BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gabanta yana dukan tara tara ta kama niqab din zata cire, me motar yace haba oga, yanzu kuma idan matar aure cefa?
Dan sandan yayi shiru Sai can yace hakane to shikkenan kawai ku wuce
Wata wawar Ajiyar zuciya tasauke, suna shiga dutse tahau motar dazata kaita maigatari
*** *** ***
Har dare Ana bincike babu matar da ake nema, Dan haka suka sanar da daddy daya Kasa zaune yakasa tsaye shida jb
Ana fada masa ba’a ganta ba Jiri ya debeshi Sai gashi yaraf Akan kujera, jb yace ya Salam, doctor yakira, yazo yaduba daddy, yana gama duba shi yace ranka ya dade zamu turaka zuwa India asake duba lafiyar ka, saboda jininka yahau sosai
Duban doctor din yayi yace zansa lokaci naje, thank you zaka iya tafiya
Yana fita, daddy ya lumshe idonsa, yarinyar nan zata kasheshi
Commissioner ne yasake Kiran wayar daddy, cikin sauri ya amsa yace anganta ne?
Yace yallabai gaskya babu labari abinda yafi shine ka turo number Wayarta, saimu tuntubi number muga inda me wayar take,sannan dazu anga wata yarinya ne niqab afuskar ta, but ance matar aure ce shiyasa muka barta suka wuce
Dasauri ya miqe tsaye yace kace niqab? Commissioner yace qwarai kuwa haka bincikenmu ya nuna
Kawai kashe wayar yayi yadubi jb yace tabbas itace, jb yace daddy mata fa masu niqab yawa garesu, yau da ace kaga kayan jikinta, to saimu kafa hujja dashi, hanyar kawai dayace a tura musu number aga inda take, nakega hakan shine zaifi bamu tabbacin inda take
Duban jb yayi a sheqe yace kanka daya kuwa jb? Number matar tawa zan dauka nabasu?
Daddy yanzu fa babu lokacin nuna kishi, nemanta muke, dole mubi wannan hanyar
Shiru yayi tare da tura number Amma cikin ransa ya qudurta cewa dole yasake mata Sim card
Yana tura musu suka kirashi sukace sun duba, Amma wayar a kashe, Dan haka zasuci gaba da dubawa dazaran anbude wayar zasu sanar dashi halin da ake ciki
Awannan Rana haka daddy yadinga faman kiransu awaya, suna cewa suna nan suna jiran kunna wayar
*** *** ***
Yamma lis na sauka agarinmu, cikin sauri nataka aqafa na qarasa gida, saboda some time bancika son Hawa machine ba, ina shiga gidan nafara ganin umma, haka itama tanajin sallamata tadago Kai tana kallo na cike da mamaki, ina zuwa nafada jikinta, umma tace Amal? Anya lafiya kuwa zuwa haka babu sanarwa?
Nace umma lafiya kalau, ina Yaya Shahid da baba? Tace babanki yafita Shahid kuma yana ciki
Daga murya nayi nace yayanah gani nazo futo
Da mamaki afuskar sa yafuto yana cewa wanake gani kamar Amal? Da murna ta Nace nice yayanah, umma taje takawo min ruwa, tana zama nakoma jikinta nakwanta nayi shiru, umma tunda ta ganni tasan cewa ba kalau ba, tsakanin uwa da da dama Sai Allah
Shahid yace umma karki Bata abinci zanje inkawowa qanwata abin dadi
Nace yauwa Yaya Shahid yi sauri, yana fita kuwa, umma tace Amal inji de kalau din ne kamar yanda kika fada?
Idanuna ne suka kawo ruwa, tana ganin haka cikin ranta tace dama nafada
Dan haka tace naji, kiyi hakuri, kowa dakike gani Amal hakuri yake agidan auren sa, karki sake naji kin fadawa babanku wani Abu tsakanin ki da mijin ki, Sarai kinsan halinsa saide yasake lalata komai
Kaina na girgiza nace to umma insha Allah, tadafa kaina tace yauwa Allah yayi miki albarka
Muna zaune Yaya Shahid yadawo naji shawarar umma haka nasaki jikina mukai ta fira, Yaya Sai daria yake bani, da daddare baba yadawo yaganni, muna zaune afalo dukanmu ya kalleni yace Amal, nace na’am baba, Amal na’am baba, Amal na’am baba, saunawa nakiraki?
Nace sau uku
Ya ki fadamin wannan zuwan naki babu sanarwa idan wani Abu Yaron nan yayi miki insaki agaba kikaini wajansa inci ubansa mudawo gida shikkenan anwuce wajan
Nace baba wallahi babu komai kawai kewarku nayi shiyasa nazo naganku, yace to shikkenan Allah yayi miki albarka nace amin baba
Yace ai muma angama ginan sabon gidan namu, jibi jibin nan mukasa zamuje wajan mijin naki da iyayansa muyi musu sabuwar godia, nace to Allah yakaimu baba yace amin
Saida naje kwanciya ne nafada duniyar tunanin mijina, Allah Sarki Yaya daddy ko Ina yake yanzu? Kome yake?
Haka nakasa bacci banda juyi Akan katifata babu abinda nakeyi
A yayinda daddy ma yakasa zaune yakasa tsaye, yakasa ci Dasha, haka kowanne ya kwana da damuwa
*** *** ***
Washe gari Yaya Shahid yace nashirya muje Inga sabon gidan, muna tafiya ahanya nace Yaya yaushe Wai zakai aure? Yace aure Amal, ba yanzu ba kuma banda wacce nakeso, nace aikuwa Yaya nasan bazaka rasa yanmata ba
Yace da gaske babu Amal, saide ki samomin
Nace aikuwa na samo Maka Yaya wata hadaddiya wallahi, yace wacece? Nace muje gidan nafadama, haka muka qarasa gidan, muna zuwa Naga ko Ina gida yatsaru dakuna har guda biyar, da furniture dinsa da komai anzuba, zama nayi nazuba tagumi a falon gidan, ashe Yaya yana kallo na, yadawo kusa Dani ya zauna yace fadamin qanwata, meyake damunki? Nace Yaya babu komai, yace yaushe kika fara boyemin damuwarki Amal?
Ganin haka yasa nafada masa komai da komai, yace haba Amal, yaushe kawai danya cemin yaro zaki dagawa mijin ki murya? Karki sake kinji? Nace to Yaya, yace Amma Amal daddy yana sanki tunda har yake kishi Akan ki, karkiga laifinsa kinji? Nace to Yaya Anima Ina sansa shine baya kulani, Dan Allah yaya ka daure kaso qanwarsa ko Shima zai Soni, Yaya duk lokacin daya tuna bakasan shahida bayajin dadi, Yaya abinda kayi shi za’a ma, bakasan shahida Shima baya sona
Jikinsa ne yayi sanyi, yace Toshiknn qanwata insha Allah zanyi tunani Akan hakan, nace Yaya shahida tana sanka, idan halinta ne baimaba kana fada Mata zata dena, Yaya a dalilin sanka shahida hawan jini takamu dashi, itace BURINAH awajanka Yaya, ka auri shahida please
Hannayena ya riqe yana murmushi yace to Amal, zan iyayin komai saboda ke, insha Allah daga yau zan fara kula da shahida, Amma fa saboda ke, nace nagode yayanah
Wayata nadauko acikin jakata na kunna ta, nadauki Tasa wayar na saka number shahida aciki, duk yana kallo na, nace gashi kira mana ita
Zubamin ido yayi yana kallo na, yace ni gaskiya kunyarta nakeji wallahi, saide kiyi mata magana saiki bani ita, daria ce takama Amal, Dan haka kawai saita kira shahidan awayarsa tasaka wayar a hands free
*** *** ***
Yaci suit ruwan suminti yana zagaye falon nasu, shahida da momy suna kallansa, wayarsa tayi qara, cikin sauri yadaga yace ya ake ciki? Daga daya bangaren akace, ranka ya dade me number nan munga no cewa tana jigawa state, maigatari local government
Ajiyar zuciya yasauke me qarfi yace ok nagode,
Cikin sauri yajuya zaibar falon, yaji wayar shahida tayi qara juyowa yayi zaiyiwa momy sallama
Kawai yaji shahida tace laaa anty Amal, layin waye wannan kika samu?
Cak yadakata, kenan gida tatafi? Ya tabbata kenan itace mai niqab din da akace angani
Daga dayan gefen Amal tace anty shahida babu lokacin bayani, yanzu de gawaya zaki gaisa da wani
Shahida tace wani kuma? Kafin Amal ta Bata amsa shahid ya karbi wayar tareda sallama, gaban shahida yafadi
Cikin in Ina tace Shahid
Adaya bangaren Shahid yace na’am ammata yajikin naki?
Ai batasan lokacin datasa daria ba tayi cikin daki, momy tabita da kallan farin ciki
Shikuwa daddy hararar Bayanta yayi, wato ita wannan yarinyar ta gyara Tata soyaiyar, Amma shi a dalilin ta Tasa soyaiyar zata lalace
Yasan duk aikin Amal ne wannan, to shikwa idan bai nemi yarinyar nanba ai Sai Allah ya tambayeshi, ficewa yayi da sauri yanufi Mota yana waya da jb Akan anganta