BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Taje ta dauko mata wani, tace gashinan Kisha kadan banasan yawan shan abin zaqin nan dakike

Cikin murmushi Amal ta karba, suna zaune suna kallo aka hasko daddy a government day secondary school bununu inda yakai musu ziyara

Abba cikin farin ciki yace babana kullum ka tabashi sai yace shide bayasan wannan mulkin Amma duba kiga yanda yadage yake aiki tuquru

Cikin Jin dadi momy tace ai alhaji daddy idan yaso akwai aiki, mutane nasansa narasa meyasa bayasan mulkin

Abba yace shirme ne kawai irin nasa

Amal najinsu tana murmushi, Wayarta ta dauka ta turawa daddy text tana me qara qarfafa masa gwiwa Akan mulkinsa, yakuma gaida yaran da yakai musu ziyara

Adede lokacin daya daga cikin security ya miqo masa wayar sa
Amma Bai amsa ba

Cikin ranta tace tofa Lalle sarakan aiki

Suna nan zaune inda su Momy suka ci gaba da kallan labarai suna tattaunawa
Amal ta tashi ahankali tashige daki danta kwanta tahuta

Tun jiya take danjin Bayanta na ciwo kadan kadan, ga wani irin ruwa datake zubarwa Shima kadan, Amma dayake ciwon Dan kadan ne saitayi shiru Dan karta daga musu hankali, tasan dole da sunji tana Dan rashin lafiya zasu tashi hankalin su, shiyasa ta danne tayi hakuri

Tana kwanciya bacci ya dauke ta

 ***      ***      ***

After one hour
Acan falo kuwa su Abba suna kallo shida momy daddy yayi sallama yashigo duk Agajiye yana zuwa yafada cikin kujera tareda dora kansa Akan kafadar momy

Abba yace ikon Allah yau kuma antuno baya kenan
Momy ce ta shafa kansa tace daddyn momy ai dama haka yake

Yace momy nagaji wallahi, tace ai yanzun nan muka gama ganin ziyarar dakakai makaranta, Allah yatemaka yabada sa’ah

Amin momy
Ahankali yatashi yayi hanyar Dakin Amal iyayen suka bishi da kallo

Yana shiga Dakin yaganta aqasan tayils tana murqususu

Cikin sauri ya qarasa wajanta yadauke ta cak, yana Kiran Amal! Amal!!
Duk ya gigice, yasan cewa yanzu Kam haihuwar ce ta tashi, innalillahi yanzu Badan yashigo dakinba Yaya zatayi

Su Momy suna falo a zaune suka ganshi yafuto da ita, ai gaba dayansu sukayi kanta

Momy tana ganinta tace wannan haihuwar ce tazo
Muje, muje asbiti da sauri

Abba ne yayi azamar Kiran doctor, dayake acikin gidan asbitin yake nan da nan doctors suka qaraso da gado, aka dorata akai, suka turata zuwa cikin Dakin labour

Daddy yakama babbar rigar sa yacire, bemasan waya meqawa ba, shide yasan yabawa mutumin dayake gefensa

Ana shiga Dakin da ita suka rufo kofar Dakin

Daddy Sai zagaye yake awajan, momy ce me kwantar masa da hankali itada Abba

Shiru shiru tun suna qirga awa daya, har saida suka je kusan awa uku Amal shiru babu labari

Doctor ce tafuto, suna ganin futowarta sukayi caaaaa akanta da tambaya, tace alhaji kuyi hakuri har yanzu de tana naquda, dasaura haihuwar, Amma idan taqara wasu awoyin zamu shiga da ita operation room
Tun kafin yagama Jin karshe zance yasaka kansa cikin Dakin
Tana kwance tana kuka, gashin kanta duk yabaje Akan fillon datake Kai, duk gumi yajiqa mata jiki

Hannunta yakama yace baby, sannu baby

Cikin kuka tace Yaya daddy kayafemin mutuwa zanyi

Ai tana ambatar mutuwa daddy yafara hawaye, ba komai ne yasashi kuka ba Sai kasancewar ta Awannan halin dakuma salma daya tuno, itamafa acikin wannan halin tarasu

Kamar tababbe yace a a! A a! Dena wannan maganar Dan Allah, baby bazaki mutu ba, insha Allah lafiya zaki haihu

Cikin kuka tasake damqe hannun sa tace Yaya daddy mutuwa zanyi kayafemin duk abinda nayima

Gaba daya Tasa jikinsa yayi mugun sanyi

Yariqe ta Yana hawaye, Idanunsa jajir, doctors din dake kanta suka zuba musu ido suna kallan me girma govnor da kansa, yana kuka tuquru kamar bashi ba

Abba ne yashigo Dakin da ruwan rubutu acikin yar qaramar jarka yabata daqyar ta’iya Sha tana daga kwance

Cikin ikon Allah ba’afi minti talatin ba naquda Ganga Ganga ta tashi
Abba ne ya janye daddy suka fice, suna fita kuwa momy tana cewa alhaji Yaya Jikin nata?
Yace a a alhmdh saide fatan Allah yaraba lafiya

Cikin Dakin kuwa doctors suna qara temaka mata wajan cewa kiyi hakuri ranki yadade
Wasu na danna mata cikinta, wasu Kuma suna fadin yi nishi, yi nishi

Tana qwaqwqwaran nishi kuwa Sai kuka sukaji, doctor din datake Gabanta ce tatemaka mata wajan janyo kan babyn

Ana ciroshi yacika Dakin da kuka
Doctor din cikin murna tace congratulation ranki yadade kinsa mu baby boy

Amal Kam batasan inda kanta yakeba ma, domin kuwa still wani ciwon takeji

Acan waje kuwa sunajin kukan jariri daddy ya tsugunna yayi wa Allah godia ta hanyar sujjada

Momy tace alhamdullah
Tasauka

Amal kuwa wani irin ciwo tasake ji yataso mata, batasan lokacin data kaiwa doctors din dake kanta wani irin riqo ba, ta rintse idonta, tana hawaye Sai ga kan wani Yaron yafuto
Nanma aka ciroshi

Aka hadashi da dayan aka gyara su, ita kuwa Uwar baccin wahala ne yadauke ta

Kayan sanyi farare qal aka dauko aka sakasu aciki Sai kuka suke

Cikin baccin ta tasaki wata irin qara tana salati

Doctor ce ta matso cikin sauri tana dubata ta kalli sauran doctors din tace akwai Yaron acikinta

Gaba dayansu suka cika da mamaki, aiki be qare musu ba kenan

Amal kuka da ihu tanata salati su kuma suna aikin rarrashi, saida sukadau kusan minti talatin Ana Abu daya sannan ta haifi danta namiji Shima

Gaba dayansu yaran kamarsu daya babu banbanci lafiyaiyu dasu

Dakin haihuwa yacika da kukan yara

Dayan Yaron aka shirya Shima irin sauran yan’uwansa, likitoci sukayi musu alamar yanda za’a Gane nafarko da masu binsa

Yara bul dasu masha Allah Sai motsi suke suna kuka, idonsu Kar Akan wutar lantarki

Wahalallan bacci ne yasake dauke Amal Bayan angyara mata jikinta

Doctors har rige rigen daukar yaran suke, sunga abin mamakin daba’a cika samun suba aqasar hausa triple kuma duk maza

Babu wadda Bata dauki pictures dinsuba awayarta, za’a nunawa jama’ah wannan abin mamaki

Su daddy suna waje Sai gani sukai doctor’s sun futo da yara

Fuskarsu dauke da murmushi suka meqa masa

Mamaki ne yakashe su gaba dayansu su ukun

Daddy yayi saurin karbar su yana kallan Abba da hawayen farin ciki yace Abba triple

Abba cikin tsananin daria yace ka godewa Allah babana

Juyawa yayi wajan momy itama da tsananin murna yahanata magana takarbe daya ta riqe, Abba ma ya karbi daya, Gaba dayansu yaran basu bar komai na ubansu ba, gashi ne kawai sukayi na Amal
Amma hatta yatsun kafarsu irin na daddy ne

Daddy yace likita zanyi muku kyauta ta mussaman Bayan nadawo nutsuwa ta

Zan iya ganin maman su? Cikin daria suka bashi damar ganin ta, aikuwa cikin sauri yashiga Dakin

Yana shiga Dakin ya zauna agefen gadon datake kwance
Yakama Hannunta yariqe yana zubawa ubangiji godia daya mallaka masa Amal
Be dade da zama ba tafarka, sake matsawa kusa ita yayi, yace sannu baby, Allah yayi miki albarka

Cikin murmushi tace Yaya daddy Mena Haifa?
Kafin yabata amsa su Abba suka shigo da kin da sauran yaran ahannunsu

Suka jere mata su a Gabanta, Abba yace ga yaranki nan yata
Cikin kunya ta rufe idonta da tafi Hannunta

Daddy yace keda kika tambaya, to ga Sunan Allah yabamu yan’uku baby duk maza

Momy tace ai babu abin godia Kam Sai Allah, haqiqa Amal kinyi kokari Allah yayi muku albarka kuda yaranku duka
Ta dubi Abba tace alhaji kagafa ikon Allah, shekara da shekaru muna fatan samun qarin zuri’ah acikin mu, Allah Bai bamu ba, Amma gashi lokaci daya yabamu yara har uku

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button