BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Gidan yadawo yaduba lungu da saqo batanan
Ahankali yazame yafadi jagwab aqasa, Idanunsa yacika da qwallah, gumi ya wanke masa fuska
Kirjinsa yaji yariqe, yaji numfashi yana gagararsa yi
Cikin ransa yafara maimaita kalmar
Innalillahi wa inna ilaihir raju’un
Comments and share please
Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
21
duhu duhu yake gani, hakan yasa ya rufe idonsa yana maimaita hailala cikin ransa
Bade yarinyar nan guduwa tayi ta barshi da halinsaba
Daqyar yakai kansa daki, yakira jb awaya
Kan gadon ya kwanta kansa na wata irin sarawa nan da nan zazzafan zazzabi ya rufeshi, yashige cikin bargo yana karkarwar sanyi
*** *** ***
Tana zuwa tasha taga mutane kowa yana harkar gabansa, jama’ah kamar ba safiya ba, anan taga amfanin niqab, domin kuwa dabata futo dashi ba da tuni anganeta, inda a jigawa ne Babu wanda zai Santa, Amma nan, mutane dayawa sun Santa
Me adedeta ta kalla tace Dan Allah bawan Allah kaini shagon da ake saida Kati
Mai adedeta yace haba hajia, maganar gaskya to kudinki ya qaru
Tace babu matsala, nide kaini
Har gaban shagon inda ake saida katin yakaita, yace sallameni hajiya
Juyowa tayi tace Dan Allah kayi hakuri Ina zuwa
Wajan me shagon taje tace Dan Allah zakasai katin? Wayarsa ya dauko Yace Fado number’s din Katin
Tace no transfer nake nufi
Yace nawane kudin? Tace dubu biyar ne
Yace to gaskya duk nera dubu Dari takwas muke siya, kinga kudinki yakama dubu hudu kenan
Tace badamuwa
Kati yabata yace ga number ta nan ki turo
Diri Diri tayi, tarasa ya zatayi, saboda Bata taba yiba, tace a a ga wayar katura da kanka
Karba yayi yasaka number yace nawane pin din transfer din?
Tace bansaniba wallahi ban taba yiba
Yace tab hajia kice aikin naki ba qarami bane, to Bari abude miki
Me adedeta ne yasaki hon
Tajuyo tace Dan Allah kayi hakuri bawan Allah, so nake yabani kudin saina baka
Me shagon ne ya kalleta yace, nawane kudin nasa hajiya?
Itama ta dubi me adedeta tace nawane kudin?
Yace Dari biyar
Me shagon yadauka yabashi, Shima yayi transfer yabata dubu hudu, tace miqa masa Dari biyar din tace gashi
Yace haba hajiya babu komai kije kawai, ainaga kina halin buqata ne, kallansa tayi sosai tace nagode bawan Allah, Dan Allah Ina zan samu motar jigawa?
Yace muje na rakaki, tana bin bayansa sukaje har wajan lodin motoci, taji Ana jigawa, jigawa, dutse, ina na dutse
Tace masa nagode bawan Allah, Allah yasaka da alkhairi, Yaya sunanka Dan Allah? Yace sunana hamza tace to ngd Malam hamza
Tana zuwa tace jigawa zata, aka Bata waje ta zauna, aranta tace gara in nemi ruwa insha Dan tafiyar ba qarama bace, futowa tayi zata fice condasta yace malama Ina zaki, saura mutum daya Mota ta tashi, tace ruwa nakeso
Hannu ya miqo mata yace kawo a siyo miki, Dan idan kikaje wajan nan za’ai tunanin wani Abu zakisa hajiya ko bomb haka, saboda kinci wannan uban hijabi ga liqabi
Itade kudin tabashi Takoma motar, yana kawo Mata ta karba tasaka a cinyar ta
Ba’a jimaba Mota ta cika aka fara hada kudin Mota tace nawane kudin?
Yace kudin ki dubu daya da dari biyar
Tadau ka tabashi
Sunyi Nisa atafiya sosai, wani yaro a cinyar maman sa yadubi Amal Yace anty budemin
Kallansa tayi taga Bobo ne ahannunsa, ta karba ta Bude masa, tana bashi yace kema ki Bude idonki irin mamana
Matar ce ta bige masa baki, tace Umar nahanaka surutu bakaji ko? Ta dubi Amal tace nagode baiwar Allah Dan Allah kiyi hakuri
Murmushi Amal tayi tace a a rabu dashi babu komai
Matar tasake cewa Lalle kin ciri tuta, wannan Bobo tun ranar juma’ah aka Raba musu shi a school Amma yaqi Sha, sai zai Bude saiya fasa, gashi yaude anbude shi
Murmushi Amal tayi tace Allah Sarki
Wani ne daga baya yace ai ance matar gwamna ce tace a dinga rabawa yara ko
Matar tace eh wlhy ai ta kyauta wallahi
Gabanta ne yafadi, kenan.. Dama Yaya daddy da gaske yake wannan uban kudin nata ne?
Kenan maganar data fada masa harya aiwatar da ita
Jingina tayi da Bayan kujerar datake zaune ta lumshe idonta
“kingama aikin, kokuma in temaka miki?”
Maganar daddy ta Fado mata arai, hawayen idonta ta share afakaice, yanzu bala’in datake ji na qaunar daddy haka shahida takeji? Harna shahida yafi nata yawa? Akan soyaiya harda su hawan jini? Amma still Yaya Shahid yaqi kulata?
Sukuwa wanne irin yayu Allah yabasu? Daddy baya sonta, Shahid bayasan shahida
Ajiyar zuciya tayi, insha Allah zan dedeta tsakanin su, shikuwa wannan yaje ya qarata da halinsa
*** *** ***
Har cikin Dakin jb yashigo, ganin mutum yayi a kwance asaman gado yana karkarwar sanyi, cikin zolaya yakama bargon yace maigirma gwamna ya akayi?
Wani irin zafi ne yabugoshi, Dasauri yace subhanallah
Daddy? Meyasameka? Me akama? Ina Amal din take ta barka haka Kai kadai?
Cikin karkarwar sanyi yace jb nashiga ukuna jb
Subhanallah daddy kana fadar min da gabafa, Dan Allah menene?
Shiru daddy ba amsa
Dagoshi jb yayi, yace daddy meyake faruwa, meyafaru da abban?
Kuka daddy yasaka
Abinda jb tunda yake dashi bai taba ganiba, yace innalillahi daddy waye ya mutu Dan Allah?
Rungume shi yayi yace jb tatafi, ta gudu ta barni, wallahi bazan iya rayuwa batare da itaba
Jikin jb ne yayi sanyi, yana kallan daddy, Amal din da ake cewa za’a saka itace yau ake kuka akanta?
Bubbuga bayansa yakeyi alamar rarrashi yace Haba daddy calm down mana menene abin kuka? Mekayi mata?
Saboda nayi fada Akan wannan Yaron shine ta rama masa
Jb yace wanne yaro kenan?
Kai tsaye yace yayanta Shahid, wanda shahidan momy take so
Jb yace to meyasa zakai mata fada akansa, ba yayanta neba?
Da sauri yadago yace yayanta ne Amma ai da aure atsakanin su, Wai harda cewa tana Sansa, kenan ni Bata sona
Daria ce takesan kwacewa jb, yace kayi hakuri, Amma tunda ka lura bataso saika dena fadan
Kamar itace agabansa cikin zafin rai yace kuma saita tafi tabarni?
Jb yakasa boye dariyar sa, dole saida ya murmusa sannan yace yanzu Ina taje? Daddy Yace bansaniba jb, nasan tsabar tsanar datamin ne yasa ta gudu
Jb yace kuma yazaka zauna haka? Muje gidan momy mu duba idan Bata nan Sai Akira commissioner of polis yasa atare ko wacce hanya aduba
Yace bazan iya tashiba jb kirjina ciwo yake
A a daddy daure muje, daure kaji, yafadi hakan yana kokarin dagashi, haka suka fice daga gidan suka nufi gidan momy, wayarsa ya dauko akaro na farko yafara Kiran number ta, Amma is switch off
Suna Zuwa gidan, jb yagaisa da momy, ta dubi daddy tace shikuma wannan me aka masa?
Cikin karyaiyar murya me kama data masu kuka daddy yace momy Bata….
Bai qarasaba jb ya tare zancan da fadin, bayajin dadi ne, Wai abinci zaici ya kwanta yahuta
Harararsa momy tayi tace kabar matarka agida kazo Nan neman abinci? Ta tashi tayi kitchen
Atare suka kalli juna shida jb kenan Bata zoba
Number commissioner daddy yanema cikin sauri yace aduba duk wata Mota dazata jigawa daga bauchi idan anga mace wata yar fara, bazata wuce shekara Sha takwas ba, to adakatar da motar
Cikin girmamawa ya amsa da angama sir, abinka da waya tuni aka dakatar da ko wacce Motar dazata shiga jigawa
*** *** ***
Suna gab da shiga cikin dutse aka dakatar da motarsu, Dan sandan ya dubi direban motar yace Dan Allah sorry fa zamu duba wata mata ne
Gabanta ne yayanke yafadi, Karde ita daddy yasa adubo
Nanta fara salatin annabi acikin ranta
Dan sandan yaduba babu ma yarinya a motar Sai mai niqab nan yace baiwar Allah Dan Allah Dan Bude fuskar ki