DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL


A6angaren su Hapsatu kuwa tun da su binta suka futa taji yarinyar ta burgeta amman batasan sunan taba
Sai wajen 8:30 sannan suka futa agida suka kama hanyar mkrt dazatakai su
Basu samu wata matsala sosai ba saboda yanada result mai kyau Fahat haka yasamu gurbin karatun sa na masters cikin kwanciyar hankali dan komai anyishi cikin sauki dan ta jajje Makarantar yafi sau akirga tun kafun takaishi
Shima Nauphal mkrnt takaishi inda anan zaiyi ss 2-3 haka tadawo gida ita kadai tanata sauri, dan tasan yanzu ana nan ana jiranta
Kamar yadda tai tunanin kuwa hakance tafaru mutane suna nan dan’kam yan siyan abunci damasu siyayya ashago
Bintuce tazo siya itama tayata tai ta shiga shagon ta sallami wasu ita kuma tashiga gida ta sallami masu siyan abunci haka ta wuni sai wajen 1:00pm sannan Nauphal yadawo shiya amshi bintu ashagon bayan yayi sallah

Washe gari kuwa tun da wurwuri sukai shirinsu suka tafi sosai sukejin dadin yanayin rayuwar tasu

*** *** ***
A6angaren su Mama Balaraba kuwa, lokacin da Jazuli yafara shafa mata fuskar nan lokacin tafarka dan ganin waye, Jazuli tagani atsaye akanta yana abunda yasaba, furgigit tayi, tace kai mahaukaci, matsa mun daga guri kanaji nako, amman ina shibai san ma tanayi ba cigaba yay daga inda yatsaya abunsa koda wasa bai matsaba
Murmushi yay yace, haka kikace inyiwa Hapsatu toke zanyiwa yanzu janyota yafarayi jikin sa da’karfi, tana kwacewa, ihuuu take, dan yafara yaga mata rigarta, dasauri Fauziyya tashigo kiching d’in, tana ganin abunda yake faruwa tad’auki muciya ta rafka masa ahannunsa da dukkan inda tasamu ajikinsa, saida yaji wuya sannan yafad’i, Mamah Balaraba kuwa ai cikin sauri ta bar gurin gida ta nufa ko takalmi babu gabanta yanata fad’uwa

Fauziyya ma gidan takama hanya ta tafi dan bazata iyaba dawannan jarabar, kowacce rana kalar tata daban,
Haka rayuwar Fauziyya taci gaba da dagulewa sosai take data sanin wannan rayuwar tata dakuma zalincin da suka aikatawa su Hapsatu

Yau watanta 4month agidan jazuli amman bata sauya zaniba yadda yaga dama haka yake rayuwarsa kuma sai abunda tagani kawai

yaune yakama zasu koma gurin boka dan yace tanayin wata 4 akoma amman Jazuli ya ‘ke’keshe idonsa yace sam shi babu inda za……….
[04/02, 7:59 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨

          ????NAH????

SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????

????—4⃣5⃣&4⃣6⃣

………..Yace sam babu inda zasu haka sukaita rokonsa ya’ki daga karshe dai dabara sukai suka tafi gidan su Hapsatu sukace Alhajine babu lpy taje ta dubashi, shine ya yadda

Haka suka tafi tana zuwa wajen nakan tsauni yace ai cikin nan da aka kwantar bai kwantuba dan yanzu yakai wata 7 
Dafe 'kirji sukai atare wata nawa, yace 7 toh yanzu menene abunyi, ai babu tunda mun shimfid'a mata doka ta'ki bi, munce duk yadda zatai tayi sukwanta tare dan cikin ya kwanta amman takasa, toh yanzu babu yadda zan muku saidai ince, kutari gaba, akan aikin likitan nan amman dai kam yanzu abunda yafaru yarigada yafaru

Kutashi kuban wajeeeee, kutashiiiiii nace ko bakwajiiiiii naneeeee
Dasauri suka tashi cikin kuwa kafun suzo gida yafuto sosai ya zazzago dukkan abun duniya ya damesu, duk inda suka wuce sai an nuna su da baki, wasu kuma da hannu, ana zum6an su

Lokacin data shiga gida akan idon Jazuli suka shiga dan haka yayi ‘kwafa yad’auke kai
Saida ta dawo gida sannan yabita dan yayi al’kawarin saiya lakad’………….

*** *** ***
Dan komai yana canjawa yadda yakamata, bayan tafiyar sune wasu motoci suka tsaya abakin ‘kofar gidansu, manyan mutanene suka futo daga cikin motar, babu wani 6ata lokaci aka yi Sallama abakin ‘kofar gidan
Amsawa Hapsatu tai, mai sallamar yace ana Sallama da matar gidan, toh ganinan, itadai tana amsawane kawai amman zuciyarta sai tsinkewa take, futowa tai da hijabunta akanta taga macece da kuma namiji sai yarinyar data siyi, waina da fanke jiya
Murmushi tai tace bisimillah kushigo mana, shigowa sukai ta shimfid’a musu tabarma asoron gidan suka zauna
Mai aikin Nusaiba ce da manager mom d’in ta
Saida suka gaisa sannan suka d’anyi jimmm kana suka fara mata bayanin akan komai daya kawosu, na sunasan wani daga gidan yazo yana yiwa Nusaiba girki sannan kuma za’ana biyan sa naira dubu 100k duk wata
Murmushi Hapsatu tai tace kuyi hkr wlh banida “ya mace agidan nan duk mazane kuma suna zuwa mkrnt sannan kuma ni inada ayyukan yi sosai acikin gidan nan danazo narin’ka mata, kuce da hjyr ta tayi hkr
Rokonta suka farayi akan ta tai maka, hakurin dai ta’kara basu, akan bazata samu yi musu abunda suke da bu’kata ba, haka badan suna soba suka tafi amman da tunanin yadda za’ai hjyr su ta fuskanta dan tace duk yadda za’ai karsu sake sudawo mata babu mai aiki

Koda suka koma gida hakadai suka shiga da fargaba acikin ransu da kuma tunanin yadda za’ai suyi mata bayani, dan sun san Allah ne kad’ay zai cece su agurin ta, da’kar idan bata kore su daga aiki ba

Suna shiga phalon da ita sukai tozali tana zaune akan kujera ‘kafa d’aya kan d’aya abunta tana ta cin apple
‘karasa shigowa sukai suka russuna agabanta, kallon su tai awula’kance tace lpy meya faru ina kuma Nusaiba take
Am….. Ammm… Am… Tana nan shigowa, Amm.. Amm… Amman abunda yafaru shine ta’ki amuncewa da sa’konki, kwashe dukkan yadda sukai yayi ya gaya mata, amugun fusace ta tashi tace sam wannan ai zancen banza ne yaza’ai ace mace kamata ta tura da sa’ko amman akasa samun amsa mai dad’i, kutashi maza kuje kugaya mata wacece ni sannan ta fad’i kuma Ada din kud’in datakeso zanna biyanta duk wata

Hjy wlh mun gaya mata amman tace a’a muyi hkr wannan ma abunda takeyi ya isheta rufun asiri
Whatt kutashi kuje na sallame ku maza tunda har anrasa mai kawomun farin cikin “‘yata acikin ku dan haka ku ‘kara mai maza nabaku minti 5 kubar gidan nan
Dan Allah kiyi hkr wlh bazamu sakeba ko ina ne zamuje mu samo mata duk wadda takeso amman karki rabamu da aikin mu, Outtttt, tafad’a da ‘karfi
Babu yadda suka iya haka suka futa daga gidan dan idan suka tsaya zata saka ayi musu korar karene
Zama tai tana lila ‘kafa akan kujera tana tunanin yadda zata kaya atsakanin su da Nusaiba dan tasan cewa zatai abarta tana siyan abuncin gidan, ita kuwa bazata bari tanacin abuncin wannan ma’kas’kancin gidan ba

Abakin ‘kofa Nusaiba ta had’u dasu suna shirin futa da jakun kunan su ahannu, kallonsu tai tace ina zaku kuma Aunty safiyya, hjy ce takoremu, akan me, gaya mata duk yadda akai tai, sbd wannan Za’a kore ku sai kace ku kuka hanata zuwa, Maza ku koma bakin aikin ku, zanje in sameta
Toh hjy mun gode
Kallon ‘kawarta tai kalisat, tace muje kalis, ok Nusy
Atare suka shiga phalon suna tafe suna hira harda tafawa, da Sallama akan labban su suka tura ‘kofar phalon, tana kishingid’e akan kujera abunta tana kallon TV

Zama Nusaiba tai kusanta, kalisat kuna ta gaidata, Amsawa tai da kulawa tace, a'a kuna tare kenan, eyyy mom yau kun'ki zuwa school ko, mom babu abunda sukeyi ai shi yasa, ok tom kunde'ki zuwa kawai amman ana karatu tunda ba hutu kukai ba
Sallama hjy safiyya tai tashigo, kallon ta mom tai da tambayoyi fall bakinta, daga ina kike,  waya dawo dake, me kikazo yi kuma, uban wa yabaki damar shigomun phalo

Mommmmm wannan tambaya haka Wacce zata amsa daga ciki, ni na bata dama nace su koma bakin aikinsu, Amman daughter yaya zakiyi haka bayan kinsan duk wanda nasa aiki ya’ki yimun “‘karshen sa kenan

Nasani mom amman kibarsu kawai, toh kefa yaza’ai da cin abuncin naki, mom na hakura basai naciba, really, yes mom, ok thank you dear, all is for you my dear mom,murmushi tai, itakam Nusaiba tashi tai takama hannun ‘kawarta sukai part din ta

Ajiyar zuciyah ta sauke tace Allah yasoki, tashi kiban guri, tafiya tai itama part din datake ajiye kayan ta danta maidasu inda suke

**  **   **

Agida kuwa koda suka tafi aikin gabanta Hapsatu taci gaba dayi dan ita bazata tafi tabar aikin ta da takeyiba da yaranta ta tafi wani gurin ba
Koda suka dawo tagaya musu duk abunda yafaru sunji dadin yake hukuncinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button