BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daddy yace jb bakasan zama, yau kana nigeria to gobe za’a ji ka koma India

Murmushi yasaki yace Toya za’ai tunda sunqi saki na, sun riqeni

Daddy yace to yayi kyau, duk abinda kake de Toya kasan ce nanda 8 months kana nigeria saboda alokacin zan zama baba

Wai da gaske kake? Allah mutumina kace harta harbu

Daddy yace wato kafara shaqiyancin naka, nide nafadama lokacin nayi ka tattaro kadawo gida

Jb cikin farin ciki yace ai dole, Amma fa abokina gaskya kodan wahalar danasha wajan neman Amal yaci ace sunana zakasa idan namiji ne

Murmushi kawai daddy yayi yakashe wayar

Amal duk tana kallansa, tana farin ciki

Number Shahid yakira, shahida ta daga, Bayan sun gaisa ne yace Mata Ina shi shahid din?
Tace Yaya gashinan yana bacci

Yace to ki fada masa antynki ta samu ciki, kifadawa su umma ma

Cikin ihun murna shahida tace wayyo Allah anty Amal

Ihun murnar datake ne yasa Shahid tashi daga baccin dayake ajikinta

Yace fiancee lafiya kuwa? Sake rungume shi tayi tace fiance anty Amal ta samu ciki, yanzu Yaya yakiraka yace nafadama

Murmushi yasaki yace alhamdullahi, Amma gaskya nayi farin ciki

Tace sosai ma, nakusa zama momy

Harararta yayi yace ko? Tace emana

Yace no ban yarda da wannan maganar ba, Nima nawa nakeso

Kasa tayi da idonta, Dan Bata manta karonta dashiba

Cikin sauri ta tashi, ganin yanayi mata wani irin kallo, tace bari inje in sanar da ummatah, ta tashi tafice da sauri, yabita da kallan qauna

   ***       ***       ***

Next day
Sunyi kyau sosai cikin manyan kaya, yaruqo Hannunta yar wajan umma, shahida Sai janye Hannunta take, Amma Shahid yaqi sakinta, saida sukaje har wajan umma
Umma na kallansu aranta tace wannan rashin kunya ta yara yan zamani dayawa take

Ta kawar da kanta kamar Bata gansu ba, har qasa suka tsugunna suka gaisa, Shahid yace umma zamu wuce, tace a a basai gobe ne tafiyar ba? Yace a a umma gara muje yau din Dan mu qara tayasu murna

Umma ta dora Hannunta ahabarta, tace Shahid kamar akanku aka fara haihuwa? To duk Dan da aka cika so baqin jini yake

Gaba dayansu sukasa daria

Shahida tace umma karfa yazo ki ganshi gaba daya ki rikice, kice saishi

Umma tace a a ku riqe abinku banayi

Shahid yace ai umma ba wannan maganar ce kadai zata kaimu ba, har maganar aikin nan da Abba yayimin

Tace Toshiknn, gaskya Kam gara kuje din, Allah ya kiyaye, idan babanku yadawo saina fada masa, inyaso kaima saika kirashi awaya

Yace to umma

Ta kalli shahida tace yata ki kula da kanki sosai kinji? Shahid yayi saurin cewa umma nikuma banda ni?

Umma tace Dan Allah ku tafi Shahid

Haka suka futo harabar gidan, da kansa yabude mata gaban motar tashiga sannan yazagaya yajasu suka dau hanya

    ***       ***        ***

Yaya daddy Dan Allah kafita daga Dakin nan, su Momy fa suna falo, karsuyi tunanin wani Abu muke
Qugunta yakama yana daga Bayanta, ya rungume ta, ya dora kansa awuyanta yace shikkenan ma kinga nahuta idan suka fahinci wani abun din, basu ne suka San yara ba

Tace to ai ansamu, Dan Allah katashi ka shirya kashiga office, Nima indomie nakesan dafawa, ita nake sha’awa

Yace no karkiyi da kanki, zan fadawa momy Sai Tasa ayi Miki

Tace Yaya daddy banajin dadin na masu aikin, inaso ne inyi da kaina

Yace Toshiknn

Wayarsa ce tayi ringing, yana dubawa yaga Abba ne me Kiran
Yadaga wayar yace yau ka manta da fita office ne?

Babu kunya daddy yace ah… Abba dama yau bazan fita ba

Abba yace ok to shikkenan

Amal ta kalleshi tace meyasa zakace bazaka ba, idan Kuma wani Abu yataso fa? Yace nariga nasanar dasu yau bazan shiga ba, yarinyata tace in zauna inbata kulawa

Cikin mamaki tace wacce yarinyar kenan? Cikinta yashafa, yace gata acikin nan

Murmushi tasaki tace to Bari inje inyi girki na

Kallanta yayi, cikin shagwaba yace please baby, kawai gaisawa zamuyi da babynah, tace Amma Kuma Yaya daddy su umma fa….

Shima kan gadon ya nuna mata yace please ko Yaya ne

Yakamata Hannunta suka yi gadon, daga nan suka Lula duniyar ma’aurata, inda Amal taji dadin abin sosai, shikuwa gogan baisan Ina kansa yakeba, Jin tasake wani irin dadi

Saida komai yalafa,tace my dear yunwa nakeji, kuma kahanani yin girki da wannan gaisuwar

Yace sorry baby na wallahi ke dince, ta daban ce, bari inje in dafa miki da kaina, aide indomie ce ko? Tokinsamu yanzu

Yatashi yayi toilet domin wanka, Amal ta bishi da kallo Itade tasan cewa bai iya komai ba, Amma tayaya zai iya dafa wata indomie, Amma bari tazuba masa ido

Yana futowa daga wanka, yashirya yace tashi Nakai ki toilet din, kiyi wanka, kafin ki futo indomie tana jiranki

Sarai zata iyayin komai da kanta Amma saboda ya dauke tan ta miqa masa
Hannayenta, yadauke ta yakaita toilet din, sannan yafice

Yana zuwa falo Sai momy ita kadai, tana kallan labarai

Taga yayi kitchen da kansa, ta daga murya tace wani Abu kake buqata ne? Keyarsa ya Sosa yace a a momy Amal ce takesan indomie, shine nace bari inyi mata

Momy aranta tace ikon Allah sabon Salo, to Bari muga wannan girkin yanda zai qare

Afili tace Toshiknn, Allah yabada sa’ah
Aikuwa babu kunya yajuya yashige kitchen din

Yana zuwa yadauki tukunya, ya wanke ya dora sannan yadebo ruwa yazuba saura kadan ruwan yakai Rabin tukunyar
Yadauko noodle din guda daya babba yabude yasaka acikin ruwan, magin daya gani aciki yabudesu duka biyun yazuba, yadebo salt yazuba, sai mai

Yana rufewa kuwa tafara tafasa, ya tsaya harta dahu, yadauko flet yajuye aciki, duk ruwa yacika indomie din, gata tayi fari fat

Yadauko yafuto falon, alokacin Amal harta futo falon itama, har Gabanta yakai mata abincin yace sauko kici gashinan

Ta kalleshi ta kalli indomie din, tace to

Momy dake gefe tana kallansu

Amal aka saka hannu zuciya daya, takai indomie Bakinta, cikin sauri ta furzar, tace Yaya daddy gishiri

Wacce irin indomie ce wannan?

Ta dauke flet din tayi kitchen dashi, Shima tashi yayi yana Sosa kansa zai bita kitchen din, yakai kallansa ga momy yaga dariyar ta take ita dakai

Yana shiga kitchen din yaga ta ajiye indomie din ta dora wata, ya kalleta yanuna mata wadda ya dafa din, yace wannan din bayarwa zakiyi?

Kallan mamaki tayi masa tace, ai babu Wanda zai iyacin wannan indomie din, duk wanda yaci kuwa to mutuwa zaiyi, gishirin dayake cikinta, shine zai kasheshi

Kansa ya kawar, yayi shiru

Yana gani tadafa wata, sannan taja kujera a kitchen din tafara ci, Shima dayaga haka, saiya dauki Tasa yasa spoon aciki yadiba yakai bakinsa, ai tuni ya furzar yana yamutsa fuska, ruwa yanema yasha

Sannan yaje wajanta yasa hannu sukaci tare

Sunkusa gamawa sukajiyo karadin shahida, aikuwa dukansu sukayo falon

Shahida na ganin Amal taje da gudu ta rungume ta, daddy yace ke kalau kike kuwa? Kiyi mata ahankali mana
Saida yafada ne sannan yajuya yaga momy da Shahid suna kallansa

Saiyayi fuska kamar ba shine yayi maganar ba yanemi waje ya zauna

Momy ce dakanta taje Tasa aka shirya musu lafiyaiyan abinci, sunaci shahida tanata tsokanar Amal

Bayan sun gama ne momy takira Abba awaya, yana zuwa suka sake gaisawa sannan yabawa Shahid opper sa, sosai yasake murna da godia

Abba yace ai babu wata matsala ko? kunada kudi cikin account? Shahid yace eh Abba akwai 7 millions

Murmushi su na manya yayi yace ai bakwa kashe kudin ma Shahid, kuyi abinda ranku yakeso fa, zuwa gobe ma insha Allah zansa aturo muku wani kudin

Dagashi har shahida ne wannan Karon sukai masa godia, sannan Shahid yace ai mungama magana da baba ma, yace nadauketa mudawo nan din saboda aiki, saimu dinga tafiya can muyi weekend

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button