BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Kallansa take da tsananin mamaki, wannan wanne irin so yakewa wannan cikin?
Batace masa komai ba Takama hannun sa tana janshi, tace bazan ci komai ba, saina tabbatar kaima ka gama komai, saimuci abincin mu kwanta, Naga kagaji sosai
Binta yake da kallan luv, ashe Shima an damu dashi haka
Babu musu yatashi sukaje ciki yayi wanka, itace ta taimaka masa yashirya, sai shagwaba yake zuba mata
Falon suka dawo, suka fara cin abinci, shida kansa yadinga Bata harta qoshi
Sannan Shima yaci nasa
Dakanta ta tashi taje ta Bude fridge a kitchen, komai da komai akwai, hatta kayan fruit Ba’a bar komai ba
Ruwa da just tadauko musu tareda cup
Bayan sunsha ne,daddy yatashi da kansa yaje ya maida
Daukarta yayi cak suka koma kan doguwar kujera, tana kwance a Kirjinsa
Cikin rada yace baby kinsan me?
Kanta ta girgiza masa batare datayi maganaba
Yace lokacin da mukaje Germany natuna, kowa baya kula dan’uwansa
Sai yanzu ne Naga babban gangancin dana tafka wajan rashin kula dake
Dagowa tayi da kanta tana kallansa ta rufe masa baki da Hannunta
Cikin daria tace Dan Allah kabari
Karkasa natuno halinka nada daria tayimin yawa
Kallanta yake yana zuba mata murmushi yace menene halin nawa nada?
Kwaikwayon maganar sa tayi tace “idan kin gama zamu fita”
Sannan tasake cewa “karki batamin lokaci minti goma nabaki”
Daddy baisan lokacin da yasa daria ba
Yace kai baby banda sharri fa
Hararar wasa ta sakar masa tace bawani sharri
Haka sukai ta tuno abubuwan dasuka faru dasu abaya suna daria
Daga qarshe suka kira yan nigeria kowa da kowa suka gaisa sannan sukayi cikin daki suka kwanta
*** *** ***
Amma gaskya Shahid babu abinda zance dakai saide nace Allah ubangiji yayi muku albarka gaba dayanku
Shahid yace amin baba
Qwallah ce ta cika idon baba hamani afili yace Allah yaji qanka ibrahima, Allah yamaka rahma
Shahid yace baba kayi shiru haka mana, umma dake gefe tace a a Shahid wannan abun farin ciki ai yafi karfin ayi shiru
Wayarta ta dauka ta kira layin dasu Amal suka kirasu dashi, tana shiga wayar na hannun daddy
Shine yafara dagawa saida suka gaisa sannan yabawa Amal wayar
Suna gaisuwa umma tace Amal din baba, yayanki fa yabiya mana umara nida shi da babanku dakuma shahida, ankusa gama komai cikin wani satin zamu tafi
Cikin farin ciki Amal tace wayyo Allah umma tah
Umma Dan Allah idan kunje nide haqorin makka nakeso, da turaren wuta irin na larabawa mai qamshi, da abaya
Umma ce ta dakatar da ita tace to shashasha, kede kullum bazaki girma ba, memakon kice abaki Shahid din ki sake yimasa godia kokuma abaki babanku kiyi masa murna a a Sai kika hau lissafi
Cikin shagwaba tace Kai umma to Naga Yaya Shahid din yayanane
Umma tace keni Sai anjima
Wayar umma ta kashe tabar Amal da waya a kunne
Daddy dayakejin duk abinda suke fada, baisan lokacin da yasa daria ba yace me haqorin makkah, a a kaga hajiya Amal
Fillon dake gefenta ta dauka tafara jifansa dashi
Yana kaucewa, haka sukai tayi dashi suna zagaye cikin falon
*** *** ***
Atamfa ce ajikinta light blue Sai adon pink da baqi ajikin atamfar
Sosai dinkin ya karbi jikinta
Farar fatar ta tafuto Shar aciki
Fuskarta tasha makeup, tasaka pink din Jan baki a yan qananan lips dinta
Daurin datayi akanta ne yabawa gashin kanta damar zubowa agadon Bayanta
Yana tsaye cikin ash din suit, tana daura masa agogo qirar Gucci
Fuskarta babu alamar farin ciki
Takalmin sa ta dauko qirar Italy ta tsugunna Takama kafarsa ta Zura masa takalmin
Temako daya yayi Mata shine daga mata kafarsa
Sumar kansa ta taje masa, sai sheqi take, sannan tashiga fesa masa turare
Tana gamawa ta ajiye turaren tayi hanyar falo idanun ta nazubar da hawayen data Kasa riqewa
Cikin sauri ya fuzgota jikinsa
Babu Bata lokaci ya rungume ta tsam ajikinsa
Hawaye ne suka sakko asaman kyakkyawar fuskar sa, yayi sauri ya goge karta gani yasake kashe mata jiki
Kuka take sosai, harda sheshsheka, cikin sanyin murya yace kiyi hakuri baby
Insha Allah bazan wuce wata daya ba zanzo naganki tareda babynmu kinji?
Kuka take tasake qanqameshi, Shima kansa kuka zuci yake, Yama rasa wacce kalmar zaiyi amfani da ita wajan rarrashin ta
Kamota yayi suka futo falon, yace Dan Allah baby kiyimin alqawarin zaki kulamin da kanki da baby na, kidinga cin abinci sosai, karkibar babynmu da yunwa
Duk abinda kike buqata kifadawa doctor’s dinnan zasuyi miki, akwai me aiki dazata fara zuwa anjima
Ban yarda ki dauke ko tsinke ba
Duk abinda baiyi miki ba
Kawai kisanar Dani tawaya
Yana fadar haka wani irin kuka yazo masa kusa, wani qullulun baqin ciki ya tokare masa wuya
Cikin sauri yajuya yabar falon yana goge hawayen idonsa yafita harabar gidan yashiga Mota suka wuce airport
Kan kujera tafada tasaki wani irin kuka mai ciwo, sai yau taji ta tsani mulki a rayuwar ta
Gashi asadinsa anrabata da daddynta
Kuka take sosai, cikin sauri daya daga cikin doctor me kula da ita tafuto daga Dakin dayake kusa dana Amal ta janyo ta jikinta tana aikin rarrashin ta, cikin harshan turanci
*** **** ***
Tunda daddy yatafi tazama wata irin shiru shiru, Bata magana sosai, kullum cikin tunanin sa take, abinda yake hanata shiga damuwa daya ne yanda zai Bata tsawon lokaci yakirata awaya suyi ta waya yana sakata daria
Saikuma video call a computer daya zama qa’ida kowanne dare, harta saba kullum yakira waya saita dage rigar ta ta nuna masa cikin yagani, banda ruwan pictures datakeyi tana tura masa
Gaba daya ta kumbura, cikin jikinta daya cika wata biyar yayi wani irin girma, abin har tsoro yake Bata, saboda ba haka take ganin na sauran mata masu ciki ba
Duk ranar Allah Sai doctor ta matsa mata kafarta saboda yanda suka kumbura
Haka doctor zata Sata agaba suyi ta zagaye gidan, saita gaji ne sannan zasu dawo ciki
Batta da aiki Sai shan fruit, kullum shine take wuni tanaci, batada damuwar komai banda rashin ganin mijinta
Idan ta zauna afalo anan take wuni, saboda cikin nauyin sa yafi karfin ta, wani lokacin tayi sallah a zaune, wataran kuma idan tanajin dama dama tayi yanda tasaba
Taqara wani irin kyau jikinta yayi bulbul ta murje, Taqara zama yar hutu kamar ka latsa jikinta jini yafuto
A bangaren daddy kuwa yafita zumudin San ganinta, so yake kawai Rana daya yayi Mata zuwan bazata, ayyukan gabansa yake burin yaga yayi sosai, yanda dazaran ya ware wajan babynsa babu me nemansa
Mrs Usman ce ✍????????BURINAH ????
(A Romantic love story)
Writing by Amnah El yaqoub
Bismillahir-rahmanirraheem
Second to the last
30
Fiancee banga perfume din danake using dashi ba Ina kika sakamin shi?
Dawowa tayi kusa dashi tace wallahi yana cikin kayana fiance, qamshin nakeso, shiyasa na sakashi cikin kayana Dan su dinga yin qamshin turaren
cikin rashin damuwa yace ok bari nayi amfani da wannan
Yasa hannu yadauki wani yana fesawa
Haka ya budawa jikinsa turare kamar sabon ango
Cikin dauria ta to she hancinta, tana turashi gaba
Da mamaki ya kalleta yace lafiya?
Cikin to she hanci tace bansan wannan qamshin turaren fice daga Dakin nan
Jikinsa ne yayi sanyi yazuba mata kyawawan idonsa yana Kallanta
Cikin sauri ya matso kusa da ita yace lafiya kike kuwa?
Jin qamshin akusa da ita ne yasa cikin azama ta tureshi tayi cikin toilet da gudu tana kwara Amai
Bin jikinsa yayi da kallo yana janyo rigar jikinsa yana shaqar qamshin turaren
Yarasa me taji dahar zaisa ta yin Amai