BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haushi ne yasa Amal ture hannun ta daga jikinta, duk abinda suke daddy yana kallansu

Ana sanarwa zasu iya shiga jirgi, yayi sallama da mutane, Amal ko kallan shahida batayiba taja Jakarta tayi ciki

Wajan daddy shahida ta nufa tace Yaya daddy saikun dawo, da tsadaddan murmushin sa yace Mata to a kula de banasan yawace yawace fa qawaye, tace to Yaya bye bye

Juyawa yayi wajan Amal, suka shiga cikin Sir Abubakar Tafawa Balewa International Airport Bauchi, inda sukabi jirgin Emirates zuwa Germany

  ***        ***      ***

Saukar dare sukayi, Amal Sai Kalle Kalle take da mamaki, ashe de da gaske yake tafiyar zaiyi, Allah Sarki hartake qaryatawa

Basu zarce ko’Inaba Sai hadaddan Hotel din nan naqasar Germany wato Berlin
Tana bayansa a reception yagama musu komai, daki daya suka kama
Suna Zuwa Dakin ta zauna jagwab,Akan kujera saboda gajiya

Shikuwa banda aikin amsa waya babu abinda yake
Yana gama wayar yatashi yafice daga Dakin

Be dade ta futaba, taji Ana nocking tana budewa taga ma’aikaciya ce takawo musu abinci, karbar abincin tayi, tajuya cikin Dakin

Gasasshiyar kaza ce da chips, sai shinkafa dataji kori
Dasu Lemon tsami aciki

Zama ta gyara taci abincin tayi Nak, ta ajiye masa sauran, tashiga toilet tayi wanka

Rigar bacci Tasa yellow, daga Saman breast dinta qoqo ne da rigar, daga qasa kuma net ne, kana iya hango komai na jikinta

Tafeshe jikinta ta turare, ta kalli Dakin, afili tace to ga gado ga qasa ga kujera

Idan nabari yadawo qarshan al’amarin zai juye ne yadawo kaina, in kwanta aqasa ko a kujera, shikuma hakimin a gado

Nikuma bazan iyaba, Dan haka bari insamawa kaina mafita, tana gama magana tahaye gadon tayi daidai akansa, tacire ribbon dinta, tare da baza gashin kanta tayi addu’ah Sai bacci

Karde amanta da :

Comments
Share

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

18

Saida yayi kusan 1hour awaje, yana qara bayani Akan aiyukan daya bayar ayi kafin yadawo, sannan yadawo Dakin
Yana turo kofar da kyakkyawar Fuskarta yayi tozali, tana baccinta hankali a kwance,duk gashin kanta ya rufe mata fuska, jijjiga kansa yayi yanufi toilet ya watsa ruwa yafuto yasaka jallabiya baqa

Jikin gadon ya matsa yana Kallanta yace “tashi kikoma qasa”

Yaji shiru

“nasan Sarai kinajina nace ki tashi kikoma qasa”

Nanma yaji shiru, fillon datayi matashi dashi ya bubbuga, ahankali ta Bude idonta, saboda gajiya ga kuma bacci daya dauko dadi
Ta kalleshi, yana tsaye qiqam, tace menene?

Yace nace ki tashi kikoma qasa

Kallansa tayi da mamaki tace qasa? Qasafa kace, uhum wallahi bazan iya kwana a qasaba, saboda ban sababa, jikina ciwo zaimin
Tajuya masa baya tayi kwanciyar ta

Kallanta yake da mamaki, wato kenan de yanzu yarinyar nan tana nufin shine yasaba kwana aqasa ko

Zagayawa yayi ta daya gefenta yadauki fillon gefenta ya wullar aqasa, yadawo yasa hannun sa Akan fillon datake kwance, yajanye fillon, jikake qum
Yabugawa Amal kanta ajikin gadon

Da sauri ta tashi zaune tace Kai Kai Kai
Tana shafa inda ta bige, yau nashiga uku Daren Hana bacci yazo

Kallanta yake sosai, yakasa Hana qwayar idonsa kallan abinda take muradi
Cikin karfin Hali yace “ki iya bakinki”
Kuma still yakasa dauke ido akanta

Harararsa tayi afakaice, aranta tace wallahi gaskiyar Yaya Shahid

Miqewa tayi, tabude kayanta ta dauko jarkar maganin da umma ta aiko mata, takafa Kai tasha sosai
Duk abinda take yana Kallanta afakaice
Tana gama Sha tajuyo tana cewa irin wannan kallan haka ai saida neman tsari

Yace “me kikace?”
Tace a a magana nake da kaina, tahaye kan gadon ta kwanta tare da rufe ilahirin jikinta

Ajiyar zuciya yasauke,yace tashi ki kawomin abinci, dago kanta tayi ta nuna masa abincin tace gashi can acan ai
Shima yace nagani

Tana zunbura baki ta tashi takai masa abincin Takoma gado, yana ganin ta kwanta yasake cewa
Bani takarda acikin jakata

Kafin ta motsa saida tadafe kanta da Hannunta, tace Yaya daddy, Amma bacci nake fa

Kallanta yayi bece mata komai ba, ta tashi ta dauko masa, Takoma gadon zata kwanta tace akwai wani Abu kuma?

Girgiza mata Kai yayi yana Kallanta, tana ganin haka tajuya tasake addu’ah ta kwanta

Iska ya firzar daga bakinsa, shi kansa yarasa gane kansa, yarasa meyasa yake sakata wannan aikin

To Amma meyasa zata lullube jikinta?

Amal kuwa tana komawa gadon bacci ya dauke ta
Shima abincin yaja Dan dole yaci kadan, ko kula takardar data bashi be yiba
Tajera fillon daya dauko agadon yadauko blanket ya shimfida aqasa, yatakure ya kwanta anan

  ***      ***      ***

Alerm ne yatashe su dede lokacin sallar asuba, atare suka farka, Amal ta tashi tana murtsike idonta, tare da hamma saboda baccin be ishetaba
Daddy yana farkawa yaji bayansa ya amsa, Dasauri yakai hannun sa wajan, yaji wajan yariqe, saboda kwana a’inda bai sababa
Dakyar yatashi yashiga toilet, yayi wanka tare da alwala, yana futowa itama tashiga tadauro alwala, tanata kallansa aranta tace wanka da wannan asubar kona menene oho

Yana sallah tana binsa abaya har suka idar, tana gama lazimi Takoma ta kwanta, shikuma yadauko alqur’ani yana karantawa, tana daga kan gadon ta zuba masa ido tana kallansa

Gashinan mutum har mutum Amma ba shida mutuncin kirki
Runtse idonta tayi, Takoma bacci
Shima yana gama karatun, yayi oder abinci yaci, yafita, be zame ko’Inaba Sai Chemist
Maganin ciwon jiki ya karba, yasha, yajefa sauran a aljihunsa, daga nan ya wuce yawon sa ko inda Amal take bai nemaba

Amal kuwa Sai wajan karfe goma ta farka, tayi wanka tashirya cikin atamfa dinkin Riga da zani, Wayarta ta dauka,zata kira su umma Amma Kuma batada Sim card din qasar
Dole Sai hakura tayi ta kwanta

Baidawoba Sai yamma, yana shigowa Dakin tayi masa barka da zuwa
Agajarce ya amsa da “yauwa”
Wanka yashiga, yafuto sanye da jallabiya ajikinsa

Tashi tayi Takoma wajan window tana kallan waje, harya gama shirya
Yadauko takardunsa yafara aiki

Ahankali tace Yaya daddy
Batare daya kalleta ba yace “inajinki”

Dama Dan Allah Dan kiramin anty mufy kaji

Kallanta yayi batare dayace mata komai ba yadau wayar yamiqa mata
Da murmushi afuskar ta, ta karba ta duba Wayarta tadau number takira

Tana shiga anty mufy ta daga, Amal tace anty Ina yini
Muryar wa nakeji kamar masu tafiya honeymoon?

Batasan lokacin datasa daria ba tace a a anty duba lafiyar Yaya daddy mukazo, mufy tace haka de kukace, kawai kuce kun tafi soyaiyarku

Amal ce ta kawar zan can da fadin anty ya junior?
Yana Nan lafiya Amal, inji de babu abinda Dan rigimar nan yake miki ko?
A a anty babu komai, Toshiknn ku kula da kanku bye bye, to anty bye
Tana kashe wayar memakon tabashi saitasa number umma suka gaisa itada baba, sannan takira maisah

Maisah tace Amal wannan layin fa, tace kede bari layin Yaya daddy ne, maisah tace inyee kice komai yazama normal anriga da anwuce wajan?
Ajiyar zuciya ta sauke tace kede bari qawata saina dawo kawai, maisah tace Toshiknn Amal, suna sallama saita kira Shahid, yana dagawa tace Yayanah yakake yagida?

Takardar hannun sa ya ajiye, tsam yatashi yanufeta, batare da yayi Mata magana ba, yamiqa mata hannun sa

Hannun nasa tabi da kallo, alama yayi da kansa ma’ana tabashi wayarsa, idanunta cikin nasa, tabashi wayar

Yana karba yakashe wayar yace “ba kudin banza gareniba dazaki dinga kiramin mutane shashakai dasu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button