BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaye duba can
Okasha yakai kallansa inda nazy yake nuna masa
Yace to Anya lafiya kuwa irin wannan kallo datake masa?
Daria nazy yasa yace kuma da alama mutumin baima saniba
Okasha yace inaga ta harbu fa, taga Dan buzaye ta rikice
Rufe littafin nasa yayi yatashi yabar wajan ko kallan ta baiyi ba
Yana tashi Wayarta tadau qara
Tana dagawa tace hello momy nah
Kafin ta amsa taci gaba da cewa momy wallahi Naga wani baki ganshi ba mai kyau inasan sa sosai momy
Maganar da momy tafada mata ne yasa ta sakin wayar hannun ta qasa nan take ta watse
*** *** ***
Ahankali yabude Zara zaran gashin idonsa, kallansa yakai ga Dakin dayake kwance, kansa ne yayi muguwar sarawa, momy dake gefensa cikin dashashiyar murya saboda tsabar kuka tace sannu daddy
Salma!
Salma!!
Why salma? Meyasa zaki tafi ki barni salma
Hawaye ne yake zarya a idonsa, abinda iyayensa basu taba gani yayi ba da girmansa de, kayi hakuri katashi muje kayi mata addu’ah za’a kaita makwancin ta
Tsam yatashi baice musu komai ba kawai tafiya yake idanunsa sun kada sunyi jajir
Direct gidansa suka wuce, yan ‘uwan ta sun zo ancika gidan danqam, kowa Sai koke koke yake, har Dakin da gawar take Abba yakaishi
Tsugunna wa yayi daidai kanta, ahankali ya yaye Fuskarta, tamkar zai kirata ta amsa, Babu alamar bacin rai afuskar, asalima tamkar murmushi take, hawaye ne suka tsiyayo daga idanunsa
“karaam kayimin alqawarin zakaci gaba da sona har abada, idan namutu zaka riqe mana babynmu dakyau “
Maganganun ta ne suka Fado masa arai, ashe tafiya zakiyi kibarni salma
Yafadi haka abaiyane, salma, meyasa salma, meyasa baki zaunaba ni natafi, salma kece mai sona mai kaunata, kece kadai zaki iya zama Dani da halaiyata
Salma yau gashi babu ke babu babynmu
Gashin kansa ya hargitsa
Idanunsa jajir, Abba dayake tsaye shi kansa hawaye yake sharewa
Mahaifinta ne yayi karfin halin matsowa yaja hannun Abba, wasu daga cikin danginta suka matso zasu dauki makarar, Abba ne yasunkuya yadafa kafadar daddy
Alamar rarrashi, domin kuwa babu bakin magana
Suka dauki makarar domin amsa Kiran mahalicci
Riqe makarar yayi, yana kuka haiqam tamkar ba gwarzon namiji jarumi karaam ba
Ganin baya hayyacinsa ne yasa Abba yahadashi da maqocinsa, kamashi yayi, suka tafi, Amma daddy banda kuka yana Kiran salma babu abinda yake yi
Direct asbiti aka mayar dashi, doctor bai Bata lokaci ba wajan yimasa allurar bacci
*** *** ***
Suna zaune adakin da aka kwantar dashi, momy da Abba da anty mufy, da junior, sai shahida data biyo jirgi tadawo gida tun washe Garin rasuwar
Tunda yafarka yayi shiru, baya um bare um um, baisan awanni nawa yadaukaba a kwance, idanunsa sun kumbura
Ashe salma tafiya zatayi ta barshi, shiyasa take masa maganar mutuwa, rayuwa kenan
Idanunsa ya maida ya lumshe, Abba ne yayi karfin halin cewa yakamata katashi kayi sallah, Kasa wani Abu acikin ka, Kai musulmi ne, dole ka yarda da qaddara mai kyau ko marar kyau, junior ne ya matsa kusa dashi, yace uncle yanzu kuma yaushe anty salma zata dawo ta haifamin qanina
Anty mufy batasan lokaci data dokeshi ba
Yaron yacika surutu dayawa, karaam ne yajanyoshi, yace yi shiru, zata dawo ka ka kajiii….. Yaqarasa maganar yana hawaye
Momy ta goge qwallar idonta tace tashi kayi sallah daddy, shahida hada masa tea
Ahankali yatashi yashiga toilet
Saida suka zo tafiya gida ne yaji Abba yana magana da likitan Akan cewa yau akayi mata sadakar uku data bakwai gaba daya
Hakuri yaqara basu, sannan sukai sallama dashi sukayi gida
Gidansa suka fara shiga zai debo kayansa, fir yaqi shiga, da Abba ya matsa ma kawai saiya sa kuka
Shi wallahi bazai shiga ba
Dole Sai anty mufy ce ta Dabo masa kayan
Suka juya gida
Tunda suka koma gida, yadena magana dakowa, Koda yaushe yana cikin dakinsa yana aikin tunani
Bashida aiki Sai kallan pictures dinsa dana salma acikin wayarsa
Koda yaushe cikin tunani yake, har hakan yafara damun iyayensa, suna ganima kamar ba’a hayyacinsa yakeba, idan cin abinci akazo saide yayi shiru ya zubawa abinci ido, sai iyayen sunyi masa magana sannan zaisha Dan shayi, yarame gaba daya ya lalace, Koda yaushe cikin rashin lafiya yake, kullum suna zarya a asbiti Amma Babu wani cigaba
*** *** ***
One month later
Office din dasuke meeting din aqawace yake da kujeru na alfarma, duk wanda kagani awajan babban Dan siyasa ne, wakilin jam’iyar aka bawa dama yabude taro da addu’ah, Bayan komai yalafa, yan majalissun dasauran jiga jigan jam’iyar suka fara bayani Akan abinda yakamata ace sunyi
Daya daga ciki ne yafara fadin, ni aaganina Yaron zai iya, sannan mahaifinsa qwararran Dan siyasa ne, dole zai samu gogewa ta wajan sa, Awannan zamanin fa wannan jihar tana buqatar matasa su shigo ciki suma ayi dasu, Dan haka ni de nagoya Bayan hakan Dari bisa Dari, daya Bayan daya jama’ar wajan kowa yayi mubaya’ah, Abdallah karaam ne yatashi yayi godia Sannan yaqara dacewa insha Allah Awannan jam’iyar tasu yanda suka yanke wannan hukunci, zai tsaya da kafafunsa wajan ganin anyi komai cikin kwanciyar hankali
Sannan Kuma cikin nasara, dahaka taron yatashi
*** *** ***
Murmushi ne kwance asaman Fuskarta tace gaskya alhaji hakan yayi, naji dadi sosai, kuma wannan yana nuna sunyima Kara ne shiyasa suke so wani naka yashigo cikin harkar Shima ayi dashi
Hakane, ai hajiya yau ansha fafatawa awajan meeting dinnan to daga baya de kowa yabada goyon baya
Tace hakane Allah yayi jagora yasa adace
Amin hajiya, ina wannan yarinyar ne? Tana ciki tana shirya wa alhaji, kasan gobe takesan komawa school, yace kirata kice taje takiramin daddy
Kira ta qwalawa shahida tana futo tace jeki kira yayanki
Bayan tatafi ne, yace hajiya inaga gobe zamuyi tafiyar nan nida daddy tace to alhaji Allah yakaiku lafiya
Zaune yake Akan danqareren gadon dakinsa, computer ce agabansa qirar Apple me Launin fari
Wando ne ajikinsa three quarter milk color, sai Riga marar hannu, ga green tea nan agabansa yana shan ahankali, fuskar nan atamke, Babu alamar rahma
Ahankali tatura kofar Dakin tashiga tare da sallama, har qasa ta tsugunna tace Yaya daddy Abba yana kiranka
Alama yayi Mata da kansa, bai qara kallanta ba, ta tashi ta futo tare da rufe masa kofar
Futowa yayi yaje falon har gaban iyayansa ya zauna aqasa yace Abba gani
Daddy dama magana nakeso muyi dakai, zuwa wannan lokacin yakamata ace kayi hakuri kamanta da komai kadawo kamar da, daddy BURINAH a rayuwa bai wuce ace naganka kadawo da walwalarka ba, kayi hakuri salma tariga da tatafi, addu’armu take buqata ayanxu
Kaikuma saide ka rungumi sabuwar qaddarar datake shirin shigo Maka ayanxu, Dasauri yadago da kansa ya kalli mahaifinsa
Abba yace qwarai kuwa domin kuwa munyi meeting dazu Kuma wannan meeting din anyi shine saboda Kai, mun tashi Akan zaka futo takarar gwamnan wannan jihar insha Allah
Amma Abba salma…. Dakata karaam, Dan Allah banasan Jin komai daga gareka
Sannan magana ta biyu ka shirya gobe da wuri tafiya ta kamamu zuwa jihar jigawa
Tashi kabani waje
Idanunsa jajir yatashi yayi dakinsa, yana zuwa yafara wulli da fulullukan Dakin tamkar sune suke da laifi
*** *** ***
Karfe goma na safe a jihar jigawa tayi musu, ko government house basujeba, kawai waya mahaifinsa yayi aka turo musu da Mota guda biyu suka dau hanyar qauyan maigatari
Tunda suka dau hanya babu abinda yake cewa, saide idan yagaji da kallan hanyar ne zai dau wayarsa yayi karatun alqur’ani, daga karshe ma ajiye wayar yayi ya zubawa sarautar Allah ido