DAN HAKIN DAKA RAINA COMPLETE NOVEL

DAN HAKIN DAKA RAINA???? COMPLETE NOVEL

Hallmarth ce ????????????

Keep waiting my fan’s????????

Hallmarth ce ????????????
????????????????????????????????????
????????????????????????????????
DASHEN ALLAH
WRITING ASSOCIATION

‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????
Story and written by

*SADIYA •A• UMAR*

{UMMUH FATEEMAH}

????—

8⃣7⃣&8⃣8⃣

……………..’Dan gidan Alhaji Hamisune yaketa kuka yana kiran Alhaji

Futowa yay yace lpy meya faru kuma, kaka Hajja ce da daddy sukai accident ankaisu asibiti

 Salati suka saka sannan suka futo motoci suka shiga sukai asibitin acan suka tarar da an'ki amsar su ance sutafi cikin kano bazasu iyaba

Doctor faruq ne ya'karasa ya saka aka shiga dasu cikin OPERATION ROOM

Sun kwashi sama da awa 5 akan su kafun aka samu nasarar ceto rayuwarsu

Sun jigatane sosai dan shi Hamisu yasamu karaya 5 acinya dai gocewa dayay ahannunsa da kafad’arsa

Fuskar sa kuwa in kaganta bazaka iya ganetaba sam dan ta murzu

Kaka Hajjah kuwa ta samu gocewa a'kugu sannan kuma 'kafarta guda d'aya ta cire dan wata mutar ce ta murje mata ita tass da hannunta guda d'aya
  Sai kuma spinal cord d'inta data samu matsala 
   Ta bugu akanta sosai dan da'kar aka samu aka tai maka mata jini baije kwakwal wartaba

   Saida sukai mata tankwall sannan aka samu nasarar yi mata aiki

 'Dakin hutu aka kaisu sannan aka dawo dan biyan kud'in aiki dana magungunan su


Uncle sulaiman ne yabiya komai sannan aka cigaba da kula dasu

Sai bayan Isha’i sannan suka dawo gida inda akabar matar Hamisu tana kula da kaka Hajjah shikuma babban d’anta yana kula da baban sa

Uncle sulaiman ne yace dama munzone muce abar wannan zancen auren nasu Umar dan gaskiya bazan bari d'ana ya auri dangin wannan matar ba

Babu komai gaskiya nima bansan haka sukeba dabazan kawo kubama daddy

Hakadai aka bar magana aka basu sauran kayan lefen su

Amman uncle sulaiman yace a’a abarsu sun yafe taci gaba da amfani dasu

Tafiya sukai Alhaji yanata musu godeeya, nan Ibrahim yace bazai tafiba zai zauna awajen mahaifinsa nanda 2weeks sannan yadawo

Basuyi masa musuba suka barsa anan suka koma gida hjy Habiba banda kuka babu abunda take

Saida Ibrahim yayta bata ha'kuri sannan taha'kura 
Suka tafi

Suna shiga gida Mm Balaraba tafara kuka tana cewa Alhaji kayafeni kozan samu salama acikin rayuwata

Kallonta yay da mamaki yace meya faru Balaraba lpy kuwa, ni babu abunda kikai mun

A'a Alhaji baka sanibadai amman dai ina 'kara neman afwaraka dan Allah tun kafin ingaya maka

Mezaki fad’amun inajinki
Zama yay shida Ibrahim akusa da ita dan ‘kafarta d’aya tafara wari amman dai haka suka zauna sbd tana zubar da wani ruwa ne

Kallonsa tai tafara basa labarin abunda kakah Hajja ta aikata masa tun daga mutuwar kakan sa har zuwa mutuwar iyayen sa da rabasu datai shida 'yan uwan sa, dakuma yadda suka sace Ibrahim suka kaisa cikin dajin duk tagaya masa

Sosai Alhaji yake kuka shida Ibrahim musamman mutuwar iyayen su wanda tasakawa wuta tacisu sosai kafun aka tai makesu

Dakuma kakansa data rin’ka bawa guba yanaci harta kasheshi

Yama kasa yi mata magana dan baisan ma ta ina zai faraba idan yace zaiyi maganar, shiyasa yay shiru saidai hawaye gashi tarabasa da matarsa da "ya"yansa ko a ina zai gansu ALLAHU A'ALAMU 

 Balaraba kitashi keda "ya"yanki kubarmun gida nasakeki saki 3 kutafi Allah yasakamun abunda kukai mun keda Kakah Hajja bazan yafe mukuba kun cutar dani sosai 

 Anas da Fauziyya da suke tsaya suna jinta kuka suka saka Anas harda fad'uwa dan tunani yake shin sud'in musul maine ko kuwa 

Anya akwai zuciya acikin ‘kirjinsu
Yayi nadamar kasan cewarta mahaifiyar sa sosai yake kukan ba’kin ciki

Sallama sukaji anyi 

Juyawa sukai dan suga waye
Abun mamaki wasu mutanene guda uku da j………….


……….Hakama Nusaiba ta dage wajen zuwa Makarantarta tamaida hankalin ta sosai wajen karatun ta

Ga soyayya dasukesha mai tsafta itada Nauphal

A6angaren saurayinta muktar kuwa saidai zumunci kawai dan tagaya masa yayi ha’kuri anbada ita

 Awajen Ummerh ta kuwa bata ta6a sanar da wani tana wannan makeken gininba nagani na fad'a 

Part 4 tai ko wanne ya amsa sunan sa, sai makeken Restaurant data bud’e akusa da gurin

‘Dayan gurin ne data siya aka fara gina musu asibiti bata yi nisaba tasa aka tsaya dan a’karasa wancan gine ginan sannan

 Wasa² Fahat yakammala karatunsa yayi komai harta nema masa aiki dan daddy Nusaiba ne yashige masa gaba yasamu aikin


Shima Nauphal saura wata 10 sukammala karatunsu

Sosai yake kewar Nusaiba amman basa d’aga musu ‘kafa ko kad’an dan lokacin wayama bashi dashi wani lokacin ma sai suyi kwana biyu basuyi waya ba

  Awajen Hapsatu kuwa ankammala mata ginin gidan ta tsap kowane part yasha gyara ansaka masa komai na bu'kata abunda yarage kad'anne acikin gurin kaya masu tsada ake zuba mata akowanne 6angare 

Sannan tazuba ma’aikata kota ina suna kula da gidan yadda yakamata

Wani lokacin ma bata samun damar zuwa ganin abunci saidai ma'aikata suyi kawai

Manya²’n masu kud’i suke fakawa siyan abuncin ta kota ina sunanta yad’aukaka daga gari² ake bata Oder abuncin dinner kona paty

Sosai tayi kud'i naban mamaki, harta gyarawa Baban Bintu da abokin sa gidansu tazuba musu kayan more rayuwa

Amman abun mamaki ita ta’ki tashi daga wannan gidan sam saidai gyarashi datakeyi kawai

Komai Nusaiba takeso tanayi matashi babu abunda tanema tarasa ita kanta yanzu takoma makaranta Hapsatun 

Kuma tana fuskantar komai sosai yadda yakamata 



 Fahat da Bintu sun d'inke dan abun yana bata mamakima dan ita tunanin ta kaliss yakeso amman saitaga ashe shi Bintu yakeso 



  Har ankai kud'in nagani inaso, da kuma kayan saka rana


 Motar Mom d'in su Nusaiba ce tai parking a'kofar gidan su Hapsatu tana mamakin yadda gurin yake cike da manyan masu kud'i da alhazawa suna cikin rumfar cin abunci ga manyan motoci kashi²

Gurin dabata sanshiba dazatace ba gurin bane dantasiye gurin gaba d’aya ta maka gida da gurin cin abunci makeke

Sosai abun yake bata mamaki sosai dan gani take kamar a film ne sbd shekararta ta biyu kenan rabonta da gurin amman yasauya sosai

Abunda bata ta6a tunani ba
WANNAN SHINE ‘DAN HAKIN????DAKA RAINA????????

Sakkowa tai tana yatsine fuska tana kallon su gaban tane yafad'i ganin............✍????✍????✍???? 

Keep waiting my fan’s????????????????

Hallmarth ce????????????

[04/02, 8:03 AM] Ummuh Fateemah????????????: ????✨????✨????✨
✨????DASHEN ????ALLAH????✨
WRITTER’S✍???? ASSOCIATION
https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7
????ALKALAMI ✍????YAFI TAKOBI????️
بسم الله الر حمن الر حيم
✨DAN HAKIN???? DAKA RAENAH????????✨

          ????NAH????

SADIYA ABDULLAHI UMAR
????UMMUH FATEEMAH????

????—

8⃣9⃣&9⃣0⃣

……………Gaban tane yafad’i ganin mahaifinta da kuma daddy’n Nusaiba agurin sunacin abunci sosai hankalinta yatashi

‘Karasawa tai wajen amugun fusace takallesu, cewa tai amman dai anyi asara wlh, SAGIR yanzu anan kakecin abunci sbd ta6ewa karasa a ina zakaci abunci sai gurin nan

Mahaifintane yakalleta yace meyake damunkine ke waya kawoki nan wajen

Babah ka kyaleni da wannan tambad’ad’d’en mana inji uwar me yazoyi nan gurin

Kiwuce nace kitafi bakyaji nane 

Wlh babu inda zani saidai mutafi tare daku dan wlh bazanje ko inaba

Mahaifintane yakalleta yace in kika ‘kara magana d’aya anan saina tsine miki

Kallonsa tai tace kadad'e baka tsinen ba indai akan SAGIR ne wlh babu inda zani saidai mutafi tare kanaji nako

Nace bazaku tafi tareba tare kuka zo, kiwuce nace

Bazan wuceba wlh babu inda zani
Kallon SAGIR yay wanda kunya ta isheshi yasunkuyar da kansa ‘kasa yace muje SAGIR

Kama hanya sukai suka tafi tazo tasha gabansu tace kashiga motata mutafi gida wlh idan ba hakaba saidai mutafi tare duk inda zaku

Mutanene suka farayi musu zobe dan haka yace tashiga motar ta shima yashiga tasa saisu tafi gidan gaba d’aya

Amman ‘kememe ta’ki tace saidai driver yaja tasa sushiga tata sutafi tare
Dan kar yazubar da mutuncinsa yasaka yashiga suka tafi tunkafu mutane sugane me ake ciki sosai

Jan motar tai sukai gidansu inda shima babanta yake bunsu abaya har suka isa gidan

 Sunayin parking tafuto hannunsa taja zuwa cikin gidan tana zuwa phalo ta wancakalar dashi tace uban me kajeyi agurin ma'kiyyata 

Hmma ma’kiyarki kuma
Eyyy tofa nikuma Allah yajarabceni dasan abuncinta sosai shiyasa ma kika ganni acan kuma munje maganar inasan dama in ‘kara aurene sbd inasan wadda zata na bani kulawa tana kuma mutuntani da……………..

Aitunkan ya’kara sa taciyo kwalarsa tafara masifa da zage² tana bala’i nizakai wa kishiya sbd kai dan tsinan niyane kuma tambad’ad’d’e wanda bashi da amana matsiyaci shege kawa……….

Kauuu taji and’auketa da mari kafun tad’ago an’kara yi mata wani, tana yun’kurin tasowa aka ‘kara yi mata wani saida akai mata triple sannan aka kyaleta

Mahaifintane yayi mata guda biyu shikuma daddy Nusaiba shiyay mata nafarko

Mahaifintane yace aurema kuwa yanzu aka fara dan saura kwana 2 d’aurin aure ko ki ‘kinso

Wani ihuuuu ta tsala tana dire² tana wlh baku isaba baza’amun kishiyaba kunyi kad’an wlh kunyi kad’an

Haka tai ta ihu tana kuka
Kamo kwalar daddy Nusaiba tai aikam yasakar mata wani marin wanda yafi na d’azu gigiitarwa
Fad’uwatai tana kuka sukuma suka futa danyin safgogin gabansu

Yau tsawon kwana 4 kenan har ankawo amarya amman mom d’in Nusaiba taba futoba

Kwanan amarya biyu tasakawa gidan wuta 

Allah yarufa asiri ma amaryar batanan sun futa yawon sha’katawa ita da daddy’n Nusaiba

Masu aiki ma guduwa sukai suka bar gidan da’kar aka samu aka kashe wutar

Anan ne fa daddy yace bazai ‘kara kwana gidan ba yatafi gidansa shida amaryarsa wanda bata saniba

Kawarta takira suka tafi wajen wani 'katon Boka ahanyar kamaru nan yahad'a musu magunguna dazata futar da kishiyar ta ta mallaki kuma daddy'n Nusaiba

Sun zuba masa kud’i masu yawa sannan suka kamo hanya dan dawowa gida

Ahanyarsu datawowa sukai accident motarsu takama da wuta da’kar aka cirosu akai asibiti dasu

Susha wula’kanci kafin aka kar6esu dukda su ba’ahayyacinsu sukeba
Kwanan su biyu sannan suka dawo hayyacinsu nan suka kira waya sukace ga inda suke da’kar mahaifin mom yataho shida daddy’n Nusaiba

Sun tsorata da ganinsu ahaka 

Amman abun tambayar shin meya kawosu wannan garin dansu basuyi dasu zasuzo garin kamaru ba

Amman babu halin tambaya
Tunda suna cikin halin jinya
Bayan kwana biyu dangin ”kawar tata suma sukazo
Sosai suka tausaya musu
Anan dai aka had’u anata alhini

Yau tsawon sati 4 kenan sukai musu transfer zuwa asibitin Nigeria suka dawo gida baki d'aya 

Anan din ma saidai ace dasau’ki amman dai ciwon nasu kamar gaba yake ‘karayi

Saida sukai wata biyu a asibitin fata sannan sukai musu transfer zuwa asibitin Aminu Kano

Saida suka kwashe tsawon wata 6 suna jinya kafun suka d'an warke dukkan wani tattalin arzi'kin su saida yakarye duk wata dukiya da mom take ta'kama da ita ta'kare dan duk ma'aikatan gidan su sun gudu

 Daddy kuma bashi da kud'i sosai

Gashi ya’ki sanarwa da Nusaiba komai dan tana exam ne bayasan ta tashi hankalinta

  Har gidajensa da filayensa da kuma motocinsa ga amarya da tsohon cikinta haihu wa yau ko gobe


Sosai yake ''ko'karin yaga ya tai makawa iyalan sa dan karya cika ro'kon mutane.

Haka har aka sallamosu gaba d’aya Amman da’kar yake iya yin wasu abubuwan

Gidan sa daya rage masa shi yasaka akasuwa yasiyar yafara sayarda kayan miya a’kofar gidansa yana samun yaci da iyalansa yasiya musu magani

Yau tun safe amaryar daddy take na'kuda gashi bashi da 'kud'i asibitin gomnaty yakaita anan aka amshi haihuwarta ta haifi yaranta maza guda biyu kyawawan gaske masu kama dashi sakk

Daddy yayi murna da farin ciki danshi tunaninsa baya haihuwa ne ashe yana haihuwa

A6angaren mom kuwa abun sai antausaya mata dan inkaganta yanzu bazaka gane taba sam, indai baka mata mugun sani ba

 Awajen Nusaiba kuwa an kammala exam lpy sosai kuma tasamu saka mako mai kyau

  Azaune suke atsakar gida suna hira Hapsatu tace mata "yar Ummerh ta 
Murmushi tai mai ''kayatarwa tace na'am Ummerh ta 
Yanzu masters zaki cigaba ko kuwa tsayawa zakiyi sai munji abunda shi mijin  naki zaice

Kunyace takama ta, tarufe fuskarta, tace Ummerh na miji kuma waye mijina kuma

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40Next page

Leave a Reply

Back to top button