BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abari tukunna har cikin yayi qwari, Amma Awannan lokacin gaskya idan aka matsa cikin zai iya fita

Daddy cikin sauri yace babu komai doctor insha Allah za’a kiyaye, Abba yasaki murmushi ganin daddy yagano dalilin dayasa tun farko suka so tura Amal wani qasar daban

Miqewa yayi yace doctor zan iya ganinta? Tana murmushi tace ranka yadade tana buqatar hutu yanzu saide nanda awa uku haka

Yace ok babu damuwa

Gaba dayansu suka futo, basu koma gida ba saida lokacin da doctor ta diba yacika
Sannan suka shiga Dakin

Suna shiga daddy yayi saurin qarasawa gadon, idonta biyu, da murmushi ta tareshi, hakanne yasake kwantar masa da hankalin sa

Yace baby yajikin naki? Tace lafiya Yaya daddy banajin komai yanzu, saide yunwa, ta qarasa maganar tana daria

Shima dariyar yasaki yace karki damu, da kaina zan dafa miki abinda kikeso kinji?

Daria tasaki tace tab gishirin zanci

Abba ne yayi gyaran murya ganin kamar basusan da mutane adakin ba, hakanne kuwa ya fargar dasu

Cikin kunya daddy ya matsa daga gadon kadan yakoma kujerar dake gefe ya zauna ya zuba mata Idanu

Momy tace sannu Amal, cikin murmushi tace yauwa momy
Abba yace bakyajin komai de yanzu ko? Tace Abba kalau nake jina babu damuwa, kawai mutafi ciki, banasan Zaman nan wajan

Abba yace to alhmdlh, Allah yaqara kiyayewa Amma de kibari ki sake hutawa tukunna

Doctor hauwa ce tashigo ta dubi Amal tace ranki yadade babu damuwa de ko? Tace babu damuwa doctor banajin komai yanzu

Cikin murmushi ta dubi daddy tace to ai zaku iya tafiya ma

Abba yace eh haka tacemin ma Wai mutafi batajin dadin nan din

Shine nace tabari tasake hutawa tukunna

Doctor tace ai alhaji Babu damuwa zata Iya tafiya dakanta ma, munyi mata allurai

Abba yace to alhmdlh
Allah yaqara kiyayewa de, dukansu suka amsa da amin

Amal tafara kokarin saukowa, daddy yayi saurin matsawa kusa da ita yace idan bazaki iyaba na daukeki

Ba doctor kadai ba, hatta iyayen saida suka murmusa, sosai suka birge doctor, yanda suke kula da junansu

Amal tace Yaya daddy Allah zan iya

Yace to taka mugani, daria Tasa sannan takama hannun sa suka futo daga Dakin

Momy ta rungume ta ajikinta, suka yi Cikin gida

Suna qarasawa ciki momy ta dubi daddy tace kuje daki, bari naje nakawo mata Dan abinda zata ci

Daddy yace to momy
Suna shiga Dakin kuwa ya kwantar da ita a gado, Amal tace ni narasa wannan lallabawa dakakemin Yaya daddy nace ma lafiya kalau nake jina
Zama yayi akusa da ita yakama Hannunta ya riqe, yace baby kiyi hakuri, Naja miki rashin lafiyar da takusa Tasa mu rasa babyn mu

Cikin alamun tambaya tace kamarya? Me kake nufi?
Saida yayi kissing Bayan Hannunta sannan yace doctor tace abinda mukayi dazu ne yasa kika fara zubar da jini, tacema Wai da bamu kaiki da wuri ba datuni kinyi bari
Shiyasa nake sake baki hakuri, Akan abinda yafaru, nasan kinsha wahala sosai, Amal tasaki Ajiyar zuciya tace
Yaya daddy dama haka ake bari?

Shima cikin tausaya wa yace hakane baby, tun lokacin da momy tace kina zubar da jini gabana yafadi, saboda nasan cewa mun Riga da mun rasa babynmu
Amma Sai gashi Allah cikin ikonsa ya tsayar dashi, Babu abinda da zance da ubangijina Sai godia

Amal tace to Yaya daddy, ni ai banga wani laifinka anan ba, Abu ne wanda ni dakai babu Wanda yasan hakan zata faru aida bazamuyi ba

Daddy yace shiyasa yanzu na daukarwa kaina alqawarin hakura, har Sai lokacin da cikinmu yayi qwari, baby shekaru qaruwa suke, ina zaune banida da ko daya nawa

Allah Bai rageni da komai ba saita wannan fannin, kuma gashi yadauka yabani, yaushe zanyi sakaci dashi?

Tace hakane Kam Allah ya kiyaye gaba, yace amin baby nah

Yanzu saura wata bakwai ki haihu, Inga jini na aduniya Nima, cikin mamaki tace Wai har qirgawa kake?
Shima cikin mamaki yace kinsan yanda na matsu Inga me zaki Haifa mana kuwa baby? Ai qirge yazama dole, sannan Ina roqon Allah yasa suyi kamarki

Amal tace meyasa Yaya daddy? Bayan kowanne uba yanasan yayansa suyi kamar sa

Cikin sauri yace a a banda ni baby, nafisan suyi kamarki, wallahi zanfi sonsu ma Allah yagani

Daria yabata sosai, tana cikin daria kuwa momy tashigo da farfesun kaza ahannun ta, ta kalli daddy tace wato kana nan kana damun ta

Yace momy kawai labari nake Bata, momy tace to naji, yata tashi Kisha farfesun nan, Amal tace to momy

Flet din daddy yadauko yasa a Gabanta yasaka spoon yafara Bata da kansa

Murmushi momy tasaki tafice daga Dakin, wannan rashin kunya ta daddy Sai shi

   ***       ***     ***

Next day

Anty Amal yajikin naki? Ajiyar zuciya tayi tace lafiya anty shahida, ai naji sauqi
Mayafinta tacire tace wallahi da momy tafadamin jiya bakiji yanda naji ba ga fiance baya nan, bare mu taho
Nide na keta tunani

Amal tasaki murmushi tace inye au fiance

Shahida tayi murmushi tace nide yanzu Dan Allah Babu abinda kikeji? Wallahi Bama San abinda zai taba lafiyar babyn nan

Amal tace to kema saiki dage ki samo mana wani

Ajiyar zuciya tasauke tace anty Amal kenan nifa auren nan yafara isata, ace kullum cikin Abu daya, Allah nagaji

Me Amal zatai inba daria ba

Tace aikuwa haka zakiyi hakuri kibar yayana yayi abinda ransa yakeso, ni Sanadin hakan ne yasa jiya na kwanta jinya

Shahida tace Wai Dan Allah da gaske?
Tace wallahi anty shahida

Jinjina Kai shahida tayi tace to ai ke dince duk kin haukata mana dan’uwa, ba dole ba

Amal tace bawani hauka, kawai de Allah ne yakawo

Shahida tace to Allah yasawaqe, yasaukeki lafiya, tace amin sis
Saida suka wuni agidan itada shahid sannan suka tafi gidansu

  ***      ***      ***

Me ciki kwana biyu
Daga bangaren ta tace maisah yagida ya amarci
Lafiya kalau Amal, yagida yasu baban baby?
Au har ya zama baban baby? Maisah tace to me za’a jira
Kede kawai yanzu kowa ke yake jira ki haifo mana musha bikin suna

Gaskya ne Bama tani kukeba ko maisah?

Maisah tace sorry qawata, kema kinsan kece first ai, kamar yanda kike first lady

Daria tasaki tace to nagode kema ya angon naki, maisah tace yana lafiya wallahi

Ganin shigowar daddy ne yasa Amal tace to Dan Allah ki gaidashi, sai mun sake waya

Maisah tace to zaiji bye

Qarasawa tayi ta karbi jakar hannun sa, tace sannu da zuwa Yaya daddy yace yauwa baby

Bani paper da biro please

Cikin mamaki tace to lafiya? Yace kede yi sauri

Daki tashige ta dauko joter da biro tace masa to gashi

Janyo ta yayi dab dashi ta zauna, sannan yadubeta yace yauwa me kike ganin yadace muyi oder na baby ne?

Ajiyar zuciya tasauke tace yanzu Yaya daddy haihuwar daba yauba ba gobe ba? Sannan Kuma nasan su Momy mafa zasu Sai komai

Kallanta yayi yace kema kikace su Momy, wannan kuma na baban baby ne da kansa
Ya sunkuyar da kansa yana jero kayan yara, ta kalleshi tace to yanaga kana saka bibbiyu?

Yace eh idan namiji ne kinga gashinan ansiya, idan mace ce ma itama gashinan
Idan Kuma dukansu Allah yabamu shikkenan kinga mun huta

Daria tasaki tace Dan samu har yara biyu? Yace to shikkenan kina wasa ko?

Yadaga hannun sa sama yace ya Allah kabani yan biyu

Cikin sauri takamashi tana sauke masa hannun sa qasa, tace a a Yaya daddy wallahi akwai wahala

Rubutun sa yaci gaba dayi, hatta takalmin da zasu saka da keken koyon zama, dana koyon tafiya, Babu abinda yabari
Amal na kallansa tana murmushi

   ***      ***      ***

Babana yakamata kadauki hutu fa a office, ka raka su Amal, kaga inda zasu zauna dakuma yanayin Garin

Amal ce ta kalli Abba cikin sauri, ita tarasa meyasa Abba yakeson nesantata da daddy

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button