BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Camera yabasu, Wai suga pictures din, suna cikin gani Yaron yataba camera yace gani, gaka, yanuna Amal Yace ga momy

Murmushi daddy yayi yace cewa zakai ga daddy, ba gani ba kaji?
Yaron yadaga kansa

Daddy yace yasunan ka? Yaron yace Sunana Hanif ahmad Muhammad marzuq

Daddy tace what?
Kafin yayi magana saiga iyayensa sunzo wajan

Daddy naganin ahmad yace haba, no wonder, nide yacemin hanif ahmad Muhammad

Cikin murmushi ahmad yace daddy, Wai Kaine anan? Gaba daya ganinku yayi wahala, siyasa ta boyeku
Daddy yace kaide bari abokina, wannan duk aikin Abba ne wallahi

Cikin daria ahmad yace wallahi nasani, kaga iyayen nan namu Sai ahankali, shiyasa nabaiwa ayyukan company na muhinmanci sosai, saboda Nima kada dady yasakani a harkar siyasar nan tasu

Gaba daya sukasa daria daddy yace eh gaskya ne, wallahi
Wai kana nufin wannan Yaron Kane? Ahmad yace emana, ai twins ne ga dayan can shida mamansu suna tahowa

Itama tana qarasowa ta miqa wa Amal hannu suka gaisa, wadda mamaki yakashe ta a zaune

Tace sunana nafeesa, Ana kirana da feenah

Amal tace sunana Amal
Abinka da mata nan suka koma gefe suma suna tasu firar

Amal nan da nan tasaki jikinta da feenah, da fira tayi tsawo nema feenah take qara wayar mata dakai Akan Zaman takewar rayuwar aure, tana qara jaddada mata cewa ta riqe mijinta dakyau
Domin kuwa sun dace mutuqa

Zan can sosai yashigi Amal, anan taita mata godia
Ahmad ne yace zasu tafi, anan daddy yake cewa yaushe zasu tafi sukace gobe, dama kawai sunzo hutawa ne nadan lokaci

Daddy yace suma suna kan hanya nanda sati uku
Amal ta riqe feenah tace anty nafeesa, Dan Allah ku daga tafiyar kizo muyita firar mu

Feenah ta dafata tace kiyi qanwata, insha Allah wataran zan kawo miki ziyara
Abinda yasa zamu tafi gobe, Ana bikin aminiyata ne Zahra da abokin karatuna kb

Amma Badan hakaba zan tsaya, rungume juna sukai
Anan sukai sallama suka tafi

Wajan shiru yasake yi kamar da, Amal ta dubeshi aranta tace kiga yanda yake zubawa abokinsa daria, Amma ni ko oho

Saida suka dade awajan sannan suka kama hanyar komawa hotel, ita kadai yace tayi gaba zaije yadawo

Batace masa komai ba tayi ciki, tana shiga daki tafada duniyar tunanin makomar aurensu

Daddy baya kulata, Amma kowa bashida bakin magana saide yace sun dace
Har tsawon wanne lokaci zasu dauka ahaka? Wanne irin miji Allah yabata ne?

Tana wannan tunanin taji yaturo kofar Dakin yashigo da Leda ahannunsa

Be tsaya ko Inaba Sai Gabanta, ya miqa mata Ledar

Karba tayi cikin sanyin jiki ta Bude, tana budewa tags ice cream ne aciki dayawa

Da murmushi a Fuskarta tadago tana kallansa

Comments and share please

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

19

Tace nagode Yaya daddy

Juyawa yayi yakoma kan kujera yana cire safar qafarsa, Kallanta yake yanda take shan ice cream din har wani lumshe ido take, ta wani kama suna ta riqe kamar a bakin ta
Yana Kallanta takai sauran cikin fridge, tadau towel zata shiga wanka yatashi yabar Dakin, Dan yadena gangancin ganowa kansa tashin hankali

Lokacin daya dawo Dakin tagama wanka, tana tsaye tana fesa turare yashigo, saudaya ya kalleta yadauke kansa

Yadau jallabiya yashiga toilet, lokacin harta kwanta, dataga yafuto ne ta tashi Takoma window danta barshi yashirya anutse duk da acikin jallabiya yake

Yanayin Garin take kalla, tako’ina yahadu, tana Nan Jikin window harya gama shirya yazo gadon Shima yaja bargo tare da kwanciya
Motsinsa taji a gado, takai Kallanta Gare shi, tace a a Yaya daddy yahaka?
Kallan rashin fahimta yayi Mata, Dan haka tace nice fa a kwance agadon
Amma Kuma Naga kazo ka kwanta, anan zaka kwanta ne?

“amsar kenan”

Abinda yafada mata kenan yajuya mata baya ya share ta
Takaici da haushi suka cika Amal, Toma da meyasa ta tashi?
Kawai daga bashi dama yashirya shine harda zuwa gadon ya harde

Fillo taja qwaya daya tayar aqasan Dakin

Taje ta dauko jarkar maganin tsuminta, muryar sa taji yana cewa “menene wannan?”

Cike da haushi ko kallan inda yake batayiba tace “maganin tsari ne”

Yana Kallanta ta kafa Kai ta diddika sannan Takoma qasan Dakin ta kwanta ko blanket Bata shinfida ba ta kwanta haka

Kallanta yake Sai cika take tana batsewa kamar zata fashe, yaruntse idonsa gamida bacci

  ***      ***      ***

Washe gari ma haka Amal ta tashi jiki duk ciwo,tana kallan maganin daya wullo mata rannan ko kula shi batayiba bare tasha, tana tashi tayi wanka, yarigata tashi, ashirye ta ganshi Amma takardu ne agabansa
Dan haka itama ta shirya ta zauna tana jiran yagama su fita

Shiru shiru bataga alamun zai fita ba tace Yaya daddy, yau ba fita?

Yace “zan fita de wajan koyan gaisuwa”

Ajiyar zuciya ta sauka, sannan tace Ina kwana?
Yayi banza ya shareta

Har yamma suna zaune ahaka, Babu me magana, shi yana aikin gabansa, ita kuma ta kama masa ido tana kallansa
Meyasa takeji ne komai yayi birgeta yake?
Meyasa take yawan tunanin sa?
Mutumin akwai aji ba laifi
Lumshe idonta tayi aranta tace dole in nemi maisah idan nakoma in fada Mata abinda nakeji game dashi, ko zata Iya bani shawara

Haka suka zauna har dare, Babu inda suka fita, da daddare yauma yarigata wanka, Dan haka yayi kwanciyarsa a gado, saboda yagaji da aiki sosai
Yakashe wutar Dakin ya kwanta

Amal na futowa daga wanka ta kalli daki duhu, ta kalli qasan Dakin baya nan, kallan gadon tayi taganshi ya kwanta harya fara bacci

Dan haka ta shirya itama, cikin rigar bacci medan kauri kadan
Tafesa turare ako’ina na jikinta, ba tayi wata wata ba ta Haye gadon ta kwanta

Wato shi ko ajikinsa, ta mutu ko Tai rai, saide ya miqe a gado yabarta da kwanan ciwon jiki

Addu’ah tayi ta kwanta

Bacci yayi bacci, Amal Sai juyi take, batasan ta kusanto kanta dashiba, haka Shima cikin hancinsa yakejin qamshin turare da humra, natashi, baisan lokacin daya matso ba, hancinsa daidai wuyan Amal, bacci yayi dadi alarm ya buga, Babu wanda ya motsa acikinsu
Saida Gari yafara haske, Amal tafara Bude idonta ahankali, Gaba daya shaf ta manta tare take da daddy, tana gama Bude idonta taganta ajikinsa

Gaba daya kansa yana Jikin wuyanta, kamar Wanda Yake kissing wuyan nata

Da karfi tace wayyo Allah nah!
Hakan data fada ne ya farkar da daddy daga daddadan baccin dayake

Kallanta yayi, yaga yanayin da suke ciki

Cikin sauri ya tureta, yatashi yashige toilet, yasakarwa kansa shower
Meyakawo wannan yarinyar kan gado? Inaga de yarinyar nan idan baiyi da gaske ba zata sa azo ayi abin kunya

Yana futowa daga wanka yaga tagama gyara gadon
Kallanta yayi yace “meyasa kika kwanta a gado?”
Murya ciki ciki tace Yaya daddy jikina ne yake ciwo idan na kwanta aqasa, saboda ban sababa

“to waye yasaba? “

Tace ba kowa, kuma saida nacema ka kwanta Akan gado Bayan nice zan kwanta kace amsar kenan

Cikin bacin rai yace ok nagane, to Dan Allah kici gaba da kwanciya kinji, zakiga abinda zai biyo baya
Yana fada Mata haka, yatada kabbarar sallah
Itama toilet din tashige tana cewa babu abinda zan gani Sai alkhairi

Tun daga wannan Rana Amal ta tsorata da maganar daddy, tadena kwana a gado, tadawo qasa, tun jiki na tsami harta saba

Bayan fitar dasukai zuwa wajan shan iska, sau daya yasake fita da ita wajan wasanni anan taga Gari sosai, daga nan bai sake fita da ita ko’inaba
Har hutu daya dauka yaqare, yau suna tashi yace ta shirya zasu fita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button