BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
*** *** ***
Yana ganin futarsu yadawo kusa da ita ya zauna agefen gadon
Idanu yazuba mata, shi Sai yauma yaga wani irin mugun kyau data masa
Abincin ya ajiye, ahankali yakai hannun sa kan nata hannun
Kanta aqasa takasa dagowa ta kalleshi saboda wani mugun kwarjini daya mata
Zame hannun ta tafara yi, tasan bayaso tunda tayi kokarin riqe kafarsa a Indonesia yakusa sheqa mata mari, Dan haka ta janye hannun ta
Kallanta yake sosai yasake Kai hannu yariqe Hannunta dakyau, wani irin laushi yaji cikin hannun nata, abinka da wanda baya aikin wahala
Murya qasa yace kiyi hakuri
Shahida tayi shiru
Shahid yasake cewa kinji?
Daga masa Kai tayi ahankali
Yace Dan Allah Koda wasa karki rage Koda digo dayake acikin soyaiyar dakikemin, nayi alqawarin zan nuna miki soyaiya fiye da wadda kikemin
Hannun ta dayake cikin nasa yakai setin bakinsa yayi kissing Bayan hannun
Shahida mamaki yakashe ta a zaune, mutumin dayake fada da sababi Akan zata riqe shi, shine yau harda kissing hannun ta? Anya Shahid din data sani abaya ne kuwa?
Abincin yadauko yadebo a spoon yayi Bakinta dashi yace to Bude bakin nabaki
Aikuwa shahida babu musu, ta Bude baki, yadinga Bata abincin, sai gashi takusa cinyewa
Yadebo zai Kai Bakinta ne su Momy Abba, umma da baba da daddy da Amal tare da doctor suka turo kofar Dakin suka shigo
Kana ganin Zaman su kasan irin wannan Zaman Sai masoya
Dasauri ya ajiye spoon din yana matsawa baya cikin sauri, shahida kanta saida yabata daria, to ai sun Riga dasun gansu
Doctor ne yaduba ta, yajuyo yacewa Abba alhaji wannan ciwon cikinfa bazata denaba saide in aure za’ai mata
Amma inba hakaba duk wata ta dinga yinsa kenan
Shahid da baisan Akan wanne irin ciwon ciki ake maganaba cikin tsananin tausayin ta yayi caraf yace to Abba ayi mata auren mana, Amma ace ciwo duk wata?
Gaba daya yan Dakin ne suka zuba masa ido
Shikuma yaji sunyi shiru, yadago kansa kenan kawai yaga dukansu shi suke kallo
Ashefa shine wanda shahidan take so
Wayyo Allah qasa tsage shahida yashige saboda wata muguwar kunya dayaji takamashi, ai cikin sauri yafice daga Dakin yayi falo
Doctor ne yabata magani, su umma da momy dasuke dariyar Shahid suma suka futo gaba dayansu
Ana zaune afalo nan take kuwa baba hamani yace yana nemawa dansa auren yarsa shahida
Abba ma cikin farin ciki yace anbaku Malam
Babu Bata lokaci Abba yakira waya yace kawo musu goro, sannan yakira abokansa biyu, a take aka saka ranar aure nan da sati biyu
Inda daddy yace yadau nauyin komai na ango da amarya
Comments please ????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
23
Godia iyayen duka suka yiwa daddy, Abba yace to Nima de baza’a barni abaya ba, yadubi Shahid yace dana Shahid ka aikomin da takardun karatun ka Bayan biki insha Allah saika fara aiki
Sannan katuromin da account number ka zansama ko miliyan goma ne ka sake rage wata hidimar, kafin muga abinda Allah zaiyi, kayi hakuri babu yawa
Mamaki ne yakama Amal, kyautar miliyan goma Amma ko ajikinsa kamar yayi kyautar dubu goma
Haka su umma sukaita godia, kowa de yana cikin farin ciki, saida suka Dan jima kafin suka fara haramar tafiya gida, daddy yasa adaukesu amaidasu
Amal ta riqe ummanta, tace umma ni wallahi banaso ku tafi, kamar ku kwana anan, umma tace Amal abinda nakeso dake shine, ki riqe mijin ki da iyayen mijin ki Amana Dan Allah, kinga de irin karamcin dasuka mana, Dan Allah karki bari wata matsala ta faru tsakanin ku
Yi nayi bari nabari, kidena barinsa da yunwa, Dan nasan halinki
Amal tace to umma insha Allah
Haka suka dunguma suka raka su wajan Mota, sannan suka dawo ciki
Suna dawowa momy ta dubi Amal tace kira mufeeda ki fada Mata zancan saka ranar
Amal tana farin ciki tace to momy
Bayan sun gaisa da anty mufy ne Amal take fada Mata zancan saka ranar, aikuwa tace to tana Nan zuwa jibi insha Allah domin afara shirin biki
Da daddare dukansu suna yin dinner, shahida Sai tsari take kamar ba majinyaciya ba, Amal nacin abincin ta anutse kanta aqasa, shikuwa gaba daya tension dinsa yana kanta, shahida ta qyalla ido taga yanda Yaya daddy yazubawa Amal ido aranta tace um masoya, har agaban su abban ma babu Kara
Tana dago Kai suka hada ido da daddy aikuwa saita qware
Tari tafara, momy tace subhanallah ungo ruwa Sha yata
Tafadi hakan tana bubbuga bayanta
Ruwan ta karba tasha kadan, momy tace sannu, ai dole ki qware irin wannan kallo haka, ninarasa inda kaje ka koyo wannan kallo wallahi, Kai bakaci abincin ba, ita baka barta taciba
Ahankali shahida Tasa daria, Amma Bata bari gogan yaganta ba
Abba ma murmushi yayi kawai, shikuwa daddy dayasan dashi ake kawai saiya sunkuyar dakai yana shafa Sumar kansa
Suna gama cin abinci, tayi Dakinta tayi wanka, ta kulle kofarta saboda tasan Sarai zai iya zuwa
Aikuwa Bata dade da kwanciya ba, taji alamun Bude kofar, but tariga data kulle
Haka ya hakura yakoma dakinsa, shidama ba komai zai mataba kawai de zaiyi mata saida safe ne
*** *** ***
Washe gari tunda sassafe yashirya yafuto falon, yayi masifar kyau cikin manyan kaya, shi kadai yanata zagaye yana jira tafuto, Amma Bata futo ba, bayasan yafita office batare daya ganta ba, idan yajema tunanin ta zaiyi tayi, bazaiyi aikin kirki ba, yarasa meyasa take masa haka yanzu, Bayan itace tajashi ajikinta harya sake da ita, Amma to meyasa yanzu ta dena?
Yana Nan atsaye shahida ta futo daga Dakinta tayi Dakin Amal din
Har qasa ta tsugunna ta gaidashi ya amsa, yabita da kallo
Tana zuwa Dakin tace anty Amal Bude nazo
Aikuwa yaga anbude kofa, kenan de har yanzu Bata huce ba, shidin ne batasan gani
Kai tsaye Shima yayi cikin Dakin tare da sallama, suna zaune agefen gado
Bema kula su ba ya wuce wajan drawer yafara dube dube
Da kallan mamaki tabishi, meya ajiye mata da zai dauka?
Kamar yasan abinda take tunani kuwa yadubeta yace akwai wasu takardu dana ajiye anan Ina kika maidasu?
Cikin mamaki tace takardu kuma?
Shahida na ganin haka tace anty Amal bari naje nadawo, tafice
Bayanta yabi tareda rufe Dakin, yadawo kusa da ita har jikinsu na gugar juna yace, meyasa kike gudunane?
Kanta ta sunkuyar qasa tace babu komai
Amma Aina baki hakuri ko? Nace nadena, kuma ni magana Akan Shahid dinma nadena, ai dan’uwana ne
Hannayenta yakama yasauko daga gadon yace kiyi hakuri baby bazan sakeba yasake yin qasa da murya yace please
Runtse idanuwanta tayi, zuciyar ta tacigaba da bata shawarar Amal, kinga tun yana bin kanki Kar yazo yadena, mutum mai aji da kudi da kyau dakuma uwa uba miskilanci shine a tsugunne agabanta
Kamar me rada yace kin hakura?
Bata Bude idonta ba ta girgiza masa Kai alamar eh
Tashi yayi yadawo kusa da itan ya zauna, hannayenta dasuke cikin nasa yafara murzawa ahankali idonsa Akanta, shiru tayi tana jinsa, Shima baiyi Mata magana ba kawai de hannun yake murzawa, wani iri takeji ajikinta, saita fara Zare hannayenta, yasan yanayin datake ciki, ahankali yasaki hannun yakama Fuskarta yace zan tafi office
Dan qaramin bakin ta tabude tace to ai baka dau takardar ba,yace gatanan nasameta
Nike nake nema bawata takarda ba
Tashi muje ki rakani, hannayenta ya riqo suka futo har cikin falon, adede lokacin shahida tafuto taci kwalliya tabisu da kallan birgewa
Bai saki hannun nataba saida suka futo har harabar gidan
Yajuyo suna fuskantar juna, Murmushin sa mai bala’in kyau yake sakar mata sannan yace “ki kula da kanki saina dawo”