BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lalle ma Yaya Shahid dinne shashasha? Tafadi haka aranta
Daukar Wayarta tayi afili tace yaqi taho shashashar wayata, ni Ina sanki, haka yanmata da qannan wasu suna rububinki
Kallanta yayi, yazo dab da ita yace maimaita abinda kikace
Cikin takaici da bacin rai itama tace cewa nayi qannan wasu na rububinki
Yace ita wayar Taki?
Tace nifa bada Kai nake ba, fuskar sa yakawo dab da Tata, ya nunata da yatsa yace idan kika kuskura kika sake kiramin wannan Yaron acikin wayata saina zaneki
Hannunsa takama zata janye takasa
Nikam yayanah ba yaro bane
Cikin bacin rai yace ok, to waye Yaron? Kinsan de inda salma na nan toda tuni na haifeki ko?
Haushi ne yakamata, Jin sunan daya ambata cikin faduwar gaba da bacin rai tace Dan Allah Nika matsa
“bazan matsa ba, kisanar Dani waye yaro? “
Abinda yace kenan
Kokarin matsawa tafarayi, shiko ko gizau be yiba, tana yunqurawa zata tashi ya damqi hannun ta yafizgota dab dashi har sunajin hucin numfashin juna
Idanu suka zubawa juna,nadan wani lokaci, itace tafara janye idanunta acikin nasa
Ta qwace jikinta, Shima yasake ruqota, da karbi ta fizge jikinta, Garin yaruqo hannun tane, saita zame, hannun sa bai sauka ako’inaba Sai Akan nashanunta, yanda yayi niyyar kaiwa Hannunta kyakykyawar damqa aka samu akasi haka yayi musu, wani irin laushi yaji
Atare suka zaro idanunsu
Cikin sauri yasaketa tare dayin baya
Itama Dasauri Takoma kan gadon tare da juya baya, Shima wajan takardunsa ya koma, shiru Dakin yayi, kamar ba yanzu ne suke hayaniyaba
Daddy shiru, Amal shiru
Cikin ransa yace shikkenan najawa kaina raini awajan yarinyar nan, da wanne ido zan kalleta?
Itama anata bangaren cewa take nashiga uku, abinda bai taba faruwa daniba, nida Bayan Yaya Shahid babu Wanda nake hada jiki dashi
Amma Yaya daddy…. Innalillahi
Runtse idonta tayi, kamar mai bacci, Awannan Rana har dare yayi suka kwanta basu sake yarda sun hada idoba
Hakane yayita kasancewa atsakanin su har tsawon sati daya, yau da dare yayi, cikin sauri yadauki wayarsa yahau kan gado ya kwanta
Amal tana ganinsa batace komai ba, saida tazo kwanciya, ta tsaya akansa tace Yaya daddy zan kwanta, qasan Dakin ya nuna mata, yace ga wajenan, nahanaki kwanciya ne?
Kallan qasan Dakin tayi, taja fillo tadau bargo tayi shinfida ta kwanta, Dan ita Kam tadena musu dashi, Kar abinda yafi na rannan yasake faruwa
Yana Kallanta, harta yi bacci sannan Shima yayi bacci
Da asuba Bayan sunyi sallah da Gari yayi haske yatashi zai koma gado ya kwanta, yaga Amal tana mammatsa Hannunta, alamun ciwo yake mata
Maganin daya siyo rannan yatashi yadauko ya wulla mata, yahaye gadon yamiqe
Maganin ta kalla, ta kalleshi, shi ko tausayin ta ma bazai jiba? Kodan yata iya tunda itace tafara
Maganin tasha ta kwanta, sai wajan shadaya nasafe suka farka, shine yarigata tashi, yashirya cikin qananun kaya, baqin wando baqar Riga mai adon ja agaban rigar, saikuma takalmi baqi Shima
Sumar sa tasha gyara, yayi kyau na qarshe
Amal tana ganinsa zai fice aranta tace wallahi nadena Zaman gadi, Dan haka tace, Yaya daddy Nima zani
Kallanta yayi, sannan yace ba Kiyi wanka ba, baki shirya ba tayaya zan tsaya ki batamin lokaci?
Cikin shagwabar da ita kanta tayi mamakin kanta, tace Yaya daddy yanzu fa zan shirya
Kafada yadaga, yanufi kayansa yana fesa turare
Cikin sauri ta dauki towel, ko kayan jikinta Bata cire ba ta nufi toilet
Kallanta yayi, yace minti goma
Dasauri tace to
Tashige toilet din
Zama yayi a bakin gadon Dakin yana kallan wayarsa
Ajima ya kalli agogo ajima yasake kallah
Amal naciki tana Cuda jikinta, ko rabi Bata yiba, taji yace “minti shida”
Sauri taqara Sawa, tagama Cuda jikinta kenan taji yace “minti tara”
Batayi wata wataba, ta sheqa ruwan taja towel tadaura tafuto
Gaba daya iyakar towel din Rabin cinyarta
Yanajin Bude kofar toilet ya kalli wajan
Idanunsa ne suka sauka Akan santala santalan fararen cinyoyinta, yazuba musu wani irin Mayan kallo, yakasa dauke idonsa akansu
Ita kuwa batasan ma yanayiba, tana sauri ta shirya karya tafi yabarta
Agabansa tayi komai, tashirya cikin doguwar Riga, tayi Rolling, tajuyo tace masa nagama
Dago kansa yayi ya kalleta, sannan yatashi yayi gaba
Yaya daddy
Takirashi
Yajuyo be ce mata komai ba
Tace meyasami idonka yayi ja?
Kai tsaye yace Mata ciwo yake
Da kallan mamaki tabishi, ciwon ido alokaci daya haka? Allah kenan me iko
Suna fita basu zarce ko’Inaba Sai wajan shan iska, Amal anata waige ta kalli nan ta kalli can
Wato kenan shi yawon sa yake fita yabarta a hotel a kulle
Wallahi ta dena yarda yafita, yabarta
Suna shiga wajan, sai yan tsirarun mutane awajan, kowa yana harkar gabansa
Wajan zama yanema yazauna, itama haka ta zauna agefensa, tana kallansa tana murmushi
Kallan qarin bayani yayi Mata
Babu wata alamar tsoro atare da ita, tace “kayan sunyi ma kyau Yaya daddy, idan muka koma nigeria kadinga saka qananun kaya”
Eh Lalle Sai yau yasake tabbatar da yarintar wannan yarinyar, in banda yarinta tayaya yana matsayin babban mutum a’idon jama’ah kuma governor zai dau qananun kaya yasaka? Shiyasa fa wasu ayyukan daya kamata ace itace zatayi baya kulata yabata, Dan yasan cewa lokaci daya zata lalata komai
Ai saide yasa suit kokuma manyan kaya,Dan haka ya share ta kawai
Tasake cewa kaji?
Dan karta dameshi ne yasa yace to
Murna acikin Amal, yau itama Tasa mijinta Abu, yace zaiyi
Kallansa tayi tasake cewa Yaya daddy zansha ice cream
Wani waje yanuna mata yace ga wajan can
Hararar sa Tayi ta shareshi, yasanfa batada ko sisi Amma yake cewa ga wajan can it means taje ta siyo
Suna zaune shiru Shiba magana ita kuma taji haushi ta qyaleshi
Saiji sukai an bugo musu ball
Atare suka kalli ball din, kafin su Dago saiga wani kyakykyawan yaro yazo zai dauka
Amal tana ganin Yaron taji ya birgeta
Kamashi tayi ta riqe
Daria Yaron yasaki yace anty nadena please
Mamaki ne yakama Amal da daddy Jin hausa radau a bakin wannan farin Yaron kamar bature
Tace Toshiknn niba abinda zanyima, zoka zauna, zaka tayani fira?
Daga Kai yayi yace eh
Daddy kuwa kallansu yake da birgewa sosai suka bashi sha’awa itada Yaron
Allah yazuba masa son yara, Amma Kuma gashi Allah Bai bashi ba
Me photo ne yake yawo da camera awuyansa, yanayiwa mutane photo suna bashi kudi
Shi kansa yana zuwa wajan su yaga sun birgeshi, yaqaro so yace wow fine boy
Kafin ma yanemi izninsu yafara yiwa Yaron photo
Yadubi Amal Yace kece maman sa? Aikuwa tace eh, yace ta dauki Yaron ayi musu, aikuwa ta sakashi a cinyar ta akayi musu pic din, ya cewa daddy Shima yamatso
Ahankali ya matsa kusa dasu, me photon yace kariqesu mana, ahankali ya rungume Amal, itama ta rungume Yaron akayi musu wani
Me photo saiyi yake, yadago kansa daga kan camera yace Amal ta zauna a cinyar daddy ta riqe Yaron yadauke su
Gabanta yafadi, itafa jikinta yafara sanyi da wannan photunan tunda anyi na marmari ai shikkenan ko
Me photon yace please
Shi kuwa daddy ido yazuba mata yaga gudun ruwan ta
Dan karta bayar da kanta awajan me photo yagano halin dasuke ciki ne yasa kawai ta tashi ta Dane cinyar daddy
Innalillahi… Wannan yarinyar kanta daya kuwa,? Yake tambayar kansa
Amal de adarare ta zauna Yaron kuwa babu ruwansa Shima yahau cinyar Amal, akayi musu photon, yana gama dauka tsilak tatashi daga cinyar sa