BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Safna abdulrashid daya daga cikin daliban tace Amal, ashe jiya baban ku yaje har gida yayiwa Malam nura kashedi Akan kinayin acuci maza

Yuuuuu kallo yadawo kan Amal, cikin mamaki tace baba kokuma Yaya Shahid? Ni ban fadawa kowaba Sai yayanah

Safna cikin sanjin gulma tace um aikuwa ya kyauta Dan yayi mana maganin wulaqancin Malam nura
Kafin inyi magana shugaban makarantar yashigo tare da wasu daga cikin malamai cikinsu kuwa harda Malam nura, idonsa qur akaina
Dana lura ni yake kallo saina sunkuyar da kaina
Ba’a dauki tsawon lokaci mai tsawo ba, shugaban makarantar ya shaida mana cewa kowa yaqara dagewa yayi gyaran karatun sa dakyau saboda Ana gab dayi mana bikin sauka

 ***     ***     ***

Wai alhaji kunsha hanya, sannunku
Tafadi haka yayinda take kokarin cire masa malun malun din jikinsa

Abba yace ai hajiya tafiyar akwai Nisa, Wai ahakan ma danma ba’a Mota mukaje ba, Amma tsakanin Garin da inda muka sauka tafiyar akwai yawa, gashi hanyar tasu tana buqatar gyara

Momy juwairah tace to sannunku alhaji muje kayi wanka kahuta, kafin ya miqe yace ga wannan

Kallan hannun nasa tayi tace alhaji qwan menene wannan? Yace shine abinda muka Sha wannan baqar wahalar akansa
Yace suci shida matarsa, da iznin Allah za’a samu abinda ake so, momy ta dinga juya qwan tace ikon Allah

To Bari gobe Sai akai musu, daga mata hannu yayi yace haba hajiya, kirasu yanzu kisa masu aiki su dafa suci su tafi

Nizan shiga ciki in watsa ruwa in kwanta
Babu abinda zan musu ayanxu alhaji Sai Bayan munje nayiwa mijina hidima tukunna

Da murmushi ya kalleta, itade akoda yaushe cikin kula dashi take, Bata nuna gajiyar ta Akan hakan, Koda yaushe tana cikin kwalliya da kalamai masu dadi ga mijinta

 ***     ***     ***

Amal gashi inji Malam nura yace nabaki, takardar hannun ta na kalla nadafe kirjina da hannun na, tace nashiga uku maisah ko takardar korata ne daga makaranta? Nashiga mezan cewa baba
Nafadi haka idonta na cikowa da qwallah

Takardar ta fizge zata Bude ta karanta, maisah ta dakatar da ita da fadin a a karki Bude a gabana idan kinje gida kin nutsu saiki karanta idan munsake haduwa saiki ban labari, Amma ki kwantar da hankalin ki, insha Allah Babu matsala

Ajiyar zuciya nasauke nace to maisah, nagode qawata ta Gari
Hararata tayi tace ni muje, baquwar haure kawai, qilama zuwa kikai ki zautar mana damalami

Ku dama yan agadaz dinnan haka kuke, da anganku shikkenan nutsuwar bawa tatafi

To yar qasa, munji, kuma babu inda zamu, kullum Ina fada miki damagaram kina kaini agadaz

Tace edin can zan kaiki, Gaba nayi nace kanki akeji

Takusa qarasawa gidansu kawai sai ganin mutum tayi agabanta, subhanallah
Haba Yaya sham, wallahi kaban tsoro
To yakike so inyi tauraruwata?
Koda yaushe bamuda ikon yin magana agida saide aboye?
Kinga Amal wallahi nagaji, sanki yana neman zautar Dani, kibani dama inturo iyayena gidanku ayi magana

Yaya sham, kasan de banda ikon yin hakan ayanxu ko? Meyasa Amal? Yafadi hakan kamar zaiyi kuka
Tace saboda yayanah yahanani sauraron kowa, sannan Yaya sham yanzu Ina tulawa bamuyi saukaba, tayaya kake tunanin zanje wa da baba wannan maganar?

Kallanta yayi da mamaki yace Amal Anya kuwa kina sona kamar yanda nake sonki? Yaya sham trust me wallahi I really love you
Amma kabani dama zuwa Bayan saukarmu, insha Allah zan gabatar dakai awajan baba, nasan cewa baba yana sona, zaiso abinda nakeso

Yauwa kokefa, to yanzu Sai yaushe? Very soon zamu hadu karka damu kaji Yaya sham din Amal
Murmushi yasaki Dan yaji dadin sunan sosai
Yace shikkenan bye bye
Dahaka suka rabu

 ***     ***     ***

Salma banaso, please kibani fillo nah

Gwalo tayi masa tace ow nahanashi kazo ka qwace, in kacika mai karfi, kokuma duk wannan dantsan kawai na adone?

Kallanta yayi, shide yasan idan yace karfi zai sa mata to da tuni ya qwace

Fillon ta sake dauka ta wulla masa, Shima yadauka yarama, sunata nishadi abin su, ta jefo masa Shima yarama, tace ko yanzu de nasa kadan motsa bakinka, haba mutum ya zauna shiru haka

Kallanta yake da tsadaddan murmushinsa mai kashe mata gabban jiki, yace aikuwa mai ganin surutu na, sai sabuwar amaryata
Nan da nan ta dauki fillon ta jefeshi dashi tace Allah a a, baka isaba
Yana kokarin ramawa, momy ta futo da filet ahannunta

Nan da nan suka nutsu gaba dayansu

Salma ta sauka qasa cikin sauri tace momy barka da futowa
Ba yabo ba fallasa ta amsa da “yauwa”

Shima ya gaida ta,ta meqo musu filet din tace gashinan kuci

Daddy ne yakarbi filet din, ganin wainar yar kadan ce yasa shi maiqawa salma
Tome zaici meze Bata anan?
Salma tayi bissmilla tafara ci
Kallansa tayi babu alamar wasa afuskarta tace Kai karaam bazakaci bane?
Yau baiga fuskar dazaiyi shagwaba ko tambaya ba, Dan haka baiyi wata wata ba yasa hannun suka cinye qwan

Amma cikin ransa fadi yake qwai Dan millili haka saikace gidan yunwa
Kuma ace mutum bai Isa yayi maganaba?

 ***     ***     ***

Gaskya abinda na fahimta gameda kalamansa shine, yana baki hakuri ne Akan wani laifi dayayi miki, sannan Kuma yana buqatar ku qulla qawance tsakanin ku
Tace to dama Ana qawa da namiji Yaya?
To shide ga abinda yace nan, meyasa kike cire niqab dinki Bayan kinbar gida? Cikin tsoro tace Allah yaya bancire ba
To baki cireba tayaya akai yaganki har zai turo miki da wasiqa?
Ai shikkenan kiyi yanda kikeso rayuwarki ce, niyyarki ne ki amince, kokuma akasin haka
Tashi yayi yashiga ciki, gabansa yana mugun faduwa

To Wai ita Dan Allah me Yaya Shahid yake so tayi? Itada tazo domin aqara yimata bayani Akan hausar, kuma zaiyi fishi yatafi?
Kuma yace ta amince ko karta amince

Wullar da wasiqar tayi, tabishi abaya

 ***    ***    ***

After 3week
Salma!
Yakamata ki tashi ki hada mana break fa inaso zan fita

Juyi tayi daga cikin lallausan blanket dinsu, domin kuwa basu taba Raba wajan kwana

My dear wlh banjin karfin jikina, bazan iya tashiba, please zo

Matsowa yayi wajan ta da mamaki, kafin yayi magana ta janyo shi jikinta tana shaqar turaren daya fesa

Jikinta yaji zafi rau, da sauri yace subhanallah, wayarsa yadauka yakira family doctor dinsu, ita kuwa tana jinsa tayi luf ajikinsa

Doctor yana zuwa yaduba ta, ya tabbatar masa da cewa tana daukeda juna biyu na Tsawon sati biyu

Daddy daskarewa yayi awajan, Yama rasa da bakin dazaiyi magana

Doctor ma yalura da halin dayake ciki Dan haka yadafa kafadarsa yana murmushi yajuya yafita
Yana fita daddy yakaiwa Salma wata wawar runguma

Yasake ta yayi sujjada yagodewa Allah, yasake dawowa ya rungume ta, ita Yama Bata daria wallahi, Gaba daya ya cukwikuya babbar rigar sa

 ***     ***     ***

Malam dama zuwa nayi in qarama godia Akan maganin daka bani, gaskya naji dadi sosai, OKASHA yana Nan yashiryu yadena shaye shaye, Babu ruwansa yanzu wlhy Abu yayi kyau sosai yanzu hakama karatu nake San turashi qasar waje

Baba hamani yace ahhh Abu yayi kyau alhaji, haka ake so ai
Shahid ne yashigo Bayan ya gaida alhaji yace baba ga mukullin shago zanje filin ball
Yace to Shahid saika dawo
Yana fita alhaji sidi yace a a Malam dama kanada yaro babba haka?

Baba hamani yace danmu biyu ne ai alhaji, Shahid ne babba Sai Amal, itada Tayi diploma, shikuma yayi NCE anan kusa damu Gumel

Alhaji sidi yace gaskya nayaba da hankalin sa sosai Malam, inaso kabani takardunsa sannan Kuma kabani dama inturashi Indonesia karatu shida Dan wajena okasha

Fara’ah ce ta bayyana afuskar baba hamani, yadinga yiwa alhaji sidi godia

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button