BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar wasa cikin baccinta taji iska me karfi natashi, Windows din Dakin Sai budewa suke suna rufewa, tashi tayi taleqa taga Gari yahadu da hadari
Tayi sauri taja windows din ta rufe, Takoma ta kwanta
Wata gigitacciyar tsawa akayi dayasa Amal sakin ihun dabata shiryaba
Ta takure awaje daya, alokacin daddy yana falo, Babu ruwa a fridge din Dakin
Yafuto zaisha ruwa yaji Qarar ta, kamar zai share ta saikuma yatunkari kofar Dakin
Ahankali yatura kofar Dakin yashiga, ya tsaya daga bakin kofar yana kallan yanda ta takure waje daya tana kuka
Rigar bacci ne ajikinsa fara qal me madauri daga cikinsa, Samanta kuma abude take, hakan ne yabaiyanar lallausan baqin gashin daya kwanta a faffadan kirjinsa
“me kike yi haka? “
Tana Jin muryar sa, tadago da kanta ta ganshi, Dasauri taje tafada jikinsa tana cigaba da kuka
Binta yayi da kallo yanda ta rirriqeshi, kallan rigar baccin dake jikinta yayi, anan yayi ido biyu da madedetan nashanunta, dasuke acike atsaye, bulbul dasu farare
Maganar tace tadawo dashi daga kallan daya Lula, cikin kuka tace ni Yaya daddy tsoro nakeji, Allah bazan iya kwana ba
Still Kallanta yake yakasa magana, haka kuma yakasa rungume ta da hannayensa
Tuno jiya yayi yanda ta rirriqe Shahid kamar wani mijinta
Wani haushi yataso masa, nan da nan yafinciketa daga jikinsa
Kan gadon ya nuna mata yace “kwanta”
Girgiza Kai tayi tace ni tsoro nakeji
“nace ki kwanta “
Ganin bayasan musu yasa taje kan gadon ta kwanta, ta maqure awaje daya
Kujerar dake gefe yanema ya zauna, yana aikin Kallanta
Ita kuwa tana runtse ido, kuma ga daddy tana gani a gefe, hakan yasa ta janyo teddy bear dinta guda daya ta rungume shi, tayi shiru ta nutsu har bacci yadauketa
Ahankali yatashi yaje kanta yatsaya yana Kallanta
Wani irin yanayi daya dade rabonsa dashi yana fizgar sa
Ganin tayi bacci yasa yakashe wutar Dakin, yarage karfin esi, sannan yaja kofar ahankali gudun kada ta tashi, yafice yayi dakinsa
Yana kwnciya yayi addu’ah, ya runtse idonsa domin bacci, saide me, yana rufe ido itan de yake gani
Yanayin su na dazu yatuna, tsoron daya gani atare da itane yafi birgeshi,murmushin dabai shirya bane ya qwace masa
Wata zuciyar tace Kai karaam shiga taitayinka, wannan yarinyar babu kowa acikin ranta banda yayanta
Fuskarsa ce Takoma yanda take Ada,Babu walwala
Yajuya ya gyara kwanciyarsa, yana tunanin to mema yakai shi Dakin?
Fillon gefensa yadauka yayi wulli dashi, yayi DANA SANI yafi aqirga
Daga baya bacci yadaushi
*** *** ***
Washe gari Amal daqyar tatashi saboda yanda baccin yayi Mata dadi, tana idar da sallar asuba, tadau alqur’ani tana karantawa, har Gari yayi haske
Window ta Bude taga yanayin Gari
Taga yana Nan baqiqqirin da hadari
Rufewa tayi, ta dauke alqur’anin data karanta, tafuto tahada musu break fast
Shayi ta zuba ta gabza Uwar madara, tayi dakinta, tana gama shan shayin tayi wanka, tasaka doguwar rigar material
Kanta babu dankwali kamar kullum tafuto falon ta zauna
Yayyafi aka fara, daga nan ruwa ya zuge ake zubashi kamar da bakin qwarya
Fita tayi harabar gidan, tafara wanka cikin ruwan Saman da ake
Kamar a mafarki yakejin daria na tashi, gashi Ana ruwan sama, tashi yayi yabude window din dakinsa, dayake asama yake, can yahango Amal tana wanka tana zuba daria acikin ruwa, sai juyawa take, gashin kanta daya jiqe yana sake dawowa yarufe mata fuska
Tana janyeshi tana cigaba da wankanta
Besan adadin lokacin daya dauka yana Kallanta ba, labulan yasaki tareda rufe window yace “kanki idan kika hadu da jinya”
Amal kuwa Bata dawo ciki ba saida tagama wanka ta tsaf, tadawo ta cire kayan jikinta, ta sauya wani ta kwanta tana game awayar ta
Dan babu komai acikin wayar banda game
*** *** ***
Washe gari karfe goma nasafe, yashirya cikin baqin yadi, kalar kayan ta karbi jikinsa, hasken fatarsa yafuto acikin yadin
Agogon hannun sa ya kalla qirar plaget, ya furzar da Iska me zafi, saura awa daya jirgin su yatashi, gashi wannan yarinyar ko futowa batayiba
Shikuma bazai shiga dakinta yagano wa kansa abinda zaizo yadameshi ba
Goma da kwata, nayi aka fara kiransa, masu jiransa ne Wanda zasu rakashi airport
Ganin zai batawa kansa lokaci yasa yasa yatura kofar Dakin ahankali, ganinta yayi tana kwance hankalinta kwance Sai sharar baccinta take
Teddy din dake gefenta yadauko ya zungureta dashi, ahankali take Bude idonta, harta budeshi gaba daya tareda wata irin miqa
Innalillahi, yafadi haka aransa yajuya mata baya, yace ki tashi ki shirya ki dauki kayanki zamuyi tafiya
Yana fada Mata haka yajuya yafita
Dakinsa ya koma ya zauna agefen gado tare da cire hularsa ya ajiye a gefe
Dama abinda yake gudu kenan, gashi kuma yafaru
Amal kuwa tana gama wanka ta duba kayan dazata saka, Murmushi tasaki ta janyo baqar abaya me adon stone ajikinta tasaka, tace yauma iri daya zamuyi Yaya daddy
Da dankwalin abayar tayi rolling, tayi farkin gashin ta, Tasa red din janbaki sosai tayi kyau, kasan farin mutum da Jan janbaki, nan da nan ta haska, shafe dinta yafuto sosai acikin rigar, kayanta tasaka Dasauri acikin trolley
Ta janyo Jakarta zuwa falo
Wayam taga bayanan, harabar gidan ta leqa still be futo ba, Dan haka tabishi dakinsa
Tana zuwa taganshi a zaune ga qaramar trolley agabansa yana kokarin rufewa Amma taqi rufuwa
Motsin ta yaji yadago kansa ya kalleta, Kasa janye Idanunsa yayi akanta, Murmushi tasakar masa, tatako ahankali har zuwa gabansa
Tsugunna wa tayi dab dashi, sai a sannan ya janye Idanunsa akanta, Gaba daya qamshin turaren data fesa yacika masa hanci, Hannunta ta miqa tace
“kozan iya temaka ma?”
Fuskarsa ahade yasakar mata jakar, ita kuwa duk ta cire kayaiyakin ciki, tayi mamaki sosai ganin gaba daya qananan kaya yadiba, aranta tace shida baya saka qananun kaya da yawa, yau shine duk ya jidesu
Daya Bayan daya take nade kayan tana maida wa cikin trolley din, aranta tana cewa ita jakar mahaukaciyar inace zata rufu Bayan an tula mata kaya ko ninkin arziqi babu
Kallanta yake sosai, harta gama, ‘yar qanqanuwar yarinya da ita, Amma ta iya wannan aiki
Jakar ta janyo tace masa Toni nafita
Abaya ya biyoba, suna Zuwa falo ya karbi jakarsa itama ta janyo Tata trolley din
Sunzo fita daga falon kenan yasake dubanta, yace
“ina wannan abin naki?”
Fari tayi da idonta, tace wanne Abu?
Babu alamar wasa afuskar sa yace “ina nufin wannan baqin abun dakike sakawa a face dinki”
Da mamaki ta kalleshi tace, au Wai niqab kake nufi?
Be Bata amsaba, sai kansa daya jijjiga mata
Juyawa tayi ciki, Dasauri ta dauko shi, agabansa ta daura sannan suka fita
Baqar Mota suka shiga qirar Range Rover, driver zai fice daga gidan kenan ya dakatar dashi, ya leqa ta window yace iliya, daga yau kadena aiki anan, ka koma can daya gidan kasanar dasu cewa nace subaka aiki kowanne iri ne
Cikin ladabi yace to ranka ya dade
Sunyi Nisa ahanya ta dage niqab dinta ta fuskanceshi tace to kuma waye zaina Bude gate din?
Kallanta yayi yace “duk mutumin daya zabi nunawa masu gadi jikinsa ai dole zaizo yaci gaba da aikin masu gadi”
Tanajin wannan furucin nasa tasan cewa da’ita yake, Dan haka taja Bakinta tayi shiru, niqab dinta ta maida tadinga hararar sa
Suna sauka a Airport jama’ah suka cika wajan, Amal na gefe taji andafa ta, tana dubawa taga shahida ce
Shahida tace anty Amal zuwa nayi Inga tafiyar ku, Dan Allah idan kunje nide karki manta da tsaraba ta nida Shahid nida dina