BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abba yasake murmushi yace Toshiknn Allah yabada sa’ah

Dukansu sukace amin

Saida suka wuni agarin sannan sukai haramar tafiya jigawa, inda zasuyi shirye shiryensu sudawo

 ***      ***       ***

After 2 week’s

Suna zaune afalo dukansu, daddy Sai zungurin Amal yake, yana kyafta mata ido, yana nufin ta tashi su tafi daki

Ita kuma taqi tashi, yana sake zungurin ta saita juya masa idonta, tana nuna masa su Abba

Alama yayi Mata da kansa ta tashi su tafi, haka ta sunkuyar da kanta, tadena kallan sa

Basusan Abba da momy duk suna ganin su ba

Wayar daddy ce tayi qara, yana amsawa daga daya bangaren akace yallabai yau ne zakuyi wannan meeting

Kansa yashafa yace meeting? Kaga a daga shi zuwa next week
Yakashe wayar

Abba yace ba meeting zakayi da wasu ba?

Kansa ya Sosa yace yace Abba dama Yan majalissar jiha ne zamuyi meeting dasu

Abba yace to ai babu dadi karya alqawari, yakamata katashi katafi

Babu yanda ya iya haka yatashi jiki ba qwari yashirya yafita

Amal na rakashi itama tayi Dakinta

Momy tayi Ajiyar zuciya tace alhaji Yaron nan bayasan fita office yanzu, narasa dalili

Abba yace to tsakaninsa ne da iyalinsa

Momy tace to ai idan yafita itama yarinyar kanta zata Dan huta

Murmushi Abba yayi yace Toya za’ai, aide batada damuwar komai ko? Momy tace babu komai alhaji

Washe gari da daddare suna gama cin abinci suka yiwa su Momy saida safe zasu tafi Abba yace kudawo dama inasan magana daku

Dawowa sukai suka zauna Abba yace nasa ashirya min ma aikata tareda doctor’s guda biyu mata, Amal zata tafi Malaysia domin renon cikinta
Saboda nan din inaga hayaniyar mutane zata dameta

So angama komai zaku iya tafiya gobe ko jibi idan ka sanar a office, idan ka rakasu saika dawo bakin aikinka

Comments
Comments

Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

27

Gaban daddy ne yayanke yafadi, wacce irin tafiya kuma yana Zaman zamansa da matarsa?

Amal ma jikinta yayi sanyi dajin furucin Abba, to Amma Yaya zatayi dole zata hakura da mijinta tabi umarninsa tunda kamar mahaifi yake awajanta, dole akwai abinda ya hango shiyasa yafadi hakan
Dan haka ta yunqura zata tashi taji caraf daddy yariqe Hannunta
Hannun nasa tabi da kallo sannan ta zauna

Daddy yace Abba mungode da hukuncin daka yanke akanmu, Amma Abba banqi takaba, saide Ina neman alfarma daya awajanka, wallahi Abba zan Bata ko wacce irin kulawa, insha Allah Babu abinda zai faru, Abba nayima alqawari, nide kar’arabamu

Abba ya kalli momy tareda ajiyar zuciya, Lalle zamani yazo qarshe, rashin Kunya qiri qiri

Sannan yace to ai babana Nima ba komai ne yasa nace hakanba, Naga ita yarinyar zata samu hutu babu hayaniyar jama’ah, sannan Kai kanka zakafi tsaida hankalinka waje daya game da aikinka

Momy tace hakane Kam, kaga daddy bakasan fita office tun daga yanzu ma da Amal ta samu ciki

To kuma idan ta haihu inajin tattaro komai naka zakayi ka zauna agida, karfa ka manta haqqin mutane ne akanka kakula dasu, nasan cewa Amal itama haqqinta na kanka but su jama’ar Gari alqawari kadauka zaka kula dasu kabawa kowa haqqinsa

Shekaran jiya ba kaje office ba, kuma babu wani dalili me karfi, sannan jiya meeting kansa zakuyi Amma Babu kunya kace a daga daddy

Haba babana, Allah fa dole zaiyima tambaya Akan hakan

Shiru su daddy sukayi, maganar momy gaskya ne, Amma tayaya suke tunanin zai iya rayuwa batare da Amal ba? Matarda bikin qawarta za’ai makusanciya Amma yahanata Koda kwana daya ne, sai a ranar sukaje suka dawo, tayaya zasuyi wannan tunanin?

Abba ne ya katse musu tunanin da fadin to kunji wasu daga cikin dalilan dazaisa tatafi

Daddy yace hakane Abba, insha Allah zan kiyaye, wallahi kullum zan dinga fita inde Akan office ne, ni wallahi kafin ku tashi daga bacci na nafita

Gaba dayansu babu Wanda bai murmusa ba Akan maganar daddy

Abba yace to ai shikkenan, ku tashi ku tafi, Allah yayi muku albarka
Suka amsa da amin

Amal tayi hanyar Dakinta, Shima daddy yabi Bayanta, tunawa yayi da iyayensa suna wajan a zaune, Dan haka cikin Sosa qeya yadawo Shima yanufi hanyar dakinsa

  ***       ***       ***

Washe gari da safe suna breakfast gwanin sha’awa su hudu, momy ce dakanta ta zubawa kowa, saboda batasan Amal tayi aikin komai, kowa yanacin abinci ahankali cikin nutsuwa Amma Amal hannu baka hannu qwarya takeci
Tas ta cinye nata, tadau flet tasake zuba wani

Daddy yazuba mata ido yana mata kallan mamaki, wanna wanne irin cin abinci ne?
Abba ma da kansa saida yayi mamaki
Amma Kuma babu Wanda ya tanka acikinsu

Wanda ta zuba dinma tasake cinyewa, momy tace a a yata yaude kice bakyajin qarnin

Cikin murmushi tace eh momy banajin…. Bata qarasa maganar datake ba taji wani irin Amai yataso mata

Aguje tayi hanyar Dakinta, tana rufe Bakinta

Daddy ya kalli iyayen nasa, yatashi Shima cikin sauri yabi Bayanta

A toilet yasa meta tanata Amai, yakamata ya riqe saida tagama, yatayata tagyara jikinta

Sai numfashi take saukewa kamar wanda tayi gudu
Agefen gadon ya sauketa yanayi mata sannu

Kawai kanta ta daga masa, ta kwanta ahankali gamida rufe idonta
Momy ce ta turo kofar tashigo tareda Abba, sannu suka sake yimata

Abba yace babu abinda yake miki ciwo de ko? Tace babu komai Abba

Momy tace to ai kinyi Amai Amal, nasan babu komai acikin ki, me kikeso adafa miki?

Tace momy babu komai, idan naci ma Amai zan sake yi, yanzu ma ji nake

To Amal zama haka ai bazai iyuba, ko tea ne bari inje inhado miki

Cikin sauri tace momy ni banason tea
Momy tace Tome kikeso?
Kai tsaye tace goruba

Momy ta kalli daddy dayake tsaye, tace to Kai kaji

Daddy yashafa lallausar sumar kansa, shi yanzu Ina zaije yasamo wata goruba? Toshi rabon dayaga goruba ma ai tun yana yaro qarami

Abba ne yasake dubanshi yace kaje Kasa asamo mata, sannan ya kalli momy tace hajiya ni zan fita, idan akwai matsala ayi saurin sanar Dani ta waya, zan turo doctor tasake duba Jikin nata

Momy tace to alhaji Allah ya kiyaye hanya

Abba tare suka fita, shida daddy, Abba nafita daddy yakira daya daga cikin ma’aikatan gidan yace yana son anemo masa goruba
Mutumin yace to yallabai za’a same ta insha Allah
Hannu yasa cikin aljihunsa, mutumin yayi saurin cewa haba yallabai
Ai karka damu, wallahi Bana buqatar kudin komai awajanka, wannan ai Abu ne na marmari

Bari inje asamo, daddy yace no please karbi kaje

Babu yanda mutumin ya iya haka ya karbi wannan uban kudi awajan daddy

Har zai tafi daga falon daddy yace masa please dayawa nakeso, mutumin cikin girmamawa yace angama yallabai

Ajiyar zuciya yasauke yakoma Dakin nata

Bai dade da zuwa ba doctor hauwa taqaraso
Duba Amal din tayi sosai, sannan Tajuyo ta kallesu tace hajiya wannan aman dama dole ne saitayi shi, Amma kada ku damu zuwa Dan wani lokacin zata dena

Ta dubi Amal tace ranki yadade ai kina iya cin abinci ko? Tace inaci sosai doctor, ni abincin danake Cima yayi yawa, kamar me cutar yunwa

Daria doctor tayi tace to hakuri zakiyi, baby ne Shima yakejin Tasa yunwar Bayan taki

Yanzu bari nabaki wannan maganin insha Allah zai temaka miki wajan rage aman dakike

Godia sosai sukayi mata sannan tafice

Futowa momy zatayi daga Dakin, Amal ma tabita, momy tace bazaki huta bane Amal? Ki kwanta ki huta

Tace momy babu abinda nakeji, muje falon

Daddy ma abaya yabisu, suna Zuwa falon momy tabata magungunan tasha

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button