BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin zumudi ta shirya, cikin doguwar rigar atamfa launin purple
Mayafi ta Yafa basu wuce ko’inaba Sai wajan siyaiya
Tunda suka shiga wajan suke ta zagayawa, tana binshi abaya, shikuma yana gaba yana amsa waya
Sunfi minti talatin dashiga shagon, ya juyo zaice mata kingama? Saiyaga wayam Babu abinda ta dauka

Kallanta yayi dakyau yace me kike yi ne?
Cikin fara’ah tace ba yawo muka zoba? Wallahi wajan yayi mugun kyau Yaya daddy, tafadi haka tana juyawa tana kallan wajan tareda wara hannayenta

Haushi kashe daddy
Gaba dayama yarasa maganar dazai fada Mata
Yanzu fisabilillahi yarasa Ina zaije yawo Sai wajan shopping? Meyake damun tane Wai?

Fizgar Hannunta yayi, yajata qiiii Sai tafiya suke, saida yakawo ta wajan kayan kwalliya ya tsaya yace kidau abinda kike so gobe zamu wuce Nigerian

Ga mamakinsa Saiyaga ta Bata fuska, tace nagode babu abinda nakeso mu koma kawai

Matso wa yayi dab da ita, yayi qasa da murya kamar me rada yace karki min musu anan, ki dauka mu tafi

Tana zunbura baki ta daukarwa Abba turaruka, ita kuma tadau kayan kwalliya
Shiru tayi tana nazari me momy take so? Sai can tasaki murmushi ita kadai, tasan momy akwai son ado, kullum cikin kwalliya take, Dan haka tajuyo ta cewa daddy zamuje wani wajan

Shikuwa Kallanta yake, yaga tana Abu kamar me jinnu, inba hakaba kiyi shiru kina tunani kuma ki saki daria ke kadai? Wani abinma de sai yara

Zagayawa ta dinga yi awajan saida suka zo wajan saida yari, ta nuna masa wata hamshaqiyar sarqar gold tace adauko mata ita, me wajan kuwa ya miqo mata ita tare da Dan kunnan ta, sai ta kuma daukan Zabe na azurfa me kyau, sai kuma wani zoben Amma shi na gold ne, ta gwada ahannun ta, sannan ta cewa daddy tsaya anan Ina zuwa

Wajan kayan maza ta nufa ta dauko masa gajerun wanduna, da three quarters, sai best masu shegen kyau da tsada
Tazo tace masa nagama mu tafi
Kallanta yayi, Shiba Wai siyaiyar ce tayi yawa ba a a kawai Yana mamakin sarqa da dankunnan datace abata ne, mezatai dashi? Anya kuwa tasan kudinsu?

Ita kuma Amal Sarai taga kudin sarqar, dubu Dari biyar ne, tunda tasan tazo da daddy tasan cewa batada matsalar kudi

Suna komawa gida tahada musu kayansu duka, tsarabar ta kuma tasaka acikin Jakarta, zoben azurfar data siyo ta kalli aranta tace nasan wannan zoben zaiyiwa Yaya Shahid kyau

Ta daga dayan zoben gold din, tace wannan kuma nasan zaiyiwa shahida kyau, bazan Bata hannu da hannu ba, Yaya Shahid zan bawa yasaka mata da kansa, nasan shahida zatai farin ciki da haka

Washe gari suka Lula nigeria, jirgin su na sauka motoci sukazo taryansa, jama’ah kamar me, dole Sai motar datake da baqin glass suka shiga wato tinte

Government house suka tafi Kai tsaye, motocinsu na sauka shahida ta futo da gudu tahadasu ta rungume su, sai sannu dazuwa take musu

Ba yabo ba fallasa Amal ta amsa mata, saida sukaci abinci suka huta

Sannan yasamu damar ganawa dasu Abba

Amal ce tafuto Fuskarta da murmushi tace miqawa Abba tureren data siyo tace Abba gashi
Yakarba yace masha Allah nagode sosai yata

Ta dauko sarqar data siyo ta bawa momy cikin ladabi tace momy kema ga naki

Duk Akan idon daddy

Momy tace Kai Kai masha Allahu Amma Amal kince nayi kwalliya naje gidan biki kaina tsaye
Gaba dayansu sukasa daria, Abba yadubi daddy yace babana to kaga yanda akeyi

Shikam mamaki ne yahanashi magana,kawai ya sunkuyar da kansa qasa cikin kunya, kenan ita Bata siyowa nata iyayen komai ba, nasa iyayen tasiyo wa, shikuma daya kamata yayi tunanin siyo musu, Shima bai siyo ba

Haka kowa yakoma dakinsa cikin nishadi
Washe gari suka koma gidansu, inda daddy yakoma bakin aikinsa

 ***        ***      ***

Bayan kwana biyu takira maisah zata fada Mata abinda takeji game da daddy, sai maisah tace gobe gobe ma zatazo bauchi takawo mata ziyara
Amal de kawai tajita ne, Amma Bata yarda ba, haka sukai sallama
Washe gari daddy bai kwana agida ba, misalin karfe biyu saiga Kiran maisah tace Amal nazo, na qwanqwasa gidan maigadin bai budeba, Amal cikin mamaki tace wanne gida maisah?

Cikin daria maisah tace gidanku mana, ai aguje Amal tazo tabude mata gidan suka rungume juna

Suna shiga ciki aka Bude babin fira, tare suka shiga kitchen suka hada abinci mai rai da lafiya, sannan suka koma falo sukaita firar su

Maisah tace inajinki yar damagaram, Amal tayi Ajiyar zuciya tace maisah tunanin sa nake, idan na zauna ni kadai banda aiki Sai tunanin murmushin sa, da maganar sa
Koya batamin rai Ana jimawa zan manta inyita tunanin sa

Maisah takama hannayenta tace wa kike nufi Amal?
Kai tsaye tace daddy maisah
Amma shi baya sona, Bana gabansa, maisah tunda nake dashi bantabajin yakira sunana ba, bayamin magana saide inta kama dole, nikuma a jinsa birgeni yake wallahi

Maisah tace Amal, kin kamu da mahaukacin kaunar mijinki

Zare hannayenta tayi daga cikin na maisah tace tayaya? Tayaya hakan zata kasance maisah?
Mutumin daya tsani inyi masa magana zan kamu da soyaiyarsa?

Maisah saboda nafita waje Ana ruwan sama nayi wanka, shikkenan yakori maigadin gidan, Wai nice zan dinga budewa tunda na zabi nuna wa maza jikina

Arana saina kirashi yafi sau nawa, Amma shi Koda wasa ban taba ji yakirani ba, kullum cikin Zaman hakuri muke nida shi

Maisah ce tasake riqo hannayen Amal tace, to Amal koma de menene, kina kaunar daddy, yanzu ai yarage namu, Wajan ganin mun shawo kansa yadawo kan layi, Koda wasa kada ki nuna masa kina sansa, Dan mazan yanzu sunce suna sanka ma Yaya aka qare, bare basu nuna suna soba,
Sannan kome zakiyi masa kawai kiyi abisa ke bakisan kinyi ba

Kidinga jansa da fira yanaso ko bayaso, sauran maganar kuma kawo kunnanki kiji

Rada maisah tayi mata, tace kin gane de, ke nida nake budurwa ma nice me gwada miki wadannan dabarun?

Maisah kin tabbatar idan nayi haka zai Soni Shima?
Sosai ma kuwa Amal, ki jarraba kigani

Amal tace Toshiknn, aikuwa zan aiwatar maisah

Haka suka tafi Dakin Amal, suka barbaje kayan akwatunan ta, maisah ta dinga ware mata wasu daban, tana qara wayar mata dakai

Sannan suka futo, suka Sha firar su, dazata tafi Amal tayi dibi dibi tarasa me zata Bata, tace maisah mezan baki?
Acikin gidan nanfa tunda nazo kudi nawa na kaina ban taba riqe wa ba, baya bani, maisah tace keni kin isheni da mitar mijinki, tsakanin ku, lokacin dazaku fara love bawanda yasani

Daria Amal Tasa, cikin ranta tana darurar aikata shawarar da maisah ta Bata

Saida ta raka maisah gar gate, sannan tadawo gidan ta zauna afalo, tana tunani, Wai ita keson daddy, mutumin dabawani kulata yakeba banda ganganci irin na zuciyar ta

Tashi tayi, tashige daki tafara hada kayanta tana gyarawa, afili tace daga yau zan fara kawo canji awajanka daddy

Nagaji da wannan rayuwar

Tunda kayi gangancin dana soka wallahi kaima saika Soni
Zakasan ka shigo hannun yar mutanan Niger

Tana ta magana afili tana shirya kayan acikin wardrobe

(Sharhi please)

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

20

Bayan tagama jera kayan, ta tsaya ta kalli Dakin, nan tacire Dan kwalin kanta tayi wulli dashi, tafara gyara Dakin, tashiga toilet ta wanke ko’ina
Sannan tasaka turaren wuta me shegen qamshi adakin, tadauko kayan data siyawa daddy a Germany tatafi dasu dakinsa
Cikin wardrobe dinsa ta Bude tasaka masa aciki, sannan tahau gyara Dakin
Gadon tafara gyarawa tayi shara tayi mopping, taje toilet din nanma ta wanke shi ta gyara tsaf, hatta turarukan dasuke kan mirror saida ta sauya musu tsari, sannan tasaka wani turaren wutar mai qamshi daban

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button