BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Momy tace hakane, saikuma magana ta biyu, alhaji, nifa nafara damuwa da yaran nan, Amal da daddy, har yanzu babu wani labari, shiru

Abba yasa dariyar su ta manya, yace to hajiya ya za’a musu, shi yanzu daka tabashi Akan batun haihuwa zai sunkuyar dakai yace yana bakin qoqarinsa

Momy tace a a alhaji ayi musu wani Abu de, ko Yaya ne, Abba yace Toshiknn hajiyata zansan abinyi
Dukansu sukasa daria

   ***      ***       ***

Yana zaune ya hakimce a office dinsa, office din yatsaru mutuqa, manyan kaya ne ajikinsa, kalar milk, agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa qirar Rolex sosai yayi kyau, daga bayansa tutar nigeria ce guda biyu manya,
Saikuma guda biyu qanana akafe agaban tebir din dake gabansa,

Deputy n sane yake masa jawabi Akan wasu takardu, ranka ya dade wannan takardar dazaka saka hannu ne Akan kudin daka ware domin akaiwa dukkanin copper’s din jihar bauchi da aka turasu camp domin atallafa musu

Sai wannan kuma signing suke buqata naka saboda suna so zasu Bude gidan mai a qauyen DASS
Gasucan guda uku, wannan agarin SHIRA wannan kuma JAMA’ARE

Dauka yayi dukansu yasa hannu, yaware guda daya aciki, yace wannan ta jama’aren nags dede wajan kamar za’a shiga cikin gonakin talakawa so bazamu saka masa hannu ba

Rissinawa yayi yace ranka ya dade Allah yatemakeka

Kallansa yasakeyi yace motoci sun zama ready ne?
Sun zama ready sir
Yace to Ina ganin yau zamu kaiwa Garin GAMAWA da GIADE dakuma KIRFI ziyara

OK sir

Babu Bata lokaci suka shiga motoci suka tafi, domin Jin korafe korafen talakawan dake qarqashin mulkinsa

  ***      ***      ***

After one week
Suna zaune a dining dukansu suna break fast, Amal, Abba, daddy, shahida, momy
Bakajin maganar kowa Sai qaran spoon dayake tashi
Shahida tace anty Amal, yaude yakamata mufita dake Garin nan kema ki duba talakawan dasuke qarqashin ku
Amal Jin maganar tayi banbara Kwai, Wai anty Amal,
Murmushin yaqe kawai tayi
Momy tace rabu da ita yata Amal, kici abinci kinji?

Daddy yazuba mata ido yanaso yaga yanayin ta

Abba ne yatashi yana goge bakinsa da tissue yadubi daddy yace to Kai idan kun gama Ina jiranku amota kaida Amal, akwai inda zamuje

Atare suka kalli juna, saikuma suka kalli abban, tsam yatashi yabi Bayan Abba, itama Dasauri ta tashi tadau mayafinta suka fita

Basu zarce ko’inaba Sai asbiti, suna Zuwa doctor ya karbesu dayake yasan da zuwansu, Amal tarasa dalilin zuwansu hakama daddy

Abba yadubi doctor, yace gasunan likita, adubamin su koba kalau suke ba, aure kusan wata shida Amma Babu ko batan wata basu taba yiba

Ba Amal kadai ba, hatta daddy saida gabansa yafadi, cikin sauri ta sunkuyar da kanta, shi kansa doctor din mamaki ne daria suka kamashi

Kai iyaye Sai hakuri,sude Koda yaushe ganin yayansu suke yara awajansu
Amma inba hakaba govnor guda asakoshi agaba haka Kamar qanqanin yaro

Dan haka yatashi yace yadubi Amal Yace ranki yadade zaki kwanta anan muyi scanning muga menene matsalar

Dago kansa yayi yacewa doctor din “am Ina ganin kawai kahadata da mace”

Abba ne ya kalleshi cikin ransa yace shegen kishi

Doctor din yace to ranka yadade, Babu dadewa yahadata da mace ta dubata, Shima aka dubashi aka tabbatar musu dacewa kalau suke kawai lokaci ne baiyi ba, anan yamai godia suka juya Mota, suna shiga Mota Amal tahada ido da daddy, atare suka kawar da kansu daga kallan juna

Suna komawa gida daddy yafada duniyar tunani waida mulkin da aka liqa masa zaiji Koda mace?
Amma zaiyi amfani da wannan damar wajan ganin ya zauna agida yahuta kamar da batare dayafita ko’inaba

  ***      ***     ***

After 2 week’s
Su daddy sun koma gidansu, yashirya yazo gida, yasamu Abba afalo, suna zaune da momy
Ya tsugunna har qasa ya gaida su, saikuma yayi shiru, Abba yace daddy nah meyake faruwa ne?

Naga alama bakin ka akwai magana, daddy yace Abba dama… Am dama Abba inasan bada riqon qwarya ne
Abba ya kalleshi da mamaki yace but why?

Daddy yace Abba ni dama wannan mulkin baya barina insake da iyali na ne

Abba dayaji haka Sai yayi tunanin ko a nasan samar musu da jika ne

Dan haka Kai tsaye cikin murmushi yace to alhmdlh ai Ina ganin saiku tafi ko Germany ne kuhuta ko, ai yafi ace za’a bada mulki riqon qwarya ko Malam karaam, saikuje kuhuta nadan lokaci ku dawo

Innalillahi… Shifa yafadi hakane Dan a barshi yahuta kamar yanda yake Ada

Abba yace tashi kaje, saika shirya kadauki matarka zuwa jibi ku wuce, Allah ya kiyaye hanya yatsare

Acan qasan muryar sa yace “Amin”

Yana fita directly office ya wuce yagama rubuce rubucensa inda yadauki hutun taqaicaccan lokaci na Tsawon wata daya, zaije qasar Germany domin aduba lafiyar sa

Babu Bata lokaci labari ya watsu zuwa dare har anfara sanarwa akafafen Yada labarai cewa maigirma governor zaije ganin likita zuwa qasar Germany

  ***      ***      ***

Tana zaune afalo tatasa TV agaba tana kallo, gajiya tayi da kallan harzata kashe taje ta kwanta, saitaga Ana sanarwa maigirma governor zuwa jibi zaije qasar Germany domin duba lafiyar sa
Inda zai dauki tsawon wata daya kafin yadawo, al’amarin daya daga hankalin masoyan sa, inda suke masa fatan samun lafiya

Tana gama Jin labaran ta kwashe da daria, afili tace maqaryatan banza, Wai Germany
Ko waye ba lafiyar oho

Daria tasake saki tace wallahi suzo wajena su samu labari, bawani Germany dazaije, yana Nan agida rass yake

Motsin dataji abayanta ne yasa cikin sauri tajuya, gabanta ne yafadi lokacin datai ido biyu da daddy atsaye

(masoyana masoyan wannan novel, ina mai Baku hakurin rashin typing din dabanyiba Daren jiya, hakan yafaru ne Sanadin rashin charge da banda shi, Amma inaso kusani yanda kukai ta tunanin BURINAH jiya haka Nima naita tunanin ku, nagode)

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

17

Cikin ranta tace shikkenan namutu
Miqewa tayi tana karkade jikinta kamar Wanda ta zauna acikin qasa,tana tafiya da baya da baya
Takowa yakeyi yana kusantota, tanayin baya yana sake matso ta, har sukaje Jikin bangon falon
Yasa hannu yadafa bangon yazuba mata ido fuskar sa babu alamar wasa
Itama zuba masa ido tayi, ganin fuskar su dab data juna kamar Wanda zaiyi kissing dinta
Nan da nan tafara zare ido

“me kikace? “
” naji kamar kina magana “
Girgiza kanta tayi, yayinda idanunta suka Raina fata, cikin tsoro tace a a badakai nakeba, wallahi wani film na kalla

Kallan kin renamin wayo yayi Mata ya nunata da hannun sa yace idan kika sake qaryatani saina tsinka miki mari

Ayanda taga qwayar idonsa tsaf zai iya Marin nata Dan haka tayi sauri ta tsugunna ta qasansa tayi wuf tashige dakinta ta datse kofar
Kan gado tafada tana maida numfashi, yayinda murmushi ya wanzu asaman Fuskarta

Murmushin sa ta tuna na jiya, yanayin Zaman su, yanda yake magana cikin aji da soyaiya

“kinata surutu baki kawo musu ruwaba?

Juya manyan idanunta tayi, data tuna abinda yafaru tsakanin su yanzu

” me kikace? “
Tatuna da maganar sa, lumshe idanunta tayi, ta Bude, afili tace lips dinsa mai kyau pink dashi Dan qarami

Fuskarta ce ta sauya data gama tunanin, ganin ita kadai take haukan ta, tashi tayi tashiga toilet domin watsa ruwa, saboda zafin da akeyi agarin
Tana futowa tasaka rigar bacci acikin rigunan aurenta, baqa ce, Gaba daya tsawon rigar iyakarsa gwiwarta, gashin ta data wanke tazo takama ta taje, ta shafa mayuka masu mutuqar qamshi
Ta daure shi ta kwanta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button