BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallanta takai wajan daddy ko zai fadi abinda zai karesu, Amma ga mamakin ta saitaji yace to Abba insha Allah zansa mana lokaci saimu shirya mu wuce
Abba yace to Allah yayi muku albarka
Zaku iya tafiya
Cikin sanyin jiki Amal ta tashi, suka hada ido da daddy tasakar masa harara tayi Dakinta
Shima bai lura da iyayen nasa suna falon ba yabi Bayanta, yana shiga Dakin yaganta Akan gado tana kuka
Cikin sanyin jiki yaqarasa gadon ya janyota jikinsa yafara bubbuga bayanta alamar rarrashi, qwace jikinta tayi tace Nika rabu Dani, baso kake arabamu ba? Ai shikkenan
Sake kamota yayi ya rungume ta sosai ajikinsa, baby bazata gane ba, shi kansa idan yacika magana a halin yanzu to zai iyayin kukan Shima
Cikin rawar murya yace “baby”
Kiyi hakuri, ni kaina bazan so abinda zaisa muyi Nisa da juna ba, kema kinsan Ina kaunarki fiye da komai
Amma baby maganar Abba akwai gaskya aciki, likita tace abarki ki huta zuwa wani lokaci
Baby Ina ganinki Koda yaushe akwai lokacin da bazan iya hakura ba, dole ne mu take dokar doctor, Bayan kuma hakan illa ne ga lafiyar ki data babynmu
Sanin kanmu ne kowa yadauki BURIN duniya ya dorawa wannan cikin, musanman ni danafi kowa buqatar sa
To tayaya zanso in aikata abinda zaisa narasasu? Baby idan Ina ganinki gaskya bazan iya hakura ba, bazan jure ba baby nah
Dagota yayi yakama Fuskarta ya riqe da hannayensa biyu, yace nayi miki alqawarin zan dinga zuwa Ina ganinki akoda yaushe kinji?
Daga masa Kai tayi, tana hawaye, ahankali yasa harshen sa yashare mata hawayen duka, sannan yahade bakinsu waje daya
Saida yayi kissing dinta sosai, sannan yadago da fuskar sa yace kin hakura?
Cikin sanyin jiki ta rungume shi, tana Ajiyar zuciya
(Ummy Abdul Nima comment dinki yatafi Dani kamar yanda BURINAH yatafi dake????)
Gaskya babu abinda zance da masoyan wannan novel, tsakanina daku Sai godia ????????
Godia ta mussaman ga masoyan BURINAH na Facebook, haqiqa inajin dadin yanda kuke zuba Sharhi Akan BURINAH, but Dan Allah karkuce yayi kadan Dan nasan Hali ????????????
Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
29
Haka suka zauna tana rungume ajikinsa har tsawon wani lokaci, yana ta faman bubbuga bayanta alamar lallashi, har bacci ya dauke ta
Ahankali ya kwantar da ita Akan gadon sannan yayi kissing goshinta yafita daga dakin
Direct dakinsa ya wuce Shima, yafada kan gadonsa gamida rufe idonsa
Koda wasa bai taba tunanin soyaiyar wata yarinya zata yi masa mugun kamu kamar hakaba Bayan salma
Sai gashi zai shiga wani Hali saboda rabuwarsa da baby
Ko Yaya zai iya rayuwa Bayan Bata nan?
Bayajin yanda yake tsananin kaunarta zai iya wata biyu batare daya sakata acikin qwayar idon saba
Murmushi yasaki lokacin daya tuna da darun datayi masa na dazu, Wai ya nasan arabasu
Baby kenan Uwar rigima
Dena murmushin yayi lokacin da maganar salma tafado masa arai, yatuna lokacin dasuke wasa da fillo a falon su Momy yace
“salma kibani wannan fillon “
” gwalo tayi masa tace bazan baka ba saikayi murmushi “
” inkinga murmushi na to amarya ta nake yiwa
Ashe kuwa hakanne, gashi yanzu yanayin murmushin ga baby akoda yaushe
*** *** ***
After one week
Rana Bata qarya, inji bahaushe
Suna tsaye acikin airport din gaba dayansu
Amal na Jikin momy Sai kuka take, momy tace Amal kiyi hakuri mana, ai Zaman nadan wani lokaci ne zaki dawo kinji yata?
Cikin kuka tace momy ni banasan rabuwa dake
Jikin momy yayi mutuqar sanyi, ita kanta batasan rabuwa da yarinyar, juyawa tayi ta kalli Abba
Shima cikin ransa quna yake, Dan haka cikin sauri yakawar da kansa Dan karsu gane halin dayake ciki
Yadubi daddy yace to karaam, ai babu wata matsala ko?
Cikin dauriya yace Abba babu damuwa, insha Allah idan munje zanyi kokarin samar mata da komai
Abba yace to kace baka buqatar doctors dinma
Daddy yace Abba ai can ma sunada qwararrun likitoci, jb yahadani da wani doctor zanje wajansa mu tattauna saiya bamu qwararrun likitocin mata zasu yi Mata komai
Abba yayi Ajiyar zuciya yace Toshiknn, Allah yakaiku lafiya
Shahida ta rungume Amal ajikinta, tana sake rarrashin ta, Shahid ya matso yace duk kune kuke sake shagwaba yarinyar nan fiancee
Yadubi Amal Yace qanwata, Allah yakaiku lafiya
Hararar wasa tasakar wa Shahid din, daddy yana kallansu yana murmushi
Komawa yayi wajan jama’ar da sukayi dandazo wajan rakoshi airport
Haka yayita meqa musu hannu, suna sake musabaha sannan yajuyo yakamata hannun Amal yariqe
Sukayi sallama dakowa suka yi ciki
Babu Bata lokaci aka bada umarnin shiga jirgi, Kai tsaye inda manyan mutane suke zama acikin jirgi suka nufa, kamar govnors da sarakuna
Basufi minti goma da shiga jirgin su ya Lula zuwa Malaysia
*** *** ***
Already yariga yayi musu booking din komai na inda zasu zauna zuwa wani lokaci
Dan haka Kai tsaye jirgin su na sauka direct gidan aka kaisu
Sosai gidan yayi masifar haduwa, daga wajansa ya qawatu da shuke shuke masu gwanin sha’awa
Bawani babban gida bane Amma yanda aka tsarashi ne kadai zaisa ya birgeka
Cikin falon komai milk and ash color ne hatta dining table din haka kalar su take
Cikin kitchen Din kuma komai green ne, dakuna ne guda biyu da aka qawata su da furnitures launin pink da baqi
Shine yayi Mata jagora har cikin gidan, ita Kam Sai Kalle Kalle take
Dubanta yayi yana cire babbar rigar jikinsa, ya ajiyeta Akan kujera yace kihuta baby, zanje in dawo
Kallansa tayi tace Amma my dear ni gaskya tsoro nakeji
Daddy yace babu abinda zai sameki baby, nuni yayi Mata da kofar falon yace dubafa akwai megadi, ki shiga kiga gidan idan akwai abinda bai miki ba saiki fadamin idan nadawo, dama ni na ganshi awaya tun kafin muzo
Cikin shagwaba tace to Amma karka dade
Yace angama baby nah, yasakai yafice daga falon
Tashi tayi ahankali tana kallan gidan, saida ta zagaya ko’ina, tanata murmushi ita kadai, gaskyar Abba dayace tana buqatar waje marar hayaniyar mutane, yanzu de duba yanda gidan nan yayi sosai, komai ya birgeta
Saide matsala daya zata zauna tsawon wani lokaci babu BURIN ranta atare da ita
Ajiyar zuciya tasauke, ta janyo jakar kayansu tayi cikin daki da ita
Rigar bacci ta janyo ta ajiye Akan gadon, sannan tadaukowa daddy nasa kayan baccin
Sannan ta daura towel tashiga wanka, tana futowa ta Bude jikinta da turare
Takama gashin kanta tayi kalba qwaya daya dashi, jelar gashin tasauko agadon Bayanta
Hijabi ta nema tayi sallolin da ake binta, sannan ta cire hijabin tafuto falo
Bata dade da zamaba, daddy yadawo
Akan kujera ya zube yana cewa wash baby
Cikin daria ta dube shi tace kagaji ko Yaya daddy? Sannu, tashi muje kayi wanka da sallah saika kwanta kahuta
Kallanta yayi cikin sauqin so yace ai nayi sallah awaje, naje nasiyo abinda zamu ci ne, sai kuma wajan doctor danaje Akan maganar ki, insha Allah gobe zai turo mana da doctors din dazasu dinga lura dake da babynmu
Daya zata dinga zuwa da safe har dare
Dayar kuma zatazo da daddare Sai Washe gari da safe idan yar’uwarta tazo saita tafi gida
Kallan mamaki tayi masa tace Yaya daddy saikace wata yar Sarki?
Hannunta yakama ya riqe sannan yace ai awajena kinfi Sarkin ma baby
Tace to naji, muje kayi wankan yanzu
Yace no Zona fara baki abinci tukun, idan na tabbatar babynmu ya qoshi sainaje nashirya Nima inzo kibani nawa