BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BURINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai Bayan sun tafi ne, yadauki goro da komai aka rarrabawa maqota da abokan zama lafiya, suna zaune da kudin ahannunsa yana yiwa umma maganar abinda yakamata aqara siyowa kafin lokacin
Bayan yagama komai ne yabawa umma umarnin takira masa Amal

Tana zuwa baba hamani yace Amal
Na’am baba
Amal
Na’am baba

Sau nawa nakiraki? Sau biyu baba
To magana zamuyi dake ta fahimta
Akwai baki da sukazo wajena kwanaki, har kika kawo musu ruwa, kin tuna?
Eh baba
To wannan Yaron da sukazo dashi an nema masa auren ki, kuma nabasu, kinga wannan kudin?

Gabanta ne yake muguwar faduwa tadago ta kalli kudin yace to kudin sa ranar auren ki ne nanda sati biyu

Gabanta ya bada Damm!

Dasauri tace Amma baba ni wallahi Bana sansa

Ni Yaya sham nakeso

Kuma baba ni ko ba hakaba Yaya Shahid yahanani kula kowa yace saiya dawo

Waye sham?

Tambayar da baba hamani yayi Mata kenan, Dan shide a iya saninsa Bata kula kowa, tunda baiyi Mata wannan tarbiya ba

Tun farkoma da yasan akwai Yaron dayake hurewa yarsa kunne daga gefe, toda haduwarsu bazatai kyau ba

Zuba mata ido yayi, yace nace miki wayene sham??

Please kuyi hakuri da wannan

Mrs Usman ce????BURINAH ????

(A Romantic love story)

Writing by Amnah El yaqoub

Bismillahir-rahmanirraheem

9

Ba tambayrki akeba? Inji umma da mamaki yakashe ta a zaune

Cikin in Ina tace baba shi.. Shin.. Shine Wanda nakeso ni

Cikin tsawa wadda ita kanta Samia saida tayi mamaki saboda tasan yanda yakeson Amal
Yace karna sake Jin wannan maganar daga bakinki, nide nasan ban baki damar kula kowa ba, kuma ko waye wannan Yaron ki fada masa zanzo in sameshi
Tunda shine yake hure miki kunne
Nariga nagama magana, yaro de nabashi, Rana kuma ansa, kiyi abinda zaki iya, tashi kibani waje marar kunya kawai

Da gudu tayi daki tana kuka, nashiga uku na
Ni wallahi banasan kowa, arasa wanne irin aure za’a min saina dole, ni wallahi banasan sa, yawani zo yaqame awaje daya saikace gunki
Wallahi Bana sansa, hijabin ta take nema zata tafi gidansu maisah

Acan wajan su umma kuwa, Malam ne ya kalli umma yace Samia kinji wata sabuwa kuma ko?
Samia da Allah zai hadani da wannan Yaron datake magana akansa toda haduwarmu bazatai kyau ba Samia

Toni Wai yaushe ma Amal din har tasan kanta dazata fara kula wani bamu saniba
Amma may be yayanta ai shi yasani, tunda tare suke abinsu
Wayarsa yadauko daga aljihun sa, Babu Bata lokaci yadannawa Shahid kira
Bayan sun gaisa baba hamani yace dama inaso zan tambayeki ne, Shahid yace to baba inaji, Wai kasan yarinyar nan tana sauraran wani sham?
Shahid yace wacce yarinya? Domin kuwa shide yasan cewa Amal bai Santa da kowa ba
Baba yace wakuwa nake nufi banda Amal
Yace gaskya baba bansanshiba, itace tafadama hakan da Bakinta?
Yace qwarai kuwa yanzu nan muka zaunar da ita nace ga yaro nan nayi Mata miji harma mun tsaida ranar auren nanda sati biyu shine takemin wani zancen banza

Gabansa ne yafadi Wai wacce Amal din? Me baba yake nufi?
Shahid yace baba Wai Amal Amal de?
Baba yace ita mana to menene?

Kansa yadafe da hannun sa daya dayake barazanar rabewa gida biyu, idanunsa suka kada sukai jajir
Yace Amma baba Ina Santa
Wallahi Ina kaunar Amal baba

Kai Shahid me kake fada haka? Wacce irin magana ce wannan?
Baba wallahi nabari ne in dawo in sanar daku komai Amma baba Ina kaunar Amal tun batada wayo baba

Baba Dan Allah Kar ayi auren nan

Baba hamani kashe waya yayi batare dayace komai ba, ya rafka uban tagumi

Umma tace meyafaru Malam

Baba yace Samia mun shiga uku

Karaf akunnan Amal datake kuka zata tafi gidansu rumaisa, innalillahi meyafaru baba yake maganar shiga uku?

Kasa kunne tayi domin tajiyo karshan maganar

Baba yaci gaba da cewa ashe Yaron nan yadade yana San yarinyar nan Amma yaqi fada mana, Wai jira yake saiya dawo daga makaranta yasanar damu
Umma tace Wai Shahid?
Aini Malam nadade da gane take taken sa, kawai de shiru nayi Inga ko shaquwarsu Tasa hakan

Nashiga uku Samia, idan nahana Shahid auren Amal banyiwa IBRAHIMA adalci ba
Ibrahima ahannu na yadanqamin amanar Shahid Samia

Wannan wacce irin masifa ce ne?

Jiri ne yadebi Amal, batasan ya akai ba Sai ganinta tayi aqasa jagwab ta zauna

Yaya Shahid
Tayaya?
Tayaya za’ai ace akwai aure atsakanin su

Yaya Shahid fa

Inaaaa bazai iyuba, Dasauri ta tashi tun kafin iyayen su ganta tayi waje, Bata zarce ko Inaba Sai gidansu maisah

 ***      ***      ***

Da hannu biyu yadafe kansa dayake masa mugun ciwo, innalillahi wa inna ilaihir raju’un

Why Amal?

taku yaji akansa, yana dago Kai yayi tozali da ita, dama ita yake jira, saboda sunyi waya tace tanaso su hadu dashi awajan domin yaganta
Kamar kullum de Riga da wando ne ajikinta
Tayi bala’in kyau
Ido ta zuba masa takasa janye idanunta akansa, meyasa me shi idonshi yayi jajir haka?
Zama tayi akusa dashi
Shide yakafeta da ido, yana kallan ta, ransa amutuqar bace, da bayanin da baba hamani yayi masa
Zama tayi dab dashi
Tace barka da hutawa
Ataqaice yace yawwa barka

Dafatan ka ganeni nice mukai waya jiya
Dan Allah inaso kafadamin sunan ka

Still agajarce yace Mata “shahid”

Fara’ah ce ta wanzu afuskar ta, ashe ma sunansu daya
Cikin murmushi tace ashe ma sunanmu daya
Ni sunana shahida
Dafatan ka amince da soyaiya ta
Wallahi tun ranar farko dana fara ganinka naji ka kwanta min

Wallahi Shahid idan bansameka ba ko zan iya….

Dakata Dan Allah baiwar Allah
Kawai shikkenan daga ganina kin zauna Sai zubamin surutu kike

Dan Allah ki kalleki

Da ido tabi jikinta da kallo tanaso tagano aibun daya gani agareta

Kinga ni banda ra’ayin aure mace haka, ban tsane Kiba, kawai Bana ra’ayin ki ne, bakiminba
Hannayensa yahada waje biyu
Yace Dan Allah naroqeki kifita daga rayuwa ta

Yana gama fadar haka, yajuya yabarta awajan, me shahida zatai banda kuka

Wallahi idan Bata sameshi ba mutuwa zatai

 ***     ***     ***

Maisah nashiga uku na, auren dole baba zaimin
Bangane ba, mekike nufi ne Amal?
Cikin kuka tace wallahi da gaske nake maisah, nanda sati biyu za’a daura min aure

To dawa?
Waida wani, nifa sau daya nataba ganinsa, kawai shine baba ya karbi kayan saka ranar su
Ashe Yaya Shahid sona yake maisah

Ashe ba cikinmu daya ba
Ta qarasa maganar cikin kuka
Yaya Shahid de Amal, Yaya akai kika sani?
Wallahi da kunne na naji su baba suna maganar

Kuma ni wallahi babu Wanda nakeso inba Yaya sham ba

Amma Kuma Da’a auramin wannan mutumin gara sau dubu in auri Yaya Shahid dina

Ajiyar zuciya maisah tasaki, tace Amal, shiyasafa kwanaki nake tambayrki cewa Anya kuwa Yaya Shahid iyayen ku daya?
Kikacemin eh

Amal abinda zan fada Miki shine kiyiwa iyayenki biyaiya, bakida kamarsu aduniyar nan

Amal baba yayi miki komai, ke kanki kinsan cewa yana sanki, bayasan bacin ranki, meyasa ba zakiyi masa biyaiya ba?

Amal baba bazai ba dake inda za’a cutar dakeba, kiyi hakuri

Rungume rumaisa tayi tana ci gaba da kuka, maisah tana bubbuga bayanta alamar rarrashi

 ***     ***     ***

Da daddare tasha maganin ciwon Kai, ta kwanta, idonta biyu, tayi shiru tana tunanin rayuwar ta yanda take neman juyewa
Umma ce tashigo ta miqo mata waya, tace gashi zakiyi magana da yayanki

Tana Bata wayar tajuya ta fita

Da sallama ta daga wayar, Yayanah
Kawai saita da kuka, Shahid da zuciyarsa ta kusa karyewa yace menene kuma abin kuka?
Ko Dan baki samu sham dinki ba?

Nifa Yaya bahak…..
A a Amal, bakiji magana ta ba, inda kinji bazakimin hakaba, cikin kuka tace Dan Allah yayanah kayafemin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47Next page

Leave a Reply

Back to top button