BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Yana riqe da itan yace, “BABY please karki sake tafiya ki barni, kin Riga da kin zama wani bangare na jikina
Yakai bakinsa saitin kunnanta cikin rada ya furta I love you
Ai Amal najin haka batasan lokacin data qwace tayi Dakinta ba, tana zuwa ta rufe kofar harda kullewa
Tafara Tsallen murna, kan gadon tafada Sai birgima take tana murna
Nan take tadau waya ta kira maisah, anan take cewa gobe tazo gida da safe zasuyi magana
Maisah da batasan da zuwan Amal dinba tace lafiya kuwa? Amal tace kede kawai kizo, dahaka sukai sallama
Shikuwa daddy da murmushi yabita da kallo, sai shine ya kawar da bahon, sannan yabude jakar Shahid yaduba wata jallabiya yakasa
Sai adakin baba Shahid yakwana, yayinda masoyan biyu suka Kasa rintsa wa kowa yana tunanin dan’uwansa
*** *** ***
Washe gari Yaya Shahid ne yayi musu komai, yayi wanka, suka shirya, har daki umma takai musu abinci, suna gamaci Shahid yake danyi masa fira haka jefi jefi duk da bawani sabawa sukai ba
Amal kuwa bacci tasha me dadin gaske, saida Gari yayi haska sosai sannan ta tashi tayi wanka, ta kira maisah, sannan tafice wajan umma taci abinci, umma tana hankalce da ita Bata nemi abincin dazata kaiwa mijinta ba, kenan da ba’a Kai musu haka zaiyi ta zama, Kai wannan Yaro yana hakuri
Maisah ce tashigo gidan tana ganin Amal suka rungume juna, Bayan sun gaisa da umma sukai ciki, Amal tabata labarin abinda yakawo ta gida, maisah taita mamaki tace yanzu Wai Dan Allah yana gidan nan? Amal tace wallahi yana ciki maisah ai ingaya miki dayaji bala’i dakansa yafada
Maisah tace meya fada qawata? Tace yana ciki
Aikuwa suka sa daria, maisah tace kice shikkenan de yanzu an wuce wajan, ke wallahi garama da kika taho
Daria nasa nace eh wallahi
Wayarta ce tadau, qara tana dubawa taga shamsu ne, cikin haushi tace nikam nashiga uku nah, Amal tunda mutumin nan yarasaki shikkenan yadawo kaina, yakade min hankali wallahi
Amal tace wakenan? Maisah tace Yaya sham mana
Amal tace alhamdullahi, wallahi wannan Abu yayi, maisah ki aure shi Dan Allah
Kallan mamaki tabi Amal dashi tace Amal kanki daya kuwa, tsohon saurayin kinefa, a a bazan iyaba, Amal tace to menene? Tsohon mijinane? Kokuma a kanmu aka fara? Kinga ni yanzu Yaya daddy nakeso, Babu sham acikin zuciyata
Kiyi tunani maisah, BURINAH Inga kinyi aure kema, Dan haka nide indan tanine karki damu, Allah yasa mudace gaba daya, maisah cikin sanyin jiki tace zanyi tunani insha Allah
Amal tace yauwa qawata kokefa
Sun dade suna fira sannan sukai sallama maisah tatafi gida
Shahid ne yazo yacewa Amal taje ta kwashe kayan dasukaci abinci, ta tashi tatafi Dakin Shima yayi wajan baba
Tana zuwa Dakin ta ganshi a zaune yana amsa waya, saida tabari yagama sannan tace Yaya daddy Ina kwana? Kallanta yayi yace haka ake gaisar da miji?
Itama tace Tome zance? Yace tsaya in nuna miki
Tashi yayi yaje ta Bayanta ya tsaya, ahankali yasa hannayensa Akan hips dinta, yasunkuyo da kansa dede wuyanta cikin muryar rada yace “baby Ina kwana?”
Kasa amsawa tayi, tayi shiru tana Jin wani iri ajikinta
Acan falo kuwa umma ce tace bari kiga naje da kaina na kwashe kayan dasu Shahid suka bari nasan wannan sakalalliyar yarinyar tanacan ta qunshe adaki
Dakin dasu Amal suke ciki ta nufo, tana zuwa bakin kofar idonta yayi Mata kyakykyawan gani, ayanda taga yasunkuyo da kansa dede wuyanta babu Wanda zaice ba kissing dinta yakeba, shikuma gaisuwace yake miqawa
Allah yaso sunbawa kofar baya, da anyi abin kunya
Dasauri ta juya, Tasa hannu ta dafe kirjinta, yanzu yaran nan banda rashin kunya agidan surukai? Lalle Allah yakawo mu wani irin zamani
Juyawa tayi taje Dakin baba tace Malam yakamata mu tafi kada muyi dare tunda yau zamu dawo, baba ne Yadubi Shahid yace jeka kirasu mudau hanya ko? Shahid yace to baba
Saida yayi sallama sannan yashiga yashiga Dakin lokacin har Amal ta fice
Basu Bata lokaci ba suka futo
Dazasu shiga motar ne sukaga daddy yasaka wannan hular
Nan da nan kuwa kamarsa ta buya, baba yace karaamullah saboda mutane ko?
Kansa aqasa yace eh baba, key din yabawa Shahid yace gashi kakaimu Shahid
Suka shiga motar, suka tafi, shida Shahid agaba, Amal da baba da umma abaya
Sunyi Nisa ahanya Amal ta katse musu shirun ta hanyar cewa baba ingayama Yaya Shahid yakusa aure, saboda nayi masa mata
Baba yace yaushe kukai maganar keda dan’uwan naki bamu saniba? Toma wacce me sa’ar ce wannan?
Tace baba anty shahida ce qanwar Yaya daddy
Umma tace to Shahid Sai munga goron gayyata tunda abin ba sanarwa
Shahid Kasa magana yayi, yayi shiru
Umma tace oh kice Nima dana yakusa zama ango
Sai a sannan yace kai umma ni wasa takemin
Baba yace a a Amal kice gidan surukai zamuje
Dukansu sukasa daria, banda daddy dayayi murmushi kawai
Sosai Shahid yake gudu, har sukaje bauchi babu ma wanda ya lura da daddy
Suna Zuwa directly government house sukaje, sojojin dake bakin gate din gidan suna ganin motar suka Bude musu suka shiga
Tun kafin motar su ta tsaya, security suka qaraso aguje suka Bude musu murfin motar, yana futowa kuwa yacire abin fuskarsa, yafara miqawa mutanan dasuka mamaye wajan hannu suna gaisawa , sai kuma security dake tsare lafiyarsa dasuke tambayarsa Yaya yadawo?
Dole Sai tsayawa yayi su kuma su Amal sukai cikin gidan
Momy tana ganinsu tarasa inda zata sakasu Sai nan nan take dasu, sai yanzu baba yaqara tabbatar wa suna riqe Amal da gaskya
Abba yana gida, Bayan sun gaisa aka gabatar musu da abinci suka ci, sosai umma taji dadi
Babu Bata lokaci ba wajan qara jaddada godiyar su
Abba yace ai babu komai,
Shahid Sai waigawa yake ko zaiga shahida, Amma kuwa tana hankalce dashi, Dan haka tace momy Ina anty shahida ne? Banganta ba
Momy tace shahida tana daki batajin dadi, ciwon ciki take wallahi, yau dashi tatashi
Bari naje natasota ku gaisa, umma tace a a hajiya barta, bari mu shiga mu dubata da kanmu
Adede lokacin daddy yashigo, suka tafi Dakin shahida gaba dayansu, banda, Shahid Sai sunkuyar dakai yake
Amal ta juya tayi masa hararar wasa
Haka itama hankali da tunanin daddy suka tattare awajanta
Tana kwance tana bacci acikin blanket fari qal dashi
Shahid yazuba mata ido, fuskar ta tayi fayau
Motsin dataji ne yasa ta farka, ahankali ta Bude idonta, dashi tafara tozali, Shahid a gidansu? Dakinta? Meza tace da Amal ita kuwa?
Su umma ne suka fara yimata ya jiki, taqayar ta motsa tana amsa musu, saboda ba qaramin ciwo marar ta takeba
Daddy ne ya kalli Abba yace Abba doctor yazo ne? Abba yace eh munyi waya yace yana hanya
Baba hamani yace sannu kinji Allah yasawaqe
Amal ma tace anty shahida sannu da jiki, itama tace yauwa anty Amal
Raliya ce tayi sallama tashigo Dakin dauke da abinci, tace hajiya ga abincin yau bataci komai ba, shahida cikin shagwaba tace momy nide naqoshi bazanciba
Shahid daya Kasa yimata magana, baisan lokacin daya miqawa momy hannu ya karbi abincin ba, ya miqawa shahida yace ki daure kici
Gaba dayan yan Dakin saida yabasu daria, daddy da aka kirashi awaya yafita daga Dakin yana murmushi
Shiru shahida tayi, ganin haka yasa umma tace to Bari mukoma falo hajiya mubar ta tahuta, tana bacci mun tasheta
Aikuwa duka suka fice daga Dakin suna Zuwa falo Amal ta zauna ajikin umma, tana kallan daddy dayake kallan window yana amsa waya cikin aji