BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Da mamaki yace shi nuran ne yayi miki wannan dukan?
Karaf akunnan baba hamani
Dagatawa yayi da shigowa falon
Cikin kuka Tace wallahi Yaya shine, Wai nayi acuci maza, ni wallahi Yaya bansan acuci mazaba
Kinga yi shiru, zan sameshi anjima har gidan iyayensa zanje
Yanzu bari inje indora miki ruwan dumi ki gasa jikinki ko?
Hawayen idonta ta goge tace yawwa Yaya to jeka
Kallanta taga yanayi tace mene?
Da ido yayi Mata Nuni da ita, Dan haka cikin sauri ta dagashi tana daria, Shima fita yayi, yafara neman tukunya
Umma cikin ranta tace haka de kuka iya, dagakai harshi
Shi yaji andaketa kokulani baiyi ba yafita
Kaikuma Kaine mai dafa mata ruwan wanka
Lokacin datayi aure aisai kubita gidan mijin kuci gaba dayi mata bauta
Da gaske yake wanke tukunyar, yaje fanfo yana tara ruwa, dagokan dazaiyi yaga tana masa daria
Kallan sa ya maida kan umma yace umma kiga yanda take min daria
Allah zan jiqaki
Lalle Yaya matarka ta huta da wanke wanke taci gaba da dariyar ta, aikuwa ruwan yatara a kofi ya watsa mata
Lalala Yaya shine ka jiqani
Aikuwa tana futowa ta dauki tiyo tatara, ta setashi nan da nan ya jiqe
Tiyon ya qwace ahannunta, tana kokarin karba shikuma yadaga kan tiyon sama aikuwa Sai saukar ruwan Sukaji akansu
*** *** ***
Cikin sauri yake tafiya,yaci baqar suit daka ganshi kaga cikakken S.S daya daga cikin security din gidan ne, yana zuwa falon ya tardasu a zaune Abba da momy juwairah
Rissinawa yayi yace yallabai angama binciken komai, komai da komai yana cikin wannan takardar
Takardar ya karba yabude, what!
Jigawa fa nagani
Ai yayi Nisa dayawa
Shide aqame yake baice komai ba
Glass din idonsa yacire yace zaka iya tafiya
Cikin sauri yajuya yafita
Momy juwairah tace yanzu de alhaji Muda muke nema aiko birnin sin ne maje
Yace hakane, Toshiknn zansa aje a karbo
Cikin sauri tace a a alhaji, Wai Yaya mun samu dama zakayi sakaci da ita, kawai kaje da kanka kokuma ni inje
Yace haba, taya zan barki kije, Babu damuwa insha Allah gobe zansa ashirya mana tafiya Sai muje, saide fatan Allah yasa adace
Tace amin
*** *** ***
Sallama yake kwadawa a kofar gidan
Salamu Alaikum!!
Daga ciki matar gidan tace Kai wannan wacce irin sallama ce haka Kamar Wanda yazo gidan makafi
Daga ciki tadaga murya tace Ana zuwa
Shima daga nesan yace basai kinzo ba, kituromin uban nura
Ha’ba ta riqe tace to uban nura kuma, wannan kuwa waye?
Mijin ta taje tasanarwa Ana sallama dashi, yana fita, yameqawa Malam hamani hannu, Badan yasan darajar amsa gaisuwaba da bazai meqa masa hannun ba
Suna gaisawa yace ba zama yakawoniba, Malam lado kajawa danka nura kunne karya kuskura yaqara taba yarmu
Kullum bashida burin daya wuce yadauki hannu yadaki Amal, Akan acuci maza, to yarmu Bata cutar maza saide su cuceta, kafada masa haka kawai
Malam lado yace aransa yace ikon Allah yau kuma tijarar akaina ta sauka
Afili yace masa Toshiknn, za’a kiyaye insha Allah
Baba hamani baice masa komaiba yakada binjimar sa yayi gaba
*** *** ***
11:30 am A dutse international Airport jirgin su yayi landing
Kai tsaye government house suka wuce shida jama’ar sa
Suka gaisa da governor of jigawa state, inda suka samu tarba mai kyau, sai Bayan sun huta ne, aka hadasu damanyan motoci guda uku qirar Benz, dukansu glass dinsu tinted ne, basu Bata lokaci ba suka dau hanyar maigatari
*** *** ***
Oya Bude bakin
Babu musu tabude Bakinta, yacigaba da bata abincin
Sake debowa yayi a spoon din yanufo bakinta, kawar da kanta tayi tace Yaya please naqoshi
No banyarda ba yarinya, oya Bude
Haka yadinga dura mata abinci, agogon hannun ta ta kalla mai sauqin kudi, tace Yaya lokaci yaja, karna makara islamiya, zuba mata shanyaiyun idanunsa yayi, yayi qasa da murya yace ni bazan samu abani ba kenan?
Yanda yayi maganar cikin sigar dabata saba ganiba hakan ne yasa ta kalleshi cikin sauri
Danya kawar da tunanin ta yasa Shima cikin sauri yace shikkenan to, tunda bazan samuba
Amal tace to Yayanah karka damu nida kaina zan baka dinner saikace kakoshi
Promise?
I promise Yayanah
Dahaka ta tashi cikin sauri ta zumbula qaton hijabin islamiyar ta, gabanta yana faduwa tana darurar haduwarta da Malam nura, ko yau Yaya zasu qare?
Saurin datake ne yasa tariqe niqab dinta ahannu
Tana futowa kofar gida tayi turus ganin wasu manya manyan motoci a kofar gidansu
Gawasu mutane sunci baqaqen suit kowa yasa baqin Glass alamar ba mutunci
Motar tsakiya taga sun nufi sun Bude kofar ta, aikuwa wani babban mutum yafuto
Da ita yafara tozali, ganin kallan datake musu ne yasa yace yarinya zo mana
Ahankali cikin nutsuwarta taqarasa har inda yake ta rissina tare da fadin Ina wuni?
Fuskarsa dauke da murmushi yace lafiya Lau
Nan ne gidan Malam hamani danda?
Yafadi haka yana mai Nuni da gidansu tace eh nan ne
Yace yauwa maza jekice yayi baqi
Dayake akwai kofar shiga ta waje, tanan tashiga aikuwa yana zaune yanajin radio
Tana fada masa yace tashiga gida ta dauko musu ruwa
Tana kawo musu ruwan, tagansu harya shigo dasu cikin falon, ss din suna tsaye, maigirma Abdallah ne kawai a zaune
Ruwan nazuba musu, Babu alamar qyanqyami yadauka yasha
Baba ne yace Amal jeki dauki wancan qwan kiyi addu’ar samun qaruwa ajiki ki kawomin
Ajiye jakar makarantar tayi tare da niqab din yadauki qwan Takoma gefe tafara rubutun da tawada cikin nutsuwa
Maigirma Abdallah ya kalli baba hamani da mamaki aransa yace yanzu wannan qanqanuwar yarinyar ce zatayi wannan aikin?
Baba hamani kamar yasan abinda yake tunani yace masa alhaji karka damu
Yaron wajanki zai haihu
Um karka damu, zai haihu da yardar Allah
Tana gama rubutun ta maiqowa baba hamani qwan
Tace baba natafi islamiya yace Amal
Tajuyo yace daura niqabin naki mana
Murmushi tasaki tace to baba
Tsayawa tayi tadaura tafice, gabanta yana faduwa saboda makarar datayi da kuma shakkar haduwarta da Malam nura
Abba yana zaune yana kallan ikon Allah, sai yaji sun birgeshi da alama mutumin akwai tarbiya agidansa
Baba hamani ya katse masa tunani da fadin to gashi alhaji
Wannan qwan guda daya ka ganshi?
Abba yace eh
Yace to afasashi asoya, abawa Yaron da matarsa sucinye
Abba yace duka su biyun qwai daya?
Baba hamani yace alhaji muna baka kana Qin karba
Inbakaso tashi jeka
Abba yace a a muna so ya karba yayi godia
Yace nawane kudin maganin?
Baba hamani yace dubu hudu, Amma nama ragi kakawo dubu biyu
Abba yace to mungode, yadauko bandir din kudi guda biyu,har dubu Dari biyu
Yace to gashi mungode
Baba hamani yadauka yacire dubu biyunsa yace jeka da kudinka mu Bama karbar cin hanci irin naku yan nigeria
Abba Abdallah yayi murmushi yace to nabawa yata Amal kyauta
Murmushi baba hamani yayi yace to Amal tana godia alhaji, za’a Bata
Daganan su maigirma Abdallah sukai godia tare da sallama suka tafi
Mrs Usman ce ✍????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
4
Ahankali take tafiya kamar yanda tasaba cikin nutsuwa, da zumbulelen hijabinta
Tana shiga harabar makarantar taga malamansu maza awaje, gabanta ne yayi mugun faduwa lokacin datayi ido biyu da Malam nura ta cikin niqabinta
Har qasa ta tsugunna ta gaidasu Amma abinda yabata mamaki shine yanda ko maganar makara babu Wanda yayi Mata acikinsu
Tana qarasawa ajin, ta zauna kusa maisah, kallan ta tayi tace Kai Amal yau kin makara dayawa, Bayan kinsan halin Malam nura bashida ‘m’
Wlh Rumaisa baba ne yasani aiki
Shiyasa nayi latti, maisah tace Ayya, aikuwa aikin iyaye shine gaba Akan komai