BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Rayuwarsu tana tafiya normal basuda matsalar komai, face rashin haihuwar karaam (dady) dayake damun su

Back to story

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

2
Nahiyar Niger
Yankin zinder wato damagaram nada girman murabba’in kilo mita 145,430,kuma kidayar da akayi a shekara ta 2001 ta nuna yawan yawan jama’ar Yankin sun Kai 2,080,250.
Kabilun dake zaune a damagaram sun hada da hausawa, fulani, larabawa da kuma abzinawa har zuwa shekara ta 1926 birnin zinder ne babban birnin Niger
Yawancin tattalin arziqin Yankin damagaram ya dogara ne Akan noma da kiwo dakuma kasuwanci
Yankin zinder na makwabtaka da wasu jihohin nigeria, kamar jihar jigawa ta kudu, sai jihar katsina ta kudu maso yamma
Acikin gida kuwa Yankin zinder na iyaka da agadez ta Arewaci da diffa ta gabashi da maradi ta yammaci

Malam Hamani danda daga wannan Yankin yake, matarsa daya mai suna Samia, Allah ya hore masa ilimi ta fanni daban daban, har hakan yasa yaransa suma suka koyi wani Abu daga cikin ilminsa, yagaji ilmi tun daga kakanni, dagashi sai dan’uwansa ibrahima Wanda Allah yayi masa cikawa tun bai dade da aure ba

Bayan iyayensa sun rasu ne, yatattara komai nasa,yahada kan yaransa sukayi qaura suka dawo nigeria da zama

Inde magani kake nema, basai nafadaba, kasan mutanan Niger suna da wannan baiwar

Cikakken bafulatanine na damagaram

Garin jigawa, qaramar hukumar maigatari, unguwar kofar fada, acan Bayan Gari sunada gidaje sababbi, cikinsu harda wani qerarran gidan wani dansanda dayake zaune a Abuja
Anan Malam Hamani yayi yasauka
Suna zaune lafiya shida iyalansa, haka kuma Koda yaushe gidan ba’a rabashi da mutane, masu siyan magani
Cikakken Hervarlist ne, haka kuma yanada Islamic chemist
Wanda dansa yake kula dashi

Yaransa biyu rak a duniya, Shahid da kuma Amal

Malam Hamani yana San yaransa, baya kaunar abinda zai taba lafiyarsu, yanzun nan zai zari takalmin sa yaje har gida yaci ma mutunci yadawo
Sabanin matarsa Samia datake da sanyin Hali

Shahid hadadden gaye ne na karshe, fari ne tass, yanada cikar gashin gira, hancinsa Dan daidai, bakinsa mai kyau, mai karatu duk yanda zan fasalta muku Shahid bazaku ganeba, Amma zaku fahinceni idan kukai tozali da pic dinsa abangon littafi na

Yanada fara’ah ga yar’uwarsa Amal, Amma inka dauketa da wahala kaga yasaki jiki da mutum awaje
Shaquwace ta gaske atsakanin su

Sosai yanada magana, Amma fa idan yaso, rashin karfin mahaifinsu ne yasa sauran kyansa rashin futowa

Amal kyakkyawar yarinya, yar lelen yayanta tare da babanta, ba siririya bace, ba kuma me irin qibar Nan bace
A a dede misali ne, jikinta amurje yake, batada wata alamar yunwa

Allah yayi Mata sura mai kyau da daukar hankali, akwai diri ajikin Amal, hips dinta abaje yake, yayinda boobs dinta suke madaidaita a tsaye

Kowanne irin kaya tasa kyau take, farace tass, Babu alamar quraje ko tabo ajikinta
Gashin kanta kuwa dogo ne sosai, mai shegen santsi, da cika, Amal kenan

Akan kataba Amal gara kaje kaciwa Malam Hamani mutunci, yaqi jinin ataba masa ita, yana kaunarta sosai

Kwata kwata shekarun ta basu wuce 19 year’s ba

 ***     ***     ***

Tana zaune a qayataccen falon nasu, atamfa ce ajikinta Holland mai tsadar gaske, lemuka ne agabanta tana Sha tana kallan labarai

Abba ne yashigo, jama’ah suna take masa baya, saida suka rakoshi cikin falon sannan suka juya

Zama yayi tare da kallan hajia juwairah, uwargida sarautar mata, kede Koda yaushe bakya rabo da kwalliya

Murmushi tasaki Wanda da gani kasan taji dadin maganar tasa har cikin ranta

Alhaji ai Kaine sirrin
Murmushi yasaki yace Allah ko

Batare datace komai ba,tace yanzu de sannu da zuwa, yakamata muje kayi wanka ka shirya Kasa wani Abu acikinka

Lemon dake gabanta yadauka yace a a aqoshe nake , wannan kwalliyar kadai ma aini ta wadatar Dani

Alhaji kaide bakada dama wallahi, Koda yaushe cikin zolaya kake

A a to kinga laifi na dannayi wasa da iyali na? Tace a a

Yace yauwa namanta ban fadamiki ba, nasa abincika min maganin wannan Yaron, agwada ko za’a dace

Fuskarta ce tabayyanar da fara’ah, tace to alhaji Allah yasa adace, tunda anyi na asbiti babu cigaba ai gara akoma na Islamic din

Lemon hannun sa ya ajiye yace hakane Kam hajiyata

Gaba dayansu sukasa daria, domin kuwa maganar Tasa, tabata daria

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

3

Dukanta yake da dorinar datake hannun sa, tana tsugunne idanunta jajir saboda tsabar kukan datasha, bazaki fadamin dalili ba?
To ita Wai meyakeso tace masa?
Cigaba yayi da dukanta har hakan yayi sanadiyar ficewar niqab din dake Fuskarta

Ido yazuba mata, saboda shi harga Allah kawai de yana ganinta tana zuwa school dinne, Amma baitaba ganin Fuskarta ba, saboda Koda yaushe tana cikin niqab

Jikinsa ne yayi sanyi, lokacin daya dakata da dukanta

Batace masa komai ba tamiqe tana goge idanunta da niqab din hannun ta

Borin kunya ne yasashi cigaba da fada gudun kada sauran dalibai su fahimci halin daya shiga

Da dorinar hannun sa yake nunata yace kiqara yi mana acuci maza kiga irin hukuncin dazan sake yimiki
Dan iskanci yara Dan kunga kun girma shine ba’a isa afada muku kuji ba, acuci maza do kace Awannan makarantar idan mutum bazai iya kiyaye wa ba, to karya sake dawowa
Yana gama fadar haka yajuya yabar cikin ajin
Malam nura kenan

Dasauri Rumaisa tazo ta rungume ta, tana goge mata hawayen idonta
Itama idanunta sun ciko da qwalla, tace
Kiyi hakuri Amal, kinsan Malam nura baida mutunci
Cikin sheshshekar kuka nace to Rumaisa yayakeso nayi? Gashin kaina yake so na aske kokuma so yake na Bude kaina yagani
Ki yi hakuri Amal, zomuje mu zauna

Suna zama malama tashigo suka fara daukar karatu, dayake islamiya ce ta yamma, basu wani dau lokaci ba aka tashesu
Suna tafiya ahanya Rumaisa tana qara Bata hakuri Akan abinda Malam nura yayi Mata, tace Dan Allah karki bari baba hamani yaji
Amal tace karki damu Rumaisa nayi miki alqawari
Dahaka suka rabu kowa yayi gida
Tana shiga gida da sallama tayi dakinta, umma da Shahid suna zaune a tsakar gida, dayaga zata shige daki nan da nan yafara tsokanarta kamar yanda yasaba
Amalun aiki!
Dasauri ta juyo cikin sigar shagwaba tace umma kin ganshi ko?
Kawai sai Tasa kuka, basusan dama akusa take ba
Ba umma kadai ba hatta Shahid saida jikinsa yayi sanyi, saboda yasan cewa ba wannan ne Karo nafarko dayake tsokanarta ba, tunda tariga da tasan bahaka sunan nata yake nufi ba ko kula shi batayi
Amma yau abin harda kuka

Littafin hannun sa ya ajiye yaqaraso wajan ta, har sunajin numfashin juna
Yakama hannun ta yace keda waye?
Tace ni Yaya ba komai,
Tsareta yayi da idanunsa, cikin rashin wasa yace nace miki keda waye?
Kyaleshi tayi tashige falonsu
Shima binta yayi da kallo, tare da take mata baya

Zama yayi Akan kujera ya shareta, ganin ya shareta ne yasa tataso ahankali tafada jikinsa tasaki kuka
Yanajin ta ya shareta
Saita yaga kukan nata sosai takeyinsa alamar tana tare da damuwa hakan ne yabashi damar rungume ta ajikinsa

Umma tana daga waje tana kallansu batace komai ba kawai de ta girgiza kanta

“keda waye? “
Abinda yace kenan
Cikin hawaye tabashi labarin Malam nura

Dasauri Yakama hijab dinta yacire aikuwa farar fatarta ce ta nuna shedar dukan datasha

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button