BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Abba yace hakane Kam hajiya, haqiqa Allah yanuna ikon sa anan
Amal de tayi shiru tana kallan yaran gaba dayansu kama suke da daddy, wata irin qaunar yaran tana ratsa jikinta
Jama’ah suka gani suna shigowa cikin Dakin,suna taya daddy murna, cikinsu harda Yan jarida inda suka fara haska wa yara pictures Suda maman su da babansu
Abba yace ya akai kuka sani ne,,? Wasu daga cikin security sukace ai doctor’s ne suka fita waje suka sanar dasu
Kafin kace me daki yacika danqam da jama’ar alamina, wasu sunzo kallan yan uku wasu Kuma suna taya me girma gwamna murna, ganin irin tsawon shekarun daya debe Allah Bai bashi haihuwa ba
Sai dare aka sallamesu daga asbitin suka koma gida
Inda nanma de basu rabu da wata jama’ar ba, shahida da Shahid sunfi kowa zaqewa Akan yaran, anty mufy kuma Sai gobe zata qaraso
Daga ita har yaran Dakin momy suka koma, mutane kuwa da wannan yafita wasu zasu shigo
Daddy babu kunya yacewa momy Ana jagwalgwala su, adena bari Ana daukar su
Momy tace to sannu me yara
*** *** ***
After 6 day’s
Dakin momy yashigo Allah yasoshi Bata Dakin, daga Amal Sai yara
Kallanta yayi cike da sha’awa yace baby wallahi nayi missing dinki, jama’ah basa bari ma ingana nida yarana
Hannu yasa yadauki daya yace dafatan sunayen dana fada miki sunyi ko? Tace Yaya daddy sunyi Allah yarayasu
Yace amin baby, kuka daya daga cikin yaran yafara yace baby kibashi nono yasha may be yanajin yunwa ne
Cikin shagwaba tace Allah yaya daddy Nagaji, yanzu fa nabasu madara, kuma ni idan sunasha zafi nakeji, da karfi suke Sha
Daria ce takamashi yace basa yi ahankali kamar niko?
Fillo ta dauka ta jefa masa yace to naji sorry
Yanzu de Dan daure kibashi ko Dan kadan ne kinji Badan halin muba
Daukar Yaron tayi tafara bashi, yanasha tana rintsa ido
Tana kwantar dashi yayi bacci kamar sauran
Daddy ya janyo ta jikinsa, yana shaqar qamshin dake tashi ajikinta, yace baby nayi missing dinki dayawa
Bata gujeshiba tace Nima haka Yaya daddy
Bakinsu yahade waje daya, yakai hannunsa gadon bayanta yazuge zip din rigar ta, yana kissing dinta yana shafa jikinta
Ahankali momy ta turo kofar Dakin tashigo, Kai wannan yaro da jaraba yake, abinda ta guda kenan fa tadauke Amal din tadawo da ita Dakinta, ashe nan dinma ba’a tsira ba
Batare da tace masa koma ba ta nuna masa hanyar waje, Shima babu musu yafice kansa aqasa
Ferfesun Hannunta ta ajiyewa Amal tace gashinan dauki ki cinye tas, kuma kici gaba da biye masa kinji, basai nafada ba aikinji wahalar dakika dandana awajan haihuwa
Amal kanta aqasa cikin ranta tace Kuma fa hakane wallahi, tsaf zata Iya samun wani cikin, dole ne tayi taka tsan tsan
*** *** ***
Washe gari aka radawa yara suna, nafarko yaci sunan mahaifin Shahid Ibrahima Ana kiransa da suhail, Nabiyu yaci sunan Abba, Abdallah anan kiransa da salim saina qarshe yaci sunan Muhammad hamani Ana kiransa da sadat
Salim, sadat, suhail
Mutane da dama sun halarci taron sunan, inda me jego take shiga tana fita cikin kaya iri iri, da temakon anty mufy
Inda me girma gwamna yayi sanarwa yana gayyatar jama’ar bauchi dama kewaye kowa yazo ayi taron suna dashi yaci yasha
Aikuwa jama’ah ba’a nemesu Bama Yaya aka qare bare kuma an nema
Mutane sosai suka zo, ciki harda wasu daga cikin gwamnonin wasu jihohin
Dole Sai Wikki hotel ake Kai mutane, wasu Kuma aka kaisu Zaranda hotel
*** *** ***
After 3 years
Ummi kinga suhail yafasa min bakina
Remote din Hannunta ta ajiye tace mugani, bakin yabude mata tagani, Babu wani alamun fashewa tace yi hakuri, zan kamashi na zaneshi kaji salim
Tana cigaba da kallan widad ta taho tace ummi boyeni sadat zai dakeni
Amal batasan lokacin data dafe kantaba, yaran nan zasu haukatata
Adede lokacin daddy yashigo, yaran suka tafi da gudu sunayi masa oyoyo
Amal tace gara da kazo danna gaji da Raba fada
Daddy yace ku taho nan abokai na
Zama sukai Akan kujera dukansu daddy yafara Jin Qarar kowa sannan yabasu hakuri
Yadubi Amal datake da Dan qaramin ciki yace shikkenan naraba fadan tace eh, Dan Allah idan zaka fita kakaisu wajan momy wallahi nagaji
Sadat yace eh akaimu, Amma banda widad
Salim yace ummi ba zamuje da sadat ba nida widad da salim zamu
Widad tace eh ummi
Suhail ne ya harareta, daddy da Amal suka kallesu sukasa daria
Itade widad duk lokacin da tazo gidan suhail ne abokin fadanta
Daddy ne ya Hadasu ya rungume su gaba daya, yace to naji, dukanmu zamuje gidan momy, Daganan muje musha ice cream
Gaba dayansu sukace yeeeee
Haka rayuwar gidansu take gudana cikin farin ciki da annushuwa, Amal tana daukeda wani cikin, yayinda Shahida Takeda yarta daya maisunan momy suna kiranta da widad
Maisah ma tana can a jigawa da danta namiji daya maisunan baban sham
Tunda tenure su daddy taqare yace bazai sake neman takaraba, dama wannan ma bashi akayi, Dan haka yahada da gidansu nafarko yahada da wani filin yayi musu tanfatsetsen gida nagani nafada, inda suke gudanar da rayuwar su cikin Jin dadi
TAMMAT BI HAMDULLAH
Anan nakawo qarshan wannan novel na BURINAH Ina roqon Allah yabamu ikon yin amfani da abinda muka tsinta aciki me amfani, ya Allah kayafemin abubuwan dana fada aciki wanda yasabawa shari’ar musulunci
ATAKAICE
Littafin BURINAH yana nuni ne Akan Abu biyu, nafarko yiwa iyaye biyaiya, daddy da Amal burinsu suga sunyiwa iyayensu biyaiya, inda sukaga hakan yahaifar musu da farin ciki me dorewa
Na biyu hakuri da kuma daukan qaddara, Shahid yayi hakuri yadauki qaddara harta kaishi ga auren Shahida, inda daddy yayi hakuri yadau qaddarar rashin matar sa kuma yaga ribar hakan
ABUBUWAN BIRGEWA
gaskya nide abinda yafaru birgeni shine miskilancin daddy, yana so yana kaiwa kasuwa, dakuma yanda shahida take Mutuwar San Shahid
MUTUMIN DAYAFI KOWA BIRGENI
shine baba hamani danda
KARBUWA
novel din BURINAH haqiqa yasamu karbuwa ta yanda banyi zato ba, nagane hananne ta hanyar kirana da wasu sukeyi ta waya wasu Kuma suna turomin saqo ta privet, haqiqa naji dadi hakan
JINJINA GA :
A and F HAUSA NOVEL
UMMY UMMEE NOVEL
MAMAN ABBA NOVEL
AYSHA UMAR NOVEL
AMNAH EL NOVELLA
JINJINA TA MUSSAMAN GA JAMA’AR FACEBOOK GABA DAYANTA
MORE ESPECIALY HAFSAT HAUSA NOVELS (H2)
DAGA QARSHE
DUK ME BUQATAR YAGA PICTURES DIN TRIPLE YAYIMIN MAGANA TA PRIVET
saimun hadu asabon novel dina wanda zaizo muku a kowanne lokaci Bayan Ramadan insha Allah mai suna
WAZAN ZABA?
Ina fatan zakuji dadinsa fiye da BURINAH
Karku manta da Sunan
WAZAN ZABA?
Mrs Usman ce ✍????