BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sakawa yayi aka kawo masa mask irin wadda maza suke sakawa lokacin sanyi yasaka a fuskarsa, banda idonsa da baki da hanci babu inda kake gani

Mutane zasu bishi ya dakatar dasu, yashiga motar da kansa qirar Mercedes Brabus, yadau hanyar jigawa

  ***      ***     ***

Yayi Nisa ahanya police suka tareshi zasu duba boot din motarsa, yana daga ciki ya bude musu suka duba babu komai
Yayi gaba wasu ma suka sake tareshi, ina driving license din ka? Yadauko ya bayar, ina takardun Mota yaudauko yabayar

Dan sandan yace kai gaskya ni banma yarda dakai ba, katashi kaboye fuska kamar barawo, kawai kawo na goro kayi gaba, daddy da takaici ya cika shi yadauko dubu goma yabashi, nan da nan dansandan yafara fara’ah
Yace aaa kace yau nayi babban kamu, zaka iya tafiya, daddy yace nine da godia ai, menene sunan Kane?
Cikin washe baki yasanar dashi, yace to ngd yaja motar yayi gaba

Yana tafiya yakira commissioner yace adakatar da aikin wannan police din

Kuma yasameshi shida dansandan a office next week

Haka yayita tafiya wasu su dubashi saboda Allah, wasu Kuma su karbi cin hanci, haka Shima daya wuce zai bada umarnin dakatar dasu daga aiki

Har ya shiga jigawa, sannan yadena cewa a kamasu, yazo wani Gari kiyawa ruwan motar yaqare, haka yafuto yadaki tayar motar, Kai wannan yarinya ta cuceni, banda yana Santa tayaya zai tsaya wasu qananan yan Sanda suna masa tambayar renin wayo, haka yafuto yaje wani gidan mai yasamu ruwa yazubawa motar sannan yaci gaba da tafiya

Sanadin tsaye tsaye dayayi ahanya hakan ne yasa bai qaraso Garin ba Sai dare, hadari yahadu gabas da yamma, dakyar da tambaya yagane gidan su Amal

Yana futowa daga aka tsuge da ruwa mai karfin gaske, yaqarasa kofar gidan harsun rufe gida, ya qwanqwasa, yaji shiru gashi Ana ruwa, abinka da me zazzabi nan da nan jikinsa yafara rawa

Umma na daga falo taji kamar Ana bugawa tatashi zata fita, Amal da Gabanta yake faduwa tun dazu tace umma zauna Ana ruwa, bari naje nabude

Kafin umma tayi magana tayi wuf tafice daga falon taje bakin qofar ta Bude ahankali

Dashi tayi tozali, ga ruwa anayi, duk yafara jiqa musu jikinsu
Idanu suka zubawa junansu kowa yakasa janye nasa idanun

Juyawa tayi zata koma ciki, yasa hannu ya fuzgota jikinsa

Amal cikin kuka tace Nika sakeni banaso

Kasakeni banas…… Bata qarasaba yayi saurin hade bakinsu waje daya, yanayi mata wani mahaukacin kiss

(idan akwai me qorafi zai iya fadamin, Kar amanta da Sharhi please inajin dadin hakan)

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

22

Tsawon minti biyar suka dauka atsaye, yaqi sakin Bakinta, ruwa duk ya yagama jiqasu
Daqyar Amal ta tureshi Gabanta yana faduwa, wani irin yanayi takeji atare da ita wanda Bata saba Jin kamarsa ba

Kallanta yake kamar sosai kamar yau yataba ganinta
Ahankali yace “yace nakeji”
Kallansa tayi, saiya Bata tausayi, daure wa tayi tayi gaba tabarshi anan, shikuma dayaga tayi gaba saiya biyo Bayanta
Tana dauke qafarsa yake maida Tasa
Har sukaje cikin falon, umma ce taganta tashigo da mutum Dasauri ta tashi tace a’a kice baqo mukayi, karaam Kaine atafe da wannan Daren?
Yana Dan karkarwar sanyi yace wallahi nine umma, Amma kansa aqasa yakasa hada ido ta ita, tace sannu da zuwa shigo mana, qaraso muje wajan Malam suna ciki shida Shahid
Bayanta yabi suka shige, Amal kuwa da sauri tayi cikin Dakinta, tafada kan katifar ta, tana maida numfashi, me Yaya daddy yake nufi da wannan abin dayamin? Idanunta take juyawa alamar tunani, ahankali takai Hannunta kan Dan qaramin lips dinta tana shafawa

Acan kuwa baba mamaki yayi ta yi dayaga daddy Bayan sun gaisa ne, yace karaamullah ashe kana hanya, Muda muke ta shiri gobe zamu taho muyi muku godia, ai angama gida, sosai yayi kyau muna godia sosai wallahi, daddy da kansa yake sunkuye yace a a babu komai
“dama tace tanasan ganinku ne shine nace tazo Sai nazo mu tafi, saimu tafi gaba daya goben insha Allah “
Abba yace to Babu damuwa Allah yakaimu, Shahid kuje yaci abinci saika hadashi da Amal yaje yahuta
Shahid yace to baba, yatashi suka koma falo,suna zama Shahid yace inasu shahida?

Maganar tabawa daddy mamaki, shi kansa Shahid din yarasa dalilin dayasa yayi tambayar

Murmushi daddy yayi yace “suna lafiya” umma ce takawo musu abinci kadan daddy yaci yace yaqoshi, Shahid ya qwalawa Amal kira, tana futowa yace ki rakashi daki yayi wanka ya kwanta, akwai kaya aciki saiki nuna masa, ni zanje wajan baba, ahankali tace to Yaya
Dubansa tayi tace zo muje
Tashi yayi yabi Bayanta suna Zuwa, yabi Dakin da kallo, shi be taba kwana a’irin wannan Dakin ba, Amma saboda ita yau zai fara, Amma Kuma babu laifi Dakin yayi, Babu tarkace

Ruwan wanka tahada masa a toilet, zai shiga ne yadubeta yace inajin zazzabi ko zan samu magani?
Batace komai ba tafice daga Dakin, Kallanta yayi, yaga alama de har yanzu Ana fishi dashi
Toilet yashiga yafara wanka
Taje wajan umma tace umma Wai zazzabi yake ko akwai magani? Umma tace dama yanda ruwa yadakeshi Kam ai dole

Jeki dauko adaki, kibashi yasha, Amma duk da haka kitafi da ruwa mai sanyi ki temaka masa ya goge jikinsa, zai rage zafin zazzabin

Tace to, tana dauko maganin, tatafi Dakin tana tunanin maganar umma, in temaka masa it means fa nice zanyi masa hakan ko

Itade jiki asanyaye Takoma Dakin, dauke da ruwa da magani, tana shiga yafuto daga wanka daure da towel din Shahid ajikinsa

Batare data kalleshi ba tace ga maganin nan Ina zuwa, tafice

Dawowa tayi dauke ruwa awata yar qaramar baho Sai qaramin towel ta ajiye agefensa

Kallan maganin data kawo tayi, ta ganshi dam ko tabawa be yiba

Kallansa tayi tace meyasa bakasha maganin ba? Idanunsa akanta yace ai baki bani ba

Kai ita tarasa meyasa yake mata wannan abubuwan
Maganin ta ballo guda daya tabashi ahannunsa, ta miqa masa ruwan ya karba yasha
Yadubi ruwan Gabanta yace”mezakiyi da wannan ruwan? “

Kame Kame tafara, tace am.. Um.. Dama fa umma ce tace waika goge jikinka dashi zaka denajin zazzabin

Kallanta yake yanda duk ta rikice, yace ai bazan iyaba, saide in zaki temakamin, kaina ciwo yake kuma zazzabi nakeji, ga sanyi danakeji, har mura duk damuna take

Kallan mamaki tamasa menene abin jero wannan jinyoyi?

Ahankali ta matsa kusa dashi, kusan tayi kusa har tanajin hucin numfashinsa, tsoma towel din tayi acikin ruwan ta matse, sannan tafara goge masa jikinsa

Kallanta yake yakasa dauke idonsa akanta, ahankali yakai hannun sa kanta yacire Dan mayafin data rufe kanta dashi

Yana cirewa kuwa gashin Kanata ya sakko har Saman Fuskarta
Yasa hannu ya maida mata gashin baya

Yaci gaba da aikin Kallanta, jiki asanyaye taci gaba da goge masa Jikin, tagama goge masa ko’Ina sannan tafara goge masa Kirjinsa da duk gashi ya kwanta

Abinda ya lura dashi shine tafi goge wajan, to Kode tana so ne?

Yanata tunani harta gama ta dauke mayafin ta, da ruwan zata fice yayi sauri yariqo Hannunta

Yana riqe da hannun nata yatashi tsaye yamatso dab da ita, yakama Fuskarta da hannayensa biyu bakinsa dab da nata yace “meyasa kika tafi kika barni?”
Gabanta ne yake aikin faduwa takasa wani Motsin kirki

Idonta ne yaciko da qwallah, Bata iya dakatar da zubowarsu ba, cikin kuka tace fada kakemin

Tasa hannu zata goge hawayen,yayi saurin kawar da Hannunta yace “no yakai bakinsa kan kumatunta ya lashe hawayen tas”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button