DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Toh gurin yayi amman itakam tsoron mutane take sosai dan haka yasa tace suje dayan wanda bashi da phalo suzauna kawai tunda shi kofar shiga part dinkama daban take data daya 6angaren kuma akwai katanga data shiga tsakaninsu kowa kofarsa daban

Nan taza6a tace masa nan yayi Baba bari muzauna anan kawai
Toh shikenan amman kinsanfa nan dubu #20 ne koh duk shekara
Ey baba zan biya yanxu bari in baka rabi zuwa nan da sati biyu zan cika maka to shikenan

Shiga sukayi da kayansu taduba tadauko masa dubu goma acikin kudin ta sanann tafuto tace gashi Baba 

Yace A’a Yar nan bari in kira dayan abokina sai mu amsa kinga saboda yanayi na rayuwa yau kaine gobe ba kai bane ko yakikace
Hakane kam
Wayarsa yadauko yacdanna kira wata number aka dauka nan yayi masa jawabi sosai yadda zai gane sannan yace gashinan zuwa
Bai dadeba yakaraso nan akayi komai akan idonsa
Nan sukace taciko dubu biyar kawai tarinka biyan dubu shabiyar 15 duk shekara taji dadi sosai kuwa
Baba sa’idune yakalleta yace yata kije asibiti aduba miki kafar nan taki dukta kumbura gashi taja ruwa ko kuma kiduba kiga ko sartse kikayi
Toh baba IN SHA ALLAH zanduba in gani kafun inje koda chemins ne
yace mata yanxu kingani kowa yanada nasa shaidun koh ke da danki daya da Malam baba
Nima nida danki daya koba hakaba
Kinga hakan yafi kai waye
Ey Babah ngd sosai
A’a karki damu ai duk wanda yataimaki wani shima Allah zai tai makesa
Hakane kam ngd
Sosai Allah yasaka da alkhairi
Ameen tafiya sukayi itakuwa Hapsatu suka fara duba yaya zasu fara aikin gidan yanzu
Cewa su Nauphal tai ina zuwa kujirani zanje in siyo mana tsintsiya da allura in duba wannan kafar
Toh Ummerh saikin dawo
Toh ngd
Futa tayi taje wani shago data gani acan bayan unguwar su tasiyo abunda duk zasu bukata sannan tadawo gidan
Lokacin sukam harsun fara futo da “Yan tarkacen da suke cikin dakin harda wasu kodaddun labulaye da tar kacen kwanuk da tukwane da farantai da wasu fasassun robobin ruwa da kuma jarka guda 6 yalaye nazuba ruwa

Cewa tayi toh wadannan kayan banamu bane amman bari inje in gayawa Babah sa’idu cewa munga kaya yaya zamuyi dasu

Toh ummerh kibari muje mugaya masa mana
A’a kubari inje dan yanzu nikam tsoron garinnan nake sosai wlh
Toh ummerh
Futa tayi tana futa tag………..

*** *** ***

A6angaren su Balaraba kuwa haka suka koma gida babu wani farin ciki ko kwanciyar hankali atare da ita
Koda gari ya waye sun shiga tashin hankali sosai dan dukkan tashoshin garin Rano lungu da sakonsa saida suka duba amman babu su Hapsatu babu dalilin su ko kuma alamun su

Hankalinsu yayi matukar tashi dan Alhaji daya dawo yatambayi Hapsatu
Sun rasa mezasu ce masa
Kawai sai fauziyya tai katsa landan tace muma bamusan inda ta tafiba
Tun jiya mun kasa bacci sbd nemanta da muke
Wlh mun gaji da halin wannan banzar yarinyar ta tafi yawon karuwancin ta sanann tabarmu da nema haka kawai
Kema dai kyafad’a haka kawai muyi tafaman wahala akan karuwa
Wlh mama wadda batasan ciwon kantaba ma kuwa wadda bata da aiki sai karuwan……….
Wani wawan mari aka dauketa dashi wanda yadauke dukkan wani jinta kanta ankara aka kara dauketa da wani marin saida yayi mata kwarara guda 4 sannan yakyaleta shima ganin tafadi kasane hancinta yana futar da jini shine yasashi kyaleta
Duka yakai mata da kafa yana fadin akwai wanda yakaiki karuwanci ne eyeee
Tunda anriga angur6ata miki rayuwarki
Kuma kisani wlh dukkan sharrin da ake kullawa akan Hapsatu kanku zai koma
WLH IN GAYA MIKI
DAN HAKIN DAKA RAINA SHINE ZAI TSONE MUKU IDO
Karkuyi tunanin kuna cutar da ita da kaninta dan ganin bata da kowa
Toh ina mai tabbatar miki da cewa Allah yana tare da su akoda yaushe
Kuma dukkan wanda Allah yatsaya masa to bashi dasauran Kuka
Har lokacin dukanta yake kamar jaka
Da gudun tsiya s…….

Hallmarht ce????????????
[04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah????????????: ✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨

          ????NAH????

SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????

????— 3⃣1⃣&3⃣2⃣

???? page

Da gudun tsiya sukayi kansa suna cewa bazaka denan dukan taba ANAS wannan wani irin haukane eyeee

Gajiya sukayi dan sunkasa kwatarta daga Alhaji har mama Balaraba sunkasa amsarta dukan ta yake kamar an aikoshi

Balaraba ce tace wlh ANAS idan baka daina dukan taba saina tsine maka kaji narantse wlh kuma baka isa ka karyamun rantsuwata ba

Jin hakan ne yasashi tsayawa da dukan nata Amman fa tadaku sosai dan bakaramun duka yayi mata ba
Dan tunda take aduniya bata ta6ajin irin wannan dukan ba gashi kuma yau ta d’an d’ana

Kamata sukayi itada Alhaji sukayi waje dan zuwa asibiti dan tahancin ta, tabakin ta, ta goshi, duk jini zuba yake
Sannan  gawani nan yana zuba ta kasanta kamar an6alloshi
Dak'ar take iya taka kafarta saboda muguwar azaba
Amugun wahale take dan jitake kamar jiri zai dauketa babu yadda suka iya dole yasasu suka je chemist dan afara dubata kafun suje asibitin

Da’kar suka shawo kan Baba iyabo yadubata sosai yayi mata kokari sosai nan yake sanar da Balaraba tana da ciki dan Allah yataimaka sun kawota da wuri dabasu kawota da wuriba daya zube

Tashi tayi amugun razane tana fadin CIII MEEEEEE…………

*** *** ***

Tana futa taga abokin Baba sa’idu gaisawa suka karayi take gaya masa kayan dasuka gani acikin dakin nan yace mata wlh matar data kama haya agidan ce tayi arziki shine tace duk kayan dasuke shiki tabar mana tofa shine muka tsinci na tsinta mukabar sauran
Kiyi amfani dasu kawai in kina so Wanda basu da amfani kuma ki xubar
Toh Baba ngd sosai Allah yasaka da alkairi
Amen “Yar nan
Komawa tayi cikin gidan ta tarar harsun fara sharo dakunan da ban dakin sunata cire yanar
Ita ma fara tayasu tayi aikin dansu gama da wuri saida suka share ko Ina nan suka kwashe sharar suka saka abuhu
Lokacin da suka bude kichin dinne sukayi mamaki dan jerene aciki nakomai tsaf Ba’ata6a ba harda sababbin kuloli acikin sa fara dubawa sukayi ahankali nan sukaga harda shinkafa buhu 2 da taliya da maka roni
Kayan avunci sosai ne acikin gurin harda mai doyarce dai tafara hun huna da dankali saidai 6ura da sukasha sosai
Ce musu tai bari inje in gayawa Baba kayan dayawa sosai fa

Sukace Toh
Tafitai gidan tayi sallama
Amsa mata sukayi nan take fada masa komai akan kayan dasuka gani sosai dana abunci
Babane yace mata kiyi amfani dasu Hapsatu wlh muma mun samu arziki sosai acikin wannan gidan
Wadannan Allah yayi rabon kine Hapsatu karki damu kinji
Toh Baba ngd sai anjima
Sannan ko kinga wani abun ma karki dawo kidauka kawai
Toh Baba
Tashi tayi danta futa kafarta ta rike gam takasa takata
Salati tasaka
Baba Hasiyace tace lpy “Yar nan meyasameki
Wlh Baba kafatace nakasa taka ta
Assha LAHAULAH
BARI MUGANI
zuwatai tafara tai maka mata tazauna sannan tace muga kafar taki
Mika mata tayi
Inna lillahi ni Hasiya mezan gani haka saikace ba mutum ba dawannan katon hakin akafa fuwanki har kusan 3 Amman kina tafiya haka nan

Binta Binta kina inane 

Ganinan Babah lpy nikam wannan kira haka
Dauko mun matse fata da leta da kuma allura maza kinji yi sauri
Dauko mata tayi dan aleda take ratayesu tasa asaman sip

Yawwa daukarsu tai ta konasu da letar nan sanan tadauki wata auduga tagogesu tas
Ahankali tafara cire mata sartsen duk inda tacire sai yayi feshin ruwa sosai
Haka saida tacire mata su tsap sannan tafara buda gurin da allura tana yankewa da sabuwar rezar data bude yanzun
Hapsatu jitai kamar ancire mata wani mugun nauyi daga kafarta
Danjitae sakayau kafar tata

Baba hasiyace tace muga dayan kafar taki dubawa tayi nan guda dayane sartsen Amman yajah ruwa yakumbura sosai
Shima matseshi tayi tana fad’in sannu kinji “Yar nan kinyi jarumta sosai
Nan kamar tar gad’e mlm zoka duba mata dan inajin nan kam tar gad’e ne
Toh tasowa yayi yafara duba mata
Yace ey wlh tar gad’ene kam
Wai nikam “Yar nan a ina kikaji Wadannan ciwukan sai kace wadda tai ya’ki
Murmushi tayi kawai batace komai ba
Sannu sukaita binta da ita sannan
Baba Hasiya tace dan huta kafun kitafi
To Baba zama tai tadan huta har wata gajiya taji tana saukar mata
Takai kusan minti 40 sannan tace bari in tafi Baba
Haba dakin kara hutawa itama kafar tasamu salama ai ko
Bari ma in kira binta ta tai maka takai miki ruwa ki watsa ko kyaji dadin jikin ki
Aa babah….
Wani A’a
Kina inane Binta
Gani nan Baba kayan make up din nan nake kwashewa
Ok toh yiki kwashe kizo
Toh Baba
Bata Jimaba tazo
Yawwa “Yar kirki kawo mata ruwan dumi tadan watsa
Ki saka mata aban d’aki
Aa Baba bari inje aiki mukeyi nabarsu sukadai karsu zata ko 6ata nayi sufuto
Aaaaaa”aaaaaaa ‘aaaaa wlh hakane kam bari inkun gama Binta takawo muku ruwan zafin kawai kuyi wankan
Toh Baba ngd sosai Allah yakara lpy
Ameen “Yar nan
Wai nikam yasu nan kine
Murmushi tai tace Hapsatu sunana
A’a kice mesunan sirikatace
ALLAH yabar kauna sirika
Murmushi ta’karayi tace amun Babah

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button