DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Hallmarth ce ????????????
Keep waiting my fan’s????‍????‍????‍????????‍????‍????‍????????‍????‍????????‍????‍????‍????????‍????‍????????‍❤️‍????‍????????????????????????????

Love you [04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨

          ????NAH????

SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????

????— 3⃣9⃣&4⃣0⃣

………….. Haka sukaita fad’i tashi akan suga sun gina kansu sosai hapsatu take ‘kori ganin ta gina rayuwar yaranta guda biyu

Kasuwanci kuwa sosai yake gara mata gasu Fahat, Nauphal suna suna goyon bayan dukkan abunda ta bullo musu dashi
Har kwantaina ta siya ta shago anzuba kaya sosai acikin sa
Runfar kuwa anan Nauphal yake saida so6o, jusi, lemon Ginger, kunun aya, da kayan snack’s kowanne akwai
Suna girmama dukkan wanda suka had’u dashi
Agida kuwa Hapsatu tanayin abunci dafaffe nasiyarwa ko kwano nawa ta d’aura saiya ‘kare kafun dare

Yau yakama ranar alhamis suna zaune aphalo lokacin Fahat ma ya rufe shago yadawo gida
Bayan sunci abunci dan akwano d’aya sukecin abunci
Hapsatu ce takallesu tace Fahat, Nauphal kubani aron hankalin ku da nutsuwarku
Atare sukace toh Ummerh
Hapsatu tace inasan ku koma mkrnt yaya za’ai
Mkrnt Ummerh
Ey kuke had’a baki mkrnt nakeson ku koma tunda Allah ya hore mana kuma muna da halin da kowannen ku zai koma mkrnt in sha Allah ta dai2 tamu
Toh Ummerh ni takadduna basanan suna gida
Toh yanzu yaya za’ai
Ummerh kawai in hkr
A’a Fahat zuwa zamuyi kad’aukosu
Ummerh so kike suganeni
Aa Fahat ba haka zamujeba ai nasan yadda zamuje babu wanda zai gane ka
Toh Ummerh
Gobe juma’a saimu tafi da wurwuri, yadda zamu dawo acikin lokaci
Toh Ummerh
Kai kuma Nauphal sai mun d’auko nashi sannan zamuje taka tunda kai nataho maka da naka
Toh Ummerh Allah yakaimu
Dahaka suka kuma kama hira sai wajen 12:00pm sannan suka tafi kowa ya kwanta
Koda gari yawaye kamar yadda tafad’a haka kuwa akai dan sun gana had’a kayan lemon Nauphal sun fasa ‘kan’kara akai sun rurrufe kulolin
Hapsatu kuwa fankasu kawai tai sai wainar da suka soya tayi miya suka zuzzuba akula aka sakawa Nauphal acikin shago sannan suka d’auki hanya itada Fahat wanda aka canja masa kala tahanyar yi masa make up irin na buzaye itama Hapsatu tayi shiga irin ta buzayen
Sosai kamar su ta canja suka tafi tasha, Nauphal kawai suka bari agida suka kama hanya su kuma
Basu dad’e da zuwaba suka samu mota aikam 7:00am suka tashi
Sund’ansha hanya kafun suka shiga cikin garin abuja, babu wani 6ata lokaci suka samu mota sukai unguwar wuse2 a’kofar gidan aka saukesu suka biya sannan suka isa bakin ‘kofa suka fara nock, baba mai gadi ne yace waye, sukace mune, daga ina kuma, hjy tasan da zuwankune?
Ey, toh bari in bud’e muku
zuwa yay yabud’e musu suka shiga, saida suka gaidashi sannan suka wuce direct phalon gidan suka tunkara
Lokacin da suka shiga babu kowa acikin phalon sallama sukai amsawa mai aikin tai sukace hjy fa, tace tana tare da ba’ki
Toh sai yaushe zata futo, gaskiya ban saniba
Toh inta futo kice mata tanada ba’ki, toh shikenan, ruwa da lemo takawo musu ta futa
Fahat ne yatashi yayi wajen part din mom d’insa yana turawa yaga gurin yayi datti sosai yayi 6ura kwallace ta zubo masa ya share sannan yashiga d’akin sa yafara dubawa, inda ya ajiye takaddunsa yaga babu, hankali tashe yashiga cikin d’akin mom d’insa anan yagansu awatse dan ranar dazasu d’aukesa ranar ne yaje neman aiki bai samuba
Haka tafara tattara su yana had’awa dukkansu yagansu acikin ‘yar jakar data zuba anan yamayar dasu yad’uki wayarsa daya ganta acikin durowa Wadda shiyay tunanin ma yasaida ita ashe tana nan
Futowa yafara shirin yi sai yaji muryar amaryar daddy ita da ‘kawayenta suna hira harda shewa da’lama futowa suke
Maza yay yasaka jakar takaddunsa acikin ‘katuwar jakar daya taho da ita yasassaka komai aciki sannan yad’an leko yaga suna bakin kofar phalo suna saka takalma
Futowa yay ahankali yalalla6o yabar bakin part d’insu
Amaryar daddy ce taganshi tace kai daga ina suwaye ku kuka shigomun gida har phalo
‘Kawayen ne suka juyo sukace daga ina kuke
Hantar cikin Hapsatu saida ta kad’a
Kai kuma meya kaika wannan part d’in waye kai…………….

**** **** ****

Cikin sauri tad’auko jakarta tabud’e zata d’auki kud’in tabawa likitan Amman me babu kud’i babu dalilin su
Ihuuuuu ta rapka saita sulale tafad’i ‘kasa sumammiya
Likitanne yayo kanta yana fad’in baba, baba, lpy kuwa
Fauziyya itama kan mama Balaraba tai tana kuka d’aukarta akai aka d’aurata akan gado aka fara duddubata da’kardai tadawo dai2 anan likita yasallamesu, yace maza tabiyashi kud’in dubata dan kati dana magani da allurar da akai mata
Tace bata da kuma ita yanzu batasan yaya zatai ba ankwashe mata kud’in data taho dasu gaba d’aya
Da’kar likitan nan yahakura da kudin maganin daya bata suka tafi, shima saida mutane suka saka baki sannan yabarta
Haka suka tafi gashi babu nasara kuma babu kud’i, kuma ciki yana nan ba’kin cikin ne yayi wa mama Balaraba yawa
Lokacin da sukaje tasha basu da kud’in mota dan dama dan canjin dayake hannun Fauziyya ne sukai kud’in zuwa tashar dasu haka suka wuni tsurrr acikin tasha basu samu wanda zai biya musu kud’iba
Daga ‘karshe bara suka kama itada Fauziyya da’kar suka samu d’ari 500 suka siyi abunci suka d’an ci na d’ari sannan suka roki alfarma da’kar suka yadda akan zasu kawosu dari 400 amman saidai suyi goyo amaleji
Haka suka hkr dan babu yadda zasuyi, lokacin da suka shiga garin rano abakin hanya aka saukesu da ‘kafa suka isa gida duk sun gala baita sosai dan ba’kar wahala
Suna zuwa abunci suka d’auko suka kamaci suka sha ruwa agurin sukai bacci
Da gari yawaye balaraba tashin Fauziyya tai suka tafi gurin nakan tsauni, nan suka gaya masa komai daya gabata, yace musu mafuta d’ayace ta auri jazuli sai akwantar da cikin idan ankwana biyu sai atashi cikin
Balaraba tagirgiza dajin abunda nakan tsauni yace ta’auri jazuli kuma nakan tsauni nida nakeson ayi wacce za’ai Fauziyya ta auri doctor faruq din nan
Hhhh hhhh aikinbar gini tunran zane abunda yafi sauki kenan amman indai kinasan ta auri wannan likitan saidai kikawo ba’kin alade da mage da bunshuru

Amman da sharad’i cewa saita auri jazuli ta haihu tukunna idan ba hakaba wannan aikin dazamuyi bazai yuyu ba
Toh zanyi kamar yadda kace, haka suka taho duk ba’kin ciki yayi mata yawa, wai Fauziyya ta auri jazuli wannan d’an tashar da ba’asan asalinsaba, dan shaye shaye kuma
Wannan wace irin ‘Kaddarah???? ce
Tun kafun su’karaso sukaje shagon su jazuli amman baya nan haka suka dawo badan tasoba
Tabarwa Anas sallahun inya dawo agaya mata, ace tana neman sa
Sai wajen karfi, 10:00pm sannan suka shigo shida jazuli, sallama sukai anan kofar daki suka tarar da su azaune
Kallon Anas tai tace, toh ngd maza jeka , Toh mamah sai anjima
Futa yay abunsa kallon jazuli tai tace zauna mana tsinanne, zama jazuli yay duk ya tsorata dan yasan Fauziyya tarugada ta tona masa asiri
Zama yay ahankali kallonsa tai tace yawwa magana nakeson yi dakai
Too…… Too…….. Toooooooottttt…… tooo ina jinnnnnki mamah
Maman uwaraka, inasan ka’auri Fauziyya sannan asatin nan nakeson ad’aura aure ku
Aure kuma
Tabbas aurenta zakai dan bazaka zubarmun da mutunciba katozartani agaban jama’a
Wulakanci kamar yaya kuma
Ey kaje kai mata ciki shegen gora sannan har kake tamabayar wani abu
Ai mamah ita tazo tace in rage mata zafi bani nace tazo ba
Inna lillahi wa inna ilaihi raju’un yanzu abunda kika aikata kenan Fauziyya kinsanda kinasan hakan ai saiki gayamun in samar miki miji kiyi aure, amman saiki zubarmun da mutunci na
Kiyi hkr mamah
Hkr’n uwarki
Tashi kiban guri
Kai kuma ina zaka sakamun “yata dan wannan aure yazama dole sai anyishi shine rufun asirina danaku
Toh nidai bani da inda zan ajiyeta sannan kuma bani da kud’i amman idan kece zaki kama mana haya to sai ayi wannan auren idan kuma ba haka ba saidai ahakura, dan ni nan ma gaba zanci dankar asirina yatonu
Haba…. Habaaa….. Aibaza’ai hakaba jazuli kabar zancen tafiya
Ninan zan nema muku haya koda d’aki d’ayane da band’aki da kicin
Aaaatooooo danni uwatace zata gindayamun doka kawai inbi
Toh yanzudai ka shirya asatin nan za’ayi auren nan
Toh ni nayi nan, Tashi yay yafuta abunsa
Mamakine yakamata tana tunanin yadda zatai haka taje tafara buga nan buga can tana neman yadda zata tara kud’in dazata kama musu haya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button