kashe kaina!!!

Kar amanta da:

Comments
Share

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

16

Subhanallah me kike fada hakane shahida? Kiyimin bayani yanda zan gane
Momy Shahid… Shahid..
Me Shahid din yayi?
Momy Shahid yayan Amal ne, wallahi yayanta ne, gasucan afalo

Innalillahi, cikin sanyin jiki momy tace yi hakuri yi shiru, ina zuwa, goge hawayenki
Tashi ki gyara fuskarki, shahida na shiga toilet momy ta rafka tagumi da wanne ido zata kalli yarinyar nan?

Acan falo kuwa Amal ta rirriqe Shahid ahankali yace Mata bari mana, hannu ya miqawa daddy dayake tsaye yana kallansu fuskar sa babu fara’ah, Ba yabo ba fallasa yabashi hannun suka gaisa, kujera ya nuna musu yadan saki fuskar Tasa, yace Bismillah ku zauna mana
Suna zama yayi ciki,domin yafadawa momy, nazy ya kalli Shahid fuskar sa fal tambayoyi

Yana kokarin tura kofar Dakin yaji momy nacewa yauwa goge fuskar ki dakyau, kuma karki sake kuka bare yarenaki, cikin shagwaba tace to momy kome nayi Shahid bazai Soni ba, momy inaga San Shahid shine ajalina

Dasauri daddy yayi baya, dama… Kenan wannan Yaron shine yar’uwarsa take mafarki? To’ina tasanshi?
Iska me zafi ya furzar, matarsa Nason Shahid
Qanwarsa Nason Shahid, shikuwa me zaiyiwa wannan Yaron?

Abinma be tsaya iya shahida ba, harda aurensa? Bawai yanajin son yarinyar bane, Gaba dayama gani yake ya haifeta, to Amma bazai bari aci mutunci aurensa ba, yanayin komai ne saboda yakare darajar aurensa

Tsaki yasaki, aransa yace to mene ma zai dameni?
Alamun Bude kofa yaji Dasauri ya kalli wajan, Murmushi yasaki ganin momy tafuto
Da mamaki ta kalleshi, tace daddy nah, me kakeyi anan?
Cikin murmushi yace momy wannan yarinyar tayi Baqi ne shine zan fada Miki

Da fara’ah momy tace aaa to muje, muje mana, tayi gaba ta barshi abaya
Momy tana zuwa falon su Shahid suka gaida ta da fara’ah har qasa

Idanu ta zubawa Shahid, Yaron yanada kyau, dole ya haukatar mata da yarinya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button