BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Gyaran Dakin tayi, sannan tashiga toilet ta wanke Tasa turaren wuta, tafuto, tana sakawa Dakin ma taga yayi juyi yaja fillon dake gefensa ya rungume shi
Shikuma mafarkin ta yake, gatanan tana kwance ajikinsa zata tashi yaqara rungume ta, Amma Kuma yakasa yimata magana
Qamshin turaren wutar dayaji ne ya farkar dashi, ahankali yabude idonsa, dede lokacin Amal tajuyo, idanunsu suka sarqe dana juna
Ido yazuba mata yakasa janyewa, meyasa nake Abu ne kamar wani wawa cikin kwanakin nan? Duk a saboda ke
Murmushi tasakar masa tace Yaya daddy Ina kwana?
Yace “lafiya”
Yatashi yashige toilet din
Tana mopping Dakin yafuto daga toilet daure da towel a’iya qugunsa, duk jikinsa awaje, kallansa tayi akaro nafarko ahaka, Dasauri ta janye idanunta daga kallansa, gashi ne dayawa a kwance akirjinsa
Gabanta yana faduwa, tadau ko masa kayansa ta ajiye Akan gadon, takasa hada ido dashi, Shima ya lura da firgicin datake ciki, Dan haka ya matso kusa da ita sosai daga Bayanta, yadan rankwafa dede tsawon ta, yakai bakinsa saitin kunnanta
Cikin aji da nutsuwa yace “kingama aikin, kokuma in temaka miki?”
Maganar ce tazo mata wani iri, shi dinne zai taimaka mata? Tab Lalle in hakane aikinta na kyau
Dasauri tace a a… Nagode, saika futo, tayi wuf tafi ce daga Dakin
Yabita da kallan murmushi
Juyawa yayi wajan mirror ya kalli kansa yanda yake murmushin
Afili yace meyake damunane? Wannan yanayin da nakeji ko Akan salma banji Shiba
Shiryawa yayi cikin sauri, yafuto qasa
Yauma tare suka ci abinci, kowa yana satar kallan dan’uwansa dasun hada ido kowa saiya kawar dakai
Suna gamawa Takoma kujera ta zauna, Shima daki yashiga yabaje takardu zai fara aiki, kawai kuma saiya fasa yadawo falon Shima, hannun sa ta kalla taga takardu da wannan jakar dayazo da ita
Zama yayi anesa da ita kadan, ita tana kallo shikuma yana aiki, yana cike takardu yana satar kallan ta, ita kuwa Bata sani Bama
Yaya daddy Dan Allah Dan aramin wayarka, dago kansa yayi ya kalleta, Babu musu ya miqa mata wayar, tana amsa number ta tasaka aciki takira, Kiran na shigowa Wayarta tayi saving number sa
Sannan ta dauki number momy, data Shahida da Abba, already tanada ta anty mufy
Bashi wayar tayi, tace gashinan nagode, ina zuwa, ta tashi tashige dakinta
Yana ganin shigarta yadauki wayar Tata, yaduba wayarsa yaga number ta tasaka aciki tayi kira
Sake Kiran wayar Tata yayi, yazubawa wayar ido ganin
“my d”
Yafuto barobaro Akan screen din wayar, me kenan? My daddy? My darling? My dear?
Motsin ta yaji yayi sauri ya ajiye wayar ya sun kunyar dakansa kamar bashiba
Akwatin daya shigo da ita jiya yatura mata Gabanta, kallan mamaki tabishi dashi tace na menene Yaya daddy? Kai tsaye yace kudinki ne
Tace kudi kuma? Girgiza kansa yayi yace haqqinki ne amatsayin ki na matar gorvnor, bakida banki shiyasa nakawo Miki duka
Mamaki ne yakamata, ita Amal itace da wannan kudin?
Dagowa tayi cikin murmushi da Jin dadi tace nagode Yaya daddy
Yace bani ne nabaki ba, wannan haqqin government ne
Tace nasani but babu abinda zanyi dashi, kayi amfani dashi wajan ciyar da yara yan primary abinci duk ranar juma’ah
Kallanta yayi da tsananin mamaki, wacce irin yarinya ce wannan?
Kafin yayi magana ta nuna masa wata takarda acikin takardun gabansa tace Yaya daddy wannan ta menene?
Cikin mamakinta yace, sunayen dalibai ne dazamu tura qasar waje domin su qaro karatu
Daria tasaki tace eh gaskya ka kyauta Allah yatemaka yatayaka riqo
Yace amin, idansa akanta
Awannan Rana haka suka wuni cikin nishadi, haka tasashi a gaba taita tambayar sa abubuwa Akan mulkin su yana fada Mata
*** *** ***
After one week
Yana zaune a office dinsa, yayi Nisa cikin tunanin ta,
“Yaya daddy oyoyo, nayi missing dinka “
Maganar tace take masa yawo acikin kunnuwansa
deputynsa yazo yakawo masa wasu takardu yace ranka ya dade!
Ranka yadade!!
Ranka yadade!!!
Yafada da Dan karfi
Firgigit yayi yadawo daga duniyar tunanin daya tafi
Yace ranka yadade wannan takardun hajiya ne, angama hada komai harma anfara rabawa yaran kamar yanda tabada umarni, sauran kudin kuma suna cikin account dinta kamar yanda kace abude asaka, inyaso duk Bayan wata saita dinga turowa
Ajiyar zuciya yasauke Yakalleshi yace yanzu na wata nawa aka dauka? Rissinawa yayi yace andau na wata shida
Na Rabin shekara kenan?
Eh ranka ya dade na Rabin shekara, daddy yace ok zaka iya tafiya
Yana fita wayar daddy tadau qara yana dubawa yaga momy ce, tace yazo gida shahida ba lafiya
Dasauri yatashi yace ganinan zuwa momy
Lokacin dayaje gidan harta samu bacci, yadubi momy yace momy Wai jikinne?
Cikin jimami tace shine daddy, shahida tacika tunani Akan Yaron nan dan’uwan Amal, nace ta rage tunani Amma taqi ji, kuma nace abbanku yayi wa mahaifinsu magana yace a a
Jinjina kansa yayi yace Allah yasawaqe insha Allah komai zaizo qarshe
Momy tace to Allah yasa
Yace bari naje gida zuwa dare zan dawo insha Allah kafin nan tafarka
Tace to daddy nah
*** *** ***
Karfe tara yashigo gidan, yana zuwa yafada kan kujerar falo yacire hularsa yayi wulli da ita, Sumar kansa ya hargitsa, Wai wannan Yaron meyake ji dashi ne zai kama yakashe masa qanwar sa?
Idanunsa suka kada sukai jajir
Amal ce tabude kofar dakinta ta futo, tace Yaya daddy sannu da zuwa
Be amsa mataba yatashi yafara dosota
Tsorata tayi da ganin yanayinsa, tafara Ja dabaya har suka je kofar dakinta
Idanunsa jajir yanuna ta da yatsa yace “ki fadawa wannan Yaron, wallahi tallahi idan ya kuskura qanwata ta rasa ranta a dalilin sa, sai nadau mummunan mataki Akan ku, dagake harshi zan hadaku in kulle
Dafe kanta tayi da Hannunta, shahidan datake tunanin yanda zata shawo kan Yaya Shahid ya kula ta, akanta ake mata wannan tozarcin
Dago kanta tayi tace, naji Yaya daddy, Amma please kadena aibata yayanah agabana, yanda kakeji da shahida haka nake jinsa acikin zuciyata
Cikin tsawa yace karki sake ambatar wannan Yaron agabana, ok wato kina jinsa azuciyarki, kenan sansa kike, kaunarsa kike
Cikin haushi da bacin rai tace, Yaya daddy sansa nake, kuma aurensa zanyi, Dan Allah kayi abinda zakayi
Tajuya cikin daki tana kuka, rufe kofar Dakin tayi tana wani irin kuka me ciwo, wato ita tana Nan tana haukan sansa shi zuciyar sa tana bashi Shahid takeso
Lalle kuka ma rahma ne, Dan dabatayi ba, inaga saita samu matsala
Shima daddy Juyawa yayi yakoma dakinsa, yafada kan gado
Da aurensa da komai Amma tana San wancan Yaron, me zai nuna masa? Meyasa shi bazata soshi ba Sai Shahid?
Binjimar jikinsa yacire yayi wulli da ita, sai huci yake shi kadai
Awannan dare haka masoyan biyu suka Kasa rintsawa kowa yana tunanin dan’uwansa
*** *** ***
Tana idar da sallar asuba, tadau Jakarta tazuba kaya kala biyu aciki, ta nayi tana share hawaye, saida Gari yayi haske wajan karfe takwas tatashi taduba ko Ina tayi batada ko sisi, Wayarta ta duba taga tanada sauran kudi aciki dubu biyar da Dari biyu
Ahankali tafuto falo taci babban hijabi, har taje harabar gidan wani tunani yafado mata, tadawo ciki tadau niqab dinta ta daura, sannan tafi ce daga gidan Bata zarce ko Inaba Sai tashar Mota
A bangaren daddy kuwa karfe goma yatashi, yayi shirin office yafuto domin ganin Yaya Amal tatashi
Yana futowa falo yaduba dining yaga wayam Babu komai
Dakinta yashiga Dasauri, saide har toilet yaduba babu ita babu alamar ta
Kamar mahaukaci yayi hanyar kitchen nanma batanan
Harabar gidan yaduba still nanma batanan