BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Itama tace Allah ya kiyaye
Sannan tajuya ciki, duk abinda suke a idon security dakuma sojojin dake tsaye
Babu wanda basu birgeba

Tana dawowa falon shahida tajata suka koma daki tace anty Amal menene sirrin? Naga kin rikita yayana, Gaba daya yawani susuce kamar bashi ba, da mutum babu fara’ah Amma yanzu duk yafara sauyawa
Amal tace babu wani sirri anty shahida, Nima haka nake ganin sauyin nasa

Shahida tace to yanzu de fadamin kece matar aure, medame Shahid dina yakeso, menene bayaso? Ajiyar zuciya Amal tayi tace mataki na farko kidinga saka hijabi, Yaya Shahid kishi gareshi bayasan ko kadan yaga mace jikinta awaje, kuma gashi ke kina saka Riga da wando, Rana daya ki gwada saka atamfa kiga yanda zaki rikitashi
Koni kafin ayimin aure baya barina nafita batare danasaka niqab ba

Shahida tace da nasan hakan tun farko daba tuni nayi ba, yanzu bani hijaban ki kigani

Amal nabata hijaban ta dinga sakawa daya Bayan daya Amal nayi Mata pictures

Sannan taje Dakinta ta duba cikin wardrobe dinta ga atamfofin nan gayu ne yahanata sakawa, daya ta dauka aciki tasaka suka futo falo akayi wani pictures din, sannan aka fita waje nanma Amal tayi mata wasu, daga karshe suka hadu su biyu suka yi

Falo suka dawo suna ganin pictures din Amal tace yanzu ki fara tura masa su ta chttng kiga yanda zaiyi biyaiya, shahida Tasa daria tace to aikuwa angama anty Amal

Yauma haka Amal ta rufe kofarta, ita batasan wannan abin da Yaya daddy yake mata, wani iri takeji ajikinta, kuma bata saba Jin hakanba, Dan haka ta kulle kofarta ta kwanta, still Yauma saida yazo yimata saida safe yaji arufe, haka yakoma dakinsa, yana tunanin ta

  ***       ***        ***

Washe gari anty mufy tazo, dukansu suna falo a zaune Ana fira junior yana kan cinyar Amal, sai fruit dake gabansu suna fira suna Sha, momy kanta ta cika da farin ciki, ganin yanda komai Yayi normal yarta ta samu cikar BURINTAH

futowa yayi cikin shirin fita, waya yake amsawa yana cewa gamunan zuwa, ok
Anty mufy yagani yace anty yaushe kika qaraso?tace zonan daddy
Da mamakinsa yaje kusa da ita ya zauna
Ranqwashi takai masa tace kanajin Motsin zuwana shine ba kazo Kamin sannu da zuwa ba

Wajan ya riqe da hannun sa cikin shagwaba yace wayyo anty mufy kullum kikazo saikin min mugun ta

Daria suka bawa Amal, kamar wasu yan biyu shida mufy, Bata duba ganin wani matsayin sa kokuma girmansa, daukarsa take da gaske aqanin nata

Dariyar datake ne tafuto fili, yajuyo yace tashi mutafi

Momy tace haba daddy na, muna fira Ina kuma zakuje?
Anty mufy tace aiba inda zataje momy, rabu dashi

Dubanta yayi yace anty mufy unguwa zamuje, akwai Hospital dana bada aiki a ITAS da DARAZO zamuje, shine zamuje abudesu yau
Inda lokaci ma zamuje BALKACUWA zan duba aikin wani titi

Anty mufy tace haba daddy, mace cefa, jeka abinka

Momy tace a a suje mana, tayaya za’a Bude waje yatafi shi kadai, itama ai yau ta Dan zaka Garin ko
Ta dubi Amal tace jeki shirya ku tafi Amal

Cikin murna kuwa tace to momy tayi cikin daki

Firarsu suka ci gaba dayi, dayaga fira ta dauke musu hankali babu Wanda yasan yabi Bayan matarsa

Amal kuwa wani rantsatstsan less tasaka kalar green, Riga da zani ne dinkin rigar bubu akayi, tadora zanin Akan rigar ta daura, taja dankwalinta ta daura, daga baya ta fitar da gashin ta
Tadau sarqa tasaka, sosai tayi mugun kyau

Dakin yatura yashiga, ya tsaya daga bakin kofar Dakin, tsarki ya tabbata ga ubangijin wannan halitta

Kasa janye idonsa yayi akanta, ahankali yake takowa har zuwa Gabanta, hannayenta yakama yamatso da ita jikinsa, yashige jikinta kamar zata maidashi ciki, ya rungume ta tsam ajikinsa
Gabanta ne yafara faduwa tafara kokarin qwace jikinta, Kallanta yayi, ya kalli janbakin datasa yace Bana hanaki saka wannan abin ba? Kallansa tayi tace wanne Abu? Matso da fuskar sa yayi daidai Tata, ahankali yasaka harshansa yafara lashe lips dinta,matso da ita yayi jikinsa yakama lips dinta nasama yashanye tas, sannan ya shanye na qasan ma
Cika mata Bakinta yayi, Idanunsa yasauya kala yace gashinan

Abin nayau ya girmi tunanin Amal Dan haka takasa hada ido dashi

  ***       ***      ***

Acan falo kuwa anty mufy tace momy kinji Amal shiru, har daddyn ma yafita inaga, momy tace to dubota mana

Aikuwa takama hanyar Dakin, takama handle din Dakin zata Bude

Taji Amal nacewa Yaya daddy kabari please
Yace meyasa?
Cikin rawar murya tace banajin dadin abinda kakemin, wani iri nakeji ajikina

Gaban anty mufy yafadi, Karde yaran nan…. Kenan… Kenan ahaka suke zaune?

Dasauri tajuya tadawo falon tanata tausayin qanin nata, wannan wacce irin rayuwa ce suka zabarwa kansu?
Momy tace Ina take?
Cikin qirqirarran murmushi tace gatanan futowa momy

Acan daki kuwa daddy cikin ransa yace akwai aiki agabana kenan Dan haka yace Toshiknn nadena, Amma please gyara wannan daurin dankwalin ki maida gashin ciki saimu tafi

Babu musu ta gyara, sannan yakamo hannun ta suka futo

Anty mufy na kallansu aranta tace dacewa har dacewa Amma ace yaran nan haka suke zaune? To yanzu har tsawon wanne lokaci zasu dauka suna jiran babies?

Sukuwa dasuka futo zuciyar su daya sukayi musu sallama suka tafi

   ***      ***      ***

Tunda ga wannan lokacin anty mufy tafara gyaran shahida ciki dabai, zuwa take har daki tatuso qeyar Amal tazo tasakasu agaba tana basu magungunan mata, wani na tsugunno wani Nasha, wani na wanka, anan tasake tabbatar da zarginta Akan su daddy taqara yarda cewa babu abinda yashiga tsakanin su tsawon wannan lokacin
Kuma tagane hakanne ta yanda take basu maganin Amma Amal ko ahabar zaninta karba kawai take tana dirka

Hankalin ta kwance zata karbi komai tasha, inda ace wani Abu yafaru atsakanin su toda ba Lalle bane tayi tashan wannan magungunan, Koda kuwa tasha to zatace tasan wani, haka anty mufy tayi ta gyaransu duka duka su biyun

Ita inda ace tasan haka suke zaune aida tuni tazo cikin dabara da wayo Tasa komai ya wakana, Amma su nan suna nan sun saki baki suna jiran yara ashe jiran gawon Shanu suke

  ***      ***      ***

Yau Bayan sungama break fast, Wajan yarage saura anty mufy da momy da Abba

Momy tace alhaji nifa al’amarin yaran nan tafara damuna, har yanzu de shiru mukeji, kuma Naga alama daga Amal din Har shi daddy babu Wanda yadamu, ko ajikinsu

Daria ce taso qwacewa anty mufy, to taya za’a samu yara? Aiba Rana

Abba ya ajiye spoon din hannunsa, ya dubi momy yace hajiya ai likita ya Riga daya dubasu yace suna lafiya, saide idan ita Amal din ta samu lokaci saita sake rubuta musu maganin dana taba karbowa marigayiya har aka dace

Momy tace au Wai kana nufin ita dince tabada maganin? Abba yace agabana mahaifinta yasa ta rubuta, kuma ta rubuta su daddy sukaci aka samu cikin

Momy tace Amma alhaji kasan da hakan kayi shiru muka zuba musu ido? Aini da nasan hakan da tuni nasa ta rubuta agabana ta dafa da kanta sunci

Abba yace Bayan wannan hayaniyar bikin zansameta inyi mata magana insha Allah

Momy tace to Allah yakaimu
Yace yaushe zaku wuce Dubai dinne?

Tace gobe zamu wuce da shahidan tazabi wanda take so, sai mufeeda da daddy yaturo mata kudin komai ita kuma zata hado lefan da sauran abubuwan buqata

Yace Toshiknn Nima zanje Abuja bazan wuce one week ba insha Allah, dukansu sukace to Allah ya kiyaye hanya

  ***      ***      ***

Washe gari su Momy suka tafi, tunda suka tafi gidan yarage saisu biyu,saikuma ma’aikata dasuke nasu bangaren, darana daddy yana office dazaran yadawo da daddare Amal ta rufe kofa, tun yana zuwa harya hakura yadena zuwa Dakin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button